Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 94 of 124

Washe gari da sassafe ya fito lokacin Ajiddeh na bacci ya tafi can gidan, a d'aki ya tadda Batuul kwance, kallo takeyi amma gaba d'aya hankalinta baya wajen, da k'yar ta samu bacci ya d'auketa jiyan nan, gaba d'aya haushinshi takeji, d'auke kai tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da abinda takeyi, hawowa yayi kan gadon ya d'agata cak yace "Wannan shariyan haka kuma fa? How is my baby?, ya fad'a yana shafa cikinta daidai nan Farida ta shigo riqe da d'an tray da glass cup a kai, had'e rai tayi ta k'araso ciki tareda gaisheshi, bai amsa mata ba saima harara da ya bita dashi, zumb'uro baki tayi tacewa Batuul "Ga lemonade d'in" ta juya zata fita, kai Batuul ta kad'a mata kawai dan kunyan yadda tazo ta samesu ta ji" Farida na fita ya juyo da Batuul yace "Hey bana son wannan silent treatment d'in mana, shout and yell yafi min da wannan shirun da kikemin", kamar ba da ita yayi maganan ba ta sake d'auke Kanta, a hankali ya fara mata magana yace "Hear me out, kinga Ajiddeh ce fa batajin dad'i shiyasa ban dawo ba jiya", kuka ta fashe mishi da ta shiga turashi daga jikinta tace "ai ni lafiyar ce dani, ka koma wajenta tunda nata lafiyan yafi damunka", dariya ne ya k'ufce mishi ganowa da yayi kishi ke damunta, nan ta k'ara k'arfin kukanta, janyota yayi jikinshi ya rungume ya shiga lallashinta, da k'yar ya samu tayi shiru, sai wajen 10 d'in safe ya fita siyo mata abubuwan da ta lissafa mishi zataci ya fita ya samo mata, lokacin da ya dawo gida a parlourn k'asa ya tadda Farida zaune tana kallon Tv yace mata "Ammah tace min Monday zakiyi resuming school dan haka nanda kwana hud'u zaki koma", tace "Ehhh", har ya fara tafiya tace "Yaa Abu wayoyinmu a gidanka, dan Allah ka kawo mana, koh jiya haka Batuul tayi ta amai kuma na rasa wanda zan fad'awa dan babu waya", har ranshi yaji aman da Batuul tayi dan yasan tana wahala sosai amma yaqi nunawa ya dake yace "anqi a kawo d'in, da uban wani ne ya saki bari can?", ya haura sama ya barta nan zaune, kullum haka yakeyi da sassafe zai zo ya dubata har sai ya sata yin bacci yake komawa wajen Ajiddeh, Ajiddeh ma bata sake mishi maganan Batuul ba, ko tambayanshi Ina take batayi ba, Dan Mummy tace mata ta kwantarda hankalinta cikin kwana biyu za ayi maganin Batuul, Farida kuma ce mata yayi ta koma Nigeria.

Bayan kwana uku ana gobe Farida zata koma da yamma Batuul na baccinta a d'aki ita kuma Farida na gefenta tana chatting da Affan d'inta sai murmushi takeyi abinta, a firgice Batuul ta farka tareda sakin k'ara, Farida dake gefenta ta mik'e a rude ta rik'ota tana tambayarta ko lafiya, kasa yi mata magana tayi sai riqe cikinta da tayi ta sulale k'asa tana yarfe hannu, hankali tashe Farida ta shiga neman layin Abutturab dan ko 2hrs baiyi da barin gidan ba, baccin ma da takeyi ajikinshi tayi snn ya kwantar da ita ya fita, kullum a rana yakan shigo sau biyar kuma da sassafe yake shigowa, watarana sai dai ta farka ta ganta a jikinshi, kwana ne kawai bayayi, kuka Farida ta fashe da ganin har ya katse bai d'auka ba, a karo na biyu ne da ta k'ira yana fara ringing ya d'aga, cikin kuka ta fad'a mishi abinda ke damun Batuul, bata gama ba ya katse wayan cikin tashin hankali, in few minutes ya iso kamar dama can yana area, a guje a ya hawo sama, ganin Batuul riqe da cikinta tanata murk'usu ya sake tada mishi hankali, nan ya rungumota ya shiga tambayarta mey ke damunta taqi cewa komai sai kukan da takeyi tana riqe da cikinta duk yanda yaso tyi magana batayi ba sai juye juye da takeyi, Shida Faridan duk hankalinsu tashe yake sosai, ganin sae gaba abun yakeyi duk ya rud'e, Farida daketa hawaye tayi k'arfin halin cewa Yaa Abu mu kaita asibiti Dan Allah kar wani abin ya sameta, sai lokacin tunanin Hospital ya fad'o mishi, ko second d'aya bai k'ara ba ya d'auke ta cak yayi waje da ita, mota ya sata shima ya shiga yaja motar duk hankalinsa tashe, a gurguje doctors suka karb'eta suka shiga dubata, duk iya kwarewarsu sun nuna amma basuga komai ba, haka suka hak'ura suka yi mata allurar pain reliever suka k'ara mata ruwa Dan ganin yanda taji jiki ta jigata, har ta fad'a daga d'an lokacin nan, likitocin na fita ya taso ya rungumeta yana sake tambayanta ta fad'a mishi inda ke mata ciwo, duk yanda yayi da ita k'in cewa komai tayi sai kukan da take tana juye juye, iyakar rudewa ya rude, Farida har fuskarta ya kumbura tsabar kukan da tasha, shikam ji yakeyi kamar ya cire mata ciwon ya dawo dashi jikinsa, Farida ce ta matso gaban gadon ta riqe hannunta d'aya ta shiga tofa mata addu'a a hankali, ta kusa minti sha biyar tana mata addu'a, ko Abutturab baisan abinda takeyi ba, a hankali ta fara tsaida kukan da takeyi jin ta fara samun relieve har dai tayi shiru tayi lamo jikinsa tana sauk'e numfashi, a hankali ya d'ago kanta yana kallon idonta da ya kumbura tsabar kukan da tasha, cikin sanyin Murya yace "Fatima don Allah tell me mey ke damunki, ina ke maki ciwo?", kyar ta iya bud'e baki tana nuna masa cikinta tace "cikina kemin wani iri", rungumeta yayi tsam jikinshi kamar wacce za a k'wace ya dinga rad'a mata sannu a hankali.
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

77

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Tana nan rungume jikinshi har tayi bacci, a hankali yaji numfashinta na sauk'a kad'an kad'an alamun baccin nata ya fara nauyi, ajiyar zuciya ya sauk'e amma har lokacin tana nan kwance jikinshi bai kwantar da ita ba, sai bayan 15mins snn a hankali ya d'an d'agota daga jikinshi ya kwantar da ita kan gadon, kallon k'aramin cute face d'inta ya tsaya yi yana lumshe ido, ciwon rana d'aya amma duk ta fad'a ta rame, dama can ba wani jikin bane da ita, sai haske da ta k'ara, yafi five minutes idonshi na kanta daga baya ya d'auke idanunshi ya sauk'esu kan Farida dake tsaye gefe duk tayi sanyi yace "Taci wani abune bayan na fita?", kai ta girgiza mishi a hankali tace "Babu abinda taci, ko baccin daka sa tayi ma fa bata tashi ba, kawai ina kwance naga ta mik'e ta riqe cikinta, shine tace yana mata ciwo ne", kallon Farida kawai yakeyi har tayi shiru snn yasa hannu cikin gashin kanshi masu santsi ya bajesu yace "take care I will b right back", daga haka yayi exiting d'akin, har ya dawo bacci Batuul keyi, Farida na zaune kan kujera ta jingina kai ta baya ta tsura ma Batuul idanu, tausayinta kawai take cikin ranta, ji takeyi kamar ta fasa komawan gobe ko kuma su tafi tare, motsin k'ofan da taji ne yasata duban wajen, Abuturrab ne ya shigo riqe da paper bags a hannyenshi har ya k'araso cikin d'akin snn Farida ta miqe tana mishi sannu da zuwa ta anshi kayan dake hannun nashi, zama yayi daga kan kujeran idonshi nan kan Batuul d'in, sai da Farida tace mishi sannu da zuwa yaya snn ya dubeta ba tareda ya amsa ba ya jeho mata tambayar "Ta tashi bayan na fita?", kai ta kad'a mishi tace "No! Bata tashi ba, baccinta takeyi tun d'azu" bai ce komai ba ya juya ga kallon Batuul d'in da yakeji kamar ya cire mata ciwon gaba d'ayanshi ta huta, hannunta da babu drip ya kamo cikin nashi ya rik'e gam yana jin wani feeling na circulating dukkanin nerves d'inshi, a hankali ya juyo ya dubi Faridan yace "Kinci abinci ne?", ta kad'a mishi kai alamar a'a, yace "gashi nan ki duba packs d'innan", yayi mata nuni da bags d'in da ya shigo dasu, bags d'in ta janyo ta shiga bubbud'esu, tab'e baki tayi ganin irin abincin da ya siyo musu, ita bata cika son jagwalgwalon turawa ba, daga k'arshe dai pasta with Lamb ragu da cauli flower crisp ta ciro ta ajiye gefe, kallon Abu tayi tace "Yaa Abu in ciro maka?", kamar me nazari yake kallonta snn ya girgiza mata yace "No am okay", batayi mishi musu ba ta koma kan kujera ta shiga cin abincinta, sai da ta gama tayi disposing packs d'in yace mata ta mik'o mishi ruwa, Fridge d'in d'akin ta bud'e ta mik'o mishi bottle d'aya bayan ta bud'e, har lokacin hannunshi na cikin na Batuul, yana jin yadda pulses d'inta ke kaiwa da komowa, basu fi thirty minutes ba bayan nan ta bud'e lumsassun idanunta a hankali, kanshi tafara sauk'esu, ido ya wara shima ya matso kan gadon ya d'agota sai ji tayi ya rungumeta jikinshi, ya kai minti biyu rungume da ita bata yi k'ok'arin k'wace kanta ba har saida ya saketa ya d'ago hab'arta yace "Ina ke miki ciwo yanxu Fatima?", murmushi tayi mishi kawai ta shiga k'ok'arin tashi ta zauna, da kanshi ya d'agata ta zauna yana making sure bata takura ba, ganin yanda Farida ta tsaya tsuru tana kallonta ya bawa Batuul dariya, tace "Hey what's up duk kin zama wata iri, am okay fa", murna ne ya cika Faridan tayi maza ta dawo kan gadon ta zauna, tace "Don't get sick pls, you scared d hell out ta me pls kinji?" murmushi tayi kamar ba ita ke ciwo ba d'azu snn ta kalli Abu da yake lumshe ido yana bud'esu yana kallonta ta d'an shagwab'e fuska tace "Mu tafi gida Yaa Abu, ni bana son asibitin nan", kai ya girgiza mata yace "No sai kin fad'amin mey ke damunki, baza mu tafi ba bamusan mey ke damunki ba", had'e rai tayi tace "Yaa Abu nifa na warke, mu tafi gida", ta fad'a tana k'ok'arin sauk'owa kan gadon, hannunta ya rik'o ya k'ura mata hazel brown idanunshi, cikin wani irin murya yace "Fatima mana, I want you to fully get better, bana son kina shan wahala kamar na yau, nafiso ki zama under medication, under proper care kinji?", zumb'uro mishi baki tayi tace "Toh fa na warke ni, bazan sake yin rashin lafiyan ba", Ido kawai ya zuba mata yanason ta gano abinda yake hange amma baya son stressing d'inta tunda ba isasshen lafiya bane da ita, a sanyaye yace mata "ina zaki yanzun?", ta zumb'uro mishi baki tace "toilet", da sauri Farida ta mik'e ta riqota tace muje in rakaki, kai ta kad'a tace "zanfa Iya da kaina na warke", kamar jira yake ta rufe baki ya sunkuceta yayi toilet da ita itako sai wuntsila k'afa takeyi ya sauk'eta, bai bi ta kanta ba har saida ya Isa toilet snn ya ajiyeta a hankali, d'an murgud'a mishi bakin tayi snn ta kalleshi tace "Toh ka tafi", wani irin kallon da yayi mata yasata yin shiru ta kasa motsi, ganin ta nemi waje ta tsaya yasashi k'arasawa gabanta ya shiga k'ok'arin d'age mata skirt d'inta, ihu ta fasa ta riqe skirt d'in da k'arfi tace "Bafa komai zanyi ba, alwala nakeson yi", kallonta kawai yakeyi snn ya kamata suka koma gaban hand wash basin d'in, kamar wata yarinya shi yayi mata alwalan, bags d'in da ya shigo dasu ya janyo bayan ya sata ta zauna kan gadon, pack d'aya ya Ciro mai d'auke da malted custard roast da Lamb Kebab salad, da kanshi ya bata abinci har saida tace ta k'oshi snn yace tayi sllhn shi kuma ya fita wajen doctor yayi maganan discharging d'inta, bai jima ya shigo lokacin har ta idar da sllh suna hiransu da Farida, ce musu yayi zasu tafi, murna Batuul ta shiga yi dan ta tsani asibiti ita kam, da murnarta ta shige gaba kamar ba ita aka kawo a galabaice ba, driving yakeyi amma duk bayan seconds biyar sai ya juyo ya dubeta, cikin lokaci kad'an suka isa gida lokacin ana k'iran Magrib,saida sukayi sllh snn suka kafa hira ita da Farida, ganin ya shigo d'akin yasa Farida fita, daidai tazo wuceshi yace " You should Get ready gobe flight d'in by 8 ne", sai a lokacin Batuul ta tuna da tafiyan Farida, jiki a sanyaye ta amsa da "toh", sam hankalinta bai kwanta da barin Batuul ba gashi shi bama zama yakeyi ba, cikin d'akin ya k'araso ya zauna bakin gadon yana kallon Batuul da har idonta ya cicciko yace "How you feeling now?", baki ta bud'e zatayi magana hawayen dake tare idonta ya shiga gangarowa, har ranshi ya ji zubowansu da hanzari ya gyara zamanshi kan gadon ya rungumota tareda cewa "Yasalam, Fatima what is it again?, I told you mu zauna asibitin amma kikayi insisting mu dawo gashi nan yana damunki kuma koh", ji yayi ta sake lafewa jikinshi a hankali tace "Does she have to leave tomorrow?", sai da ya tsaya for some seconds snn ya gano abinda take nufi, ajiyar zuciya ya sauk'e jin ba ciwon cikin nata bane ta d'ago kanta yace "School zata koma, dama mid semester break ta zo", a hankali ta d'ago ta dubeshi tace "toh ni yaushe zaka kaini gidan, I want to go home" muryarta na rawa ta kare maganar, rungumota ya sakeyi jikinshi yana shafa kanta yace "very soon, ko har kin manta deal d'inmune?, ba nace zan kaiki gida da kaina ba in kika haifa min baby na", d'an zumb'uro baki tayi jin ya ambaci Babyn shi ta kauda kanta, murmushi yayi tareda juyo da kan nata, idonshi kan lips d'inta yace "I like them when you pout, I miss them so much", kamin ta ankara har kai nashi lips d'in kan nata, passionately yake kissing d'inta kamar yau ya fara kissing d'in nata idonsa lumshe, haka yayita tarairayarta har wajen sha d'aya bayan yayi mata wanka ya jasu Sllh Isha ya kwantar da ita ya shiga sata bacci, a jikinshi tayi baccin wajen 11:30, saida ya tabbatar tayi nisa a baccin tukunna ya saka mata temperature d'in d'akin ya koma moderate, ya tabbatar she is fine snn ya fita, a parlourn k'asa ya tadda Farida ta kashe wutan ko ina tana kallon CBS, Ce mata yayi ta koma d'aki gun Batuul snn yayi mata sai da safe ya fita akan gobe da safe zaizo kaita airport ta zama cikin shiri, sai da ya shiga mota tukunna ya tuna da wayoyinsa, missed calls ya gani babu adadi daga mutane daban daban amma duk na Ajiddeh yafi yawa, d'an murza goshinshi yayi snn yayi igniting motar ya d'au hanyan gida, lokacin da ya isa Ajiddeh na kwance parlour tayi bacci da alama tasha kuka ba kad'an, tausayinta yaji Sosai har cikin ranshi yasan bai kyauta mata ba, kashe appliances d'in yayi snn ya dawo ya d'auketa yayi sama da ita

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.