Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 99 of 124

82

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Duk da batayi tsammanin fiyeda haka daga maganganunshi ba amma jikinta saida yayi sanyi, janye jikinta tayi daga nashi ta sauk'a ta zauna kan gadon, wani iri ta dinga ji ranta batasan lokacin da hawaye ya shiga zubo mata ba, a d'an tsorace ya kalleta ganin ta fara hawaye da sauri ya kamo hannunta yace "Not again, tashi muje malamin na k'asa.....", bata bari ya k'arasa ba ta warce hannunta daga nashi had'e da murgud'a d'an k'aramin bakinta, da serious expression shimfid'e kan fuskarshi yace "Hey watch out", yayi sauri ya sake rik'ota ganin yanda ta mike kamar zata tashi sama, hawaye ne ya cicciko idonta cikin b'acin rai ta tureshi tace "Let me be, I don't wanna talk to you", ta fizge jikinta hawayen dake fuskanta na k'arasa gangarowa, cikin zafin nama ya dad'a fizgota yana mata wani irin kallo yace "Fatima are you okay?, kinada hankali kuwa, na fad'a miki you should stop being rough okay?, you are carrying my baby, i cant risk anything happening to my baby, beside kema bakida lafiya, are you trying to hurt yourself?, mesa bakijin magana ne", ido ta lumshe snn ta bud'esu a hankali hawayen na ci gaba da zubowa, wani matsanancin kuka ta fashe dashi, baisan lokacin da ya furta "Yasalam", ba ya rungumota sosai jikinshi, zama yayi bakin gadon yana patting bayanta tareda d'an rocking d'inta, yanzu ne yake tabbatar da zancen da yayi da Ammah d'azu da ta ce ciwon Batuul ba normal ciwo bane da sa hannu, in ba haka ba she was jovial yanzun nan lokaci d'aya ta fara acting strangely, ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya sunkuyo daidai kunnenta yace "Kinaso nima inyi kukan ko Fatima, I don't like you crying yana d'agamin hankali fiyeda komai, I can feel it a duka pulses d'ina in kina kukan nan, Dan Allah ki dena kinji?", bata d'ago ba
sai ma ci gaba da kukanta da takeyi, ido ya lumshe tareda sake matseta jikinshi yayi pecking goshinta snn yace "Tell me mey ya saki kukan", a hankali ta iya bud'e baki tace "zanje wajen Aunty?", kallonta ya tsaya yi for seconds snn yace "I thought we were done with that Fatima, haka kikeso Aunty ta ganki ba lafiya?, ko kinfiso hankalin Aunty ya tashi in taga yadda kika koma, kinga fa duk kin rame", ya fad'a yana d'aura hannunshi saman wuyanta, "I want you to get better kamin Aunty ta ganki kinji, she will b happy okay?", d'agota yayi yana share mata hawayen dake fuskarta, idanunshi gaba daya na exploring fuskarta kamar maison gano wani abun, Four months back da za a ce mishi akwai ran da zai zauna rarrashin mace kallon you are sick upstairs zai yiwa maishi, amma yau shi da kanshi ya zauna rarrashin yarinya k'arama har yakejin shima kamar zai biye mata suyi kukan tare, murmushi yayi ya jawo plate d'in Baby cucumbeya d'auki slice d'aya ya kai mata shi baki, batayi musu ba ta bud'e mishi baki ya saka mata, haka ya dinga bata har ta cinye slices uku tace mishi ya isheta snn ya d'auki cup d'in madaran nan ya fara bata, shima saida ta kusa shanyewa snn ta kauda kanta, zaiyi magana wayarta dake aljihunshi ta fara ringing, hannu yasa ya ciro wayar, ganin mai k'iran yasa ya mik'a mata

Tagumi tayi ta zubawa wayar dake hannunta idanu, yaushe ma ya zama mutum da har zai wani nemi ta dawo, Mummy ce ta fito daga bedroom dinta sai k'anshi take zubawa ta tsaya kallon Jainaba da tayi tagumi tana kallon wayar hannunta tana mata magana bata amsawa, a d'an tsawace Mum tace "Keee kinada hankali kuwa, tunanin uban wa kike tun d'azu na fito ina miki magana baki sani ba kuma koh shiryawar bakiyi ba bayan tun d'azu nace miki zamu fita", a firgice Jainaba ta juyo snn ta sauk'e Ajiyar zuciya tace "kinga ni banma jiki ba, wai wannan shasha shan ne yake son d'aga min hakali wai lallai lallai gobe in dawo", Mum tana kallonta tace "Waye kuma, shi Idrees d'inne yake ce miki sai kin dawo a goben?, sai yayi himma yazo ya kinkime ki ai, in kinje can dinma uwar mey zai miki in banda jaraba, y'ay'ansa ai kin samo masu kula dasu toh meye zai wani ce ki koma", tab'e baki Jainaba tayi tace "jarababbe d'aya ko biyu, ni da kaina bansan mey zan mishi ba, ni Lagos dinnan ba sonshi nakeba, zama cikin k'abilu ba iyawa zanyi ba", "Mum tace rabu dashi tashi muje inda zamu, zamuyi maganinshi ne ai, so nake inyi maganin wannan sallamammiyar yarinyar nan da batasan mey takeyi ba, wai har ni take cewa babu ruwanta in wannan tsinanniyar ta mutu, kai nasan ba banxa ba har da sa hannu Ajiddeh da hankalinta baxa tayi haka ba", Jainaba tace "Nima haka nake gani wllh in banda haka yaushe ne Ajiddeh zataji tausayin wanna
yarinyar, tsanar da tayi mata koda wuk'a aka bata tsaf zata kasheta amma lokaci d'aya ta wanice ita ba haka ba, gaskiya da ayar tambaya", Mum tayi k'wafa tace "ni tashi muje inma yi mata akayi inma yin kanta ne duk zasuci uwar ubansu, badai ni Bilkisu tayi shirin tozartawa ba, ta Allah ba tata ba, ki taso muje kada raina ya kuma b'aci", Mik'ewa Jainaba tayi tace "muje", a parking lot suka had'u da Daddy zai fita, tsuru tsuru suka tsaya suna muzurai kamar wasu munafukai, har zai shiga motar ya fasa ya kallosu, a d'arare Mum ta k'arasa gurinshi tace "yanxu nakeson shiga wajenka, ashe har zaka fita", kallon shigar dake jikjnta yayi alamar fita zatayi yace mata "ki sameni a part d'ina", ya kalli driver da guard d'inshi yace musu "zaku iya tafiya", da haka ya juya ya koma ciki, gaban Mum na fad'uwa tabi bayan Dad, tasan shi ba mai magana bane kan abu koda yana damunshi amma inhar yayi magana toh lallai abin ya girmama, babban parlour shi ya koma ya shiga tana biye dashi a baya, waje ta samu ta zauna bayan ya zauna cikin nutsuwa yace "Ina Zainab ta tafi sati d'aya kenan rabona da ita", murmushi ta k'irk'iro tace "Laah ai tana gidansu Salma, ai inace ta fad'a maka kafin ta tafi tunda Salman tayi kwana biyu da zata koma shine suka tafi tare", kai ya kad'a yace "Zuwaira keh yanzu zaman yarinyar nan gabanki bai isheki ba har sai ta had'a da yawo", ido ta wara tace "Bafa yawo ta tafi ba, gidansu Salma taje ko nan dinma yawo ne", kallonta kawai ya tsayayi yama rasa mey zaice mata can yace "shirin ina kuma kikayi keh yanzun", tsuke fuska tayi ta had'e rai tace "Y'ar Sa'adatu da akayiwa aure kwanaki toh ta haihu kuma aiki aka mata shine zanje dubata a asibiti", d'an k'aramin tsaki yaja snn yace "in baki nutsu yanzu ba Zuwaira sai yaushe zaki nutsu, shekara kusan nawa da aure kin haifi yara har sunyi aure suma amma bakisan abinda ya kamata ba, ba dole a sako miki y'a ba tunda abinda taga kinayi shi zatayi a gidanta kuma su na tabbata da hankalinsu shiyasa suka dawo miki da y'ar, tunda abinda kike so kenan sai ki barta tayi ta shirme kina biyeta, aikinki kenan kullum bin k'awaye kamar wata yarinya k'arama? da girmanki bakisan kula da miji ba, gabaki dayanshi hakkin auren ma ba saninshi kikayi ba", had'e rai tayi tace "Nasani ai dama cin fuska zakamin, zumunci zaka hanani yinshine, menene a cikin auren da banayi maka masu aikine gasu nan kai kake biyansu, komai sunayi, so kake sai in riqa zuwa ina baka abincin a baki ina maka wanka, dududu ma sau nawa ake ganinka a wata, ni wlhy bazan
iya da zaman matsi kamar wata y'ar
k'auye ba, a matsayinka kamata yayi ina matar perm sect ace duk bayan sati biyu bana Nigeria, ka tsare ka hana kuma cikin gari ma ka hanani, wlhy bai yiwuwa, exposure ko wane irine yaci na ganshi amma duk kabi ka datse, toh ni ban iyawa", kallonta kawai yakeyi da mamaki, murmushi yayi yace "Tashi kije", dan yasan babu abinda zai fad'a taji tayi aiki dashi ta riga da tayi nisa, babu kunya ba tsoron Allah ta mik'e ta kad'a gyale ta fice daga

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.