Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 89 of 124

Take a minute of silence and pray 馃檱 for Burma, (our Muslim brother and Sisters) Ya Allah, Dan sunayenka kyawawa, Dan tsarkin mulkinka ya Zul jalali wal Ikram, Ya Allah ka kawowa bayinka sassauci cikin al'amarinsu, ka gafartawa wadanda magabatanmu, wad'anda suke raye Ya Allah ka kubutar dasu daga sharrin masharranta, Allah ka kawo musu Agaji Ya Rabbal Alamin.Amin

Hey to everyone reading Batuul, zaku jini shiru kwana biyu, abubuwane suka min yawa snn ga Exams da zan fara next week (Allah ya bamu sa'a), am not promising you guys update all the time, but In sha Allah I will try my best inga nayi muku update whenever I get d chance, and I thank you all for your prayers, naji dadi sosai gaskiya, Allah yasa mudace
馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

73

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Sulalewa kasa tayi wasu hawaye masu d'umi na bin kuncinta bayan tayi recover daga shock din da ta tafi na kusan minti goma, ta kai minti ashirin xaune nan gun ta kasa motsi, so take kawai taji wani yace mata a mafarki take jin duk abin nan da ya faru a while a ago, kuka ta fashe da da karfi, wanda hakan ya tabbatar mata ba mafarki takeyi ba, komai a zahiri yake faruwa, ba gizo kunnenta ke mata, sai a lokacin taji zuciyanta na bugawa kamar mai shirin fitowa, a hankali ta shiga girgiza kai tana tariyo duk abinda ya faru kanta, yanzu duk wannan abinda Abu ya fad'a mata duk gaske ne, Batuul matar Abu ce, ji tayi zuciyarta na shirin fitowa don wani irin bugu yakeyi da ya tsorata ta, a hankali ta kai hannu kan fuskarta ta shafo hawayen dake ta kwaranya ba tareda ta shirya fitowansu ba, maganganun Abuturrab ne ya rik'a dawowa a hankali yana mata yawo kwakwalwarta "kika kuskura ki sake tab'ata ko kika yi gigin k'iranta da karuwa sai na hallaka ki wllh, don matsayinta d'aya yake da naki a gidan nan, "Let me tell you what you don't know jiddah, kamar yadda kike matata a gidan nan, toh haka Batuul ma take matata ta sunna, snn cikin dake jikinta ba na kowa bane, nawane" wani irin ihu ta saki tana toshe kunnuwanta ta fad'a k'asa tana rik'e da kanta tana birgima kamar wata yarinya, gaba d'aya ta fita hayyacinta sai ihu takeyi, abunka da farar fata har ta canja kamanni tayi jajir, tun ranar da ta fara ganin Batuul a gun graduation d'insu har aka sashi yin pictures da ita kawae ke tariyo mata, ranan dinner d'insu da ya d'aukota a motarshi, ranan da ya dawo mata da Batuul gida wai karatu tazoyi har yau da ya bud'i baki yake ce mata Batuul matarsace kuma shi keda cikin jikinta, wani abune taji ya tokare mata mak'oshi ta rintse ido ta bud'e jikinta ya dau rawa, wani kara ta kuma saki tace "Inaaaa, Bazai yiwu ba wlhy, zakuyi dana sanin rainamin hankali da kukayi daga ku har iyayenku, bakusan wacece Ajiddeh ba, Aliyu sai na sa kayi dana sanin cin amanata da kayi wlhy, ita kuma tsinanniyar nan wlhy na rantse sai ta d'and'ani azaba da zata gwammace gara ta mutu da ita snn in aikata Lahira da ita da shegen dake cikinta, wlhy sai nasa na Lahira ya fiki jin dad'i, da haka ta mik'e ta haura sama da k'yar dan ji take zuciyarta kamar zata fito ga wani mugun jiri da take gani, tunda take bata taba shiga tashin hankali da rudani irin na lokacin ba.

Shi kam yana haurawa sama, kan gadon d'akin da yake kwana ciki yanzu ya kwantar da Batuul da kanta yake a d'aure, gaba d'aya jiri ke damunta, idonta taf da hawaye, k'ok'arin rage mata kayan jikinta ya shiga yi, dukda bata jin k'arfin jikinta hakan bai hanata rik'e rigan ba, lumsassun idanunshi ya sauk'e kan fuskarta yace "stay still or I slap you", ture hannunshi tayi daga jikinta tace "Ni ka bari sanyi nakeji", mik'ewa yayi yaje ya kaso ACn d'akin ya dawo ya zauna kan gadon, kallonshi kawai Batuul keyi har saida yayi noticing d'in kallon ya d'age girarshi d'aya yace "Anything", d'auke kanta tayi daga kallonshi ta rintse ido, gaba d'aya maganganun da Ajiddeh ta fad'a mata ke dawo mata yanzu, "In kana tunanin ni xa ayi ma wasa da hankali kayi karya Aliyu, don zaman karuwan nan ya k'are gidan nan, Munafuka algunguma, ashe karuwanci kike yi dama, toh yau Allah ya toni asirinki, iskanci ba a gidana za ayishi ba dan ban gada ba, a tafi can inda aka saba aci gaba dayi, Dan ni dai kam ban zama da mai cikin shege a gidana, k'arshen karuwanci dai yau ya k'are gidana, aje gaba aci gaba daga inda aka tsaya", idonta taf da hawaye take kallonshi, a hankali ta bud'e baki tace "I don't get abinda matar ka ke cewa, waye mai ciki a gidan?" jin tambayar da ta mishi yasashi juyowa yana kallonta, had'e rai yayi yace "wane cikin? were you eavesdropping?", had'e rai tayi itama ta harareshi tace "Ba ina wajen ba naji ta fad'a", had'e rai ya sakeyi yace "look! Lie down and sleep, bana son shirme", daga haka ya Shiga k'ok'arin kwantar da ita, ture hannayenshi ta shiga yi tana kokarin saukowa kan gadon tace "I have classes today, ni zan shirya in tafi" ta fad'a tana k'ok'arin sauk'a daga kan gadon, jiri ne ya d'ebeta tayi baya zata koma yayi sauri ya jawota jikinshi yana mata wani irin kallo yace "ina miki wasa ko, I will slap you if you dare move an inche daga nan", da k'arfi ta shiga janye jikinta daga nashi tace "Nikam ka kyaleni, I told you school zanje, av missed a lot", har lokacin yana rik'e da ita yace "You are going no where," kuka ta fashe mishi da tace "nikam sai naje, kuma zan fad'awa Ammah baka barin ina xuwa makaranta", kallon fuskarta yakeyi yanda hawaye ke kwaranya daya na bin d'aya har cikin ranshi yakejin kukan da takeyi, ji yakeyi kamar zaiyi affecting abinda ke cikinta, yace "not just today, daga yau baki sake fita ko ina, and dare going anywhere kiga abinda zan miki", birkice mishi tayi tana kuka ta shiga dukan k'irjinshi tana turashi ya saketa tace "I knew it dama you are always against my happiness and you will surely stop it someday, gashi yanzu ka fara da hanani zuwa school, why? What have I done to you to deserve all this, why why why me?", rintse ido yayi dan ji yakeyi ko improper motsi tayi wani abun zai sami babyn cikin dake jikinta, a hankali ya bud'e lumsassun idanunshi da har sun fara canja kala, shoulders d'inta yayi gripping firmly yana kallon face d'inta da ya jik'e da hawaye da d'an k'aramin lips d'inta da ya sake rinewa saboda kukan da takeyi, cikin husky voice d'inshi in a serious tone yace mata "Fatima you are carrying my baby, I can't risk losing my child, zaki koma school bayan kin haifa min babyna", ya sassauta muryanshi ya kamo fuskanta yace "I promise you zaki koma school kinji Fatima, for now kiyi hakuri I need to take care of my child and in kina zuwa school you will b stressed har yayi affecting babyna kuma bazan samu time d'in kula da Babyna ba, kinji", ya fad'a yana d'an kad'a kanshi yana son yayi convincing d'inta, tsit tayi tana kallonsa da mamaki fuskarta, baby kuma, which baby is he referring to, kamar yasan tunanin da take a hankali yace "Yea our baby!" Wani matsanancin kuka ta fashe da, wato ita ce me cikin da Ajiddeh ke nufi, jawota yayi ya shiga lallashinta, wani haushin shi kawae ta dinga ji a lokacin, kenan wannan aman da take tayi da bacci duk cikin ne ya jawo mata, ita da anytime sooner or later take tunanin zai maidata gida shine wai itace harda haihuwa, d'an k'aramin tsaki yaja daga ciki jim kamar ana d'ada tunxurata, yarinyar nan na birkita mishi kwakwalwa ba kadan ba, ko shirmen da Ajiddeh ta gama yi mishi bai d'aga mishi hankali ba kamar yadda kukanta ke yi ynxu, duk wani motsi nata yanzu a ranshi yakeji, rungumota yayi jikinshi sosai a kunnenta yace "Batuuul mana, its okay tell me, duk mey kikeso zanyi miki shi, I promise", har ranta taji yadda ya k'ira sunan nata, this is his first time calling her Batuul, shi baima san ya fad'i ba, a hankali ya sassauta rik'on ya d'ago hab'arta yana kallon fuskanta yace "kinji?", bata bashi amsa sai tambayar da ta jefo mishi tana shessheka tace "zaka maidani gidan Aunty in na baka babyn ka toh?", ya kai 2mins yana kallonta jin mey tace, it caught him off guard, lumshe ido yayi ya bud'e sannan yace "will that make you happy?", kai ta gyad'a mishi, yace "Fine, but for the time being xakiyi duk abinda nace, babu arguments, zaki barni in kula da Babyna dake kanki, you will do everything as I say, and then we will b best of friends, babu tsiwa kuma", da sauri ta shiga gyad'a mishi kai tace "na yadda, kuma dama ai can ni bana tsiwa", yace "That's my girl, I will do that for you", murmushi ne yayi escaping lips d'inta ta dunk'ule hannunta tare da miko mishi tace "Deal?", shima murmushin yayi ya miqo nashi hannun yace "Deal", janyota jikinshi yayi daga haka ya shiga kissing lips d'inta da suke tempting d'insa passionately

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.