Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 21 of 124
k'iran Massa ne ya shigo wayanshi, recieving yayi yace mishi "ka iso ne?, toh gani nan fitowa", motar da Massa ke ciki yaje ya bu膹e ya zauna , Massa ne ya tambayeshi "ya jikin dai Man, wannan rashin lafiyan ai sai ya bari a kwanakin nan ba, kai da kake shirin zama ango da dai ya isa wani wajen, yayi wrong timing gashi da yake ka fishi k'wari kayi fighting 膹inshi", kallon Massa yayi da 膹an murmushi a fuskanshi ya girgiza kai yaci gaba da danna wayarsa, "Hello", yace bayan ya an 膹auki wayar da ya buga 膹in, amsa akayi da "Hello baby, am missing you over here, ya gajiya dan ni gaba 膹aya na gaji so nake kawai a 膹aura auren nan mu tafi mu huta dan ba k'aramar gajiya nakeji ba a jikina, yanxu ma a 膹aki nake ni ka膹ai wai za a min gyara....", yasan idan ya barta taci gaba da magana sai ya manta dalilin da yasa ya k'irata, katseta yayi yace "gajiya Alhamdulillah, ki fa膹awa su Mum za ayi miki k茅la tul before a tafi wushe wushen a gidan Aunty 膹ina, kuma kayan wushe wushen ma daga can zaki sa, zan aiko mota by 5, you should be ready", ce mishi tayi "Aliyu gaskiya wa膹annan abubuwan naku na al'ada na gaji dasu, tunfa last week ake ta yi, kuma kayan ma mum ta riga da tasa an siyomin a turkey, ni gaskiya a bar wannan 膹in kawai, ai anyi sauran, kuma ma its too late yaushe zan fa膹a musu su shirya", ranshi ne ya fara b'aci, cikin dakewa yace "wani shiri zakuyi, ce miki nayi zan aiko mota ki taho ke ka膹ai, kuma in kin fa膹awa mum 膹in nasan ba hanaki zatayi ba", tsaki yaja dan ranshi da膹a baci yayi yace "in na aiko da motar kar kizo" ya kashe wayan , Massa ne ya dubeshi yaga ranshi ya b'aci yace "lafiya naga kana tsaki", tsakin ya kuma ja yace mishi "yarinyar nan , tun last few days nayi observing that duk abinda na fa膹a sai ta canja, ce mata fa nayi yanxu zan turo driver a kaita gidab Yaa, take cemin ita baza taje ba", bai ci gaba ba Massa ya dafa kafadm膹anshi yace mishi "Man its okay, zata dena in sha Allah", da haka suka canja hira, hotel 膹in sukaje yaga abokananshi dayawa sun sake k'aruwa, sai da ya 膹an huta yake tambayan Massa, "gobe what time za a tafi 膹aurin auren Maiduguri", "sunce flight 膹in goben k'arfe hu膹u ne , so muna da time da in mutane suka k'aru za a yi musu booking tunda da yamma ne", "okay" kawai yace mishi suka shiga cikin abokanan
Ganin ya katse wayan ne ta tsaya ta k'urawa wayan ido kamar wanda sukayi wayan dashi 膹in zai fito, Mesa Aliyu yake min hakane take tambayar kanta, jibi nefa 膹aurin aurensu amma kawai dan ta fa膹i magana ya katse mata waya harda cewa in ya turo motar kar tazo, ai gaskiya ta fa膹a tun kwananki suke ta yi musu abubuwa wai al'ada, shi kuma kawai sai ya 膹au fushi, a ranta take cewa "dan yaga inasonshi ne yake wasu abubuwan", k'wafa tayi ta cewa mai yi mata gyaran jikin zata je ta dawo, matar tace mata babu komai sai kin dawo, fita tayi daga 膹akin, tun daga bakin k'ofa gidan cike yake da y'an uwa d abokan arziki, matane kyawawa, farare da gashi kowa taci kwalliya an zuba gwalagwalai, 膹a膹膹aya zaka bak'i a gidan nan, tana tafiya mutane na ta gaisheta wasu ta gaishesu cikin yarensu shuwa, wani 膹aki ta bu膹e ta shiga, 膹akin babba ne mai kyan gaske, babu mutane a ciki sosai, daga Mum , sai wata mata da zatayi sa'ar Mum sai Yaa zee, k'arasawa tayi ta zauana daga gefen mom, matar kawai tace wa "Jainaba inta afe", matar ce tace mata "afe selai Ajiddeh, ya shirye shirye, da gajiya", tace gashinan fa na gaji sosai, ina su Attutu, Abba Mahammad da Adum", ce mata tayi "suna gida bamuzo tare ba anjima za a kawosu", juyawa tayi ta dubi mum da ke jiranta ta gama ta fa膹a mata dalilinta na fitiwa ana mata gyaran jiki, ce mata tayi "Mum yanxu Aliyu ya k'irani wai zai turo a 膹aukeni k'arfe biyar a kaini gidan k'anwar mamanshi, wai akwai wani abu da zasu yi min daga can zamu wuce wajen wushe wushen, kuma ma wai kayan da zan saka ma su zasu bani", cikin 膹aga murya Mum ta fara magana "nifa Abun nan nasu Hajiya Bilqees ya isheni, wace al'adarsu ce bamu gani ba fara bikin nan, ni sanin da nayiwa Hajiya Bilqees ma ba kanuriya bace amma gaba 膹aya dan tana auren kanuri ta canja gaba 膹aya, a ina ake wani k茅la tul a Ndjamena, kuma da suke cewa su zasu baki kayan kisa ai ganin kasawarsu ne yasa muka ce zamuyi miki , ko 膹ari mukace muna so ai yaci a kawo miki, kinfi k'arfin akwatuna arba'in, ba dan Babanku yace a bari ba kuma zai sab'awa duk wanda ya tada maganan wlhy da sai an maida musu tunda dama cewa tayi a dawo dashi in muka k'i karb'a", Yaa zee ce tace "Mum ai ita tabi ta liqewa yaron kamar babu wani namiji a duniya sai shi, ni gaba 膹ayanshi bai min, sai girman kai da uake dashi kamar mutumin da", matar da aka k'ira da Jainaba ce tace "toh ku yanxu menene na tada jijiyoyin wuya, ai damu suke zancen , ku bari kawai a gama bikin zasu shigo hannu, tayi yadda yace 膹in, anjima in ya turo driver kije, tashi kije a gama miki gyaran kamin lokacin yayi", da haka ta mik'e ta koma 膹akin, tana zama ta k'irashi, ansawa yayi shiru yana jiran yaji mai zata ce mai zata ce mishi, cewa tayi "Hello baby, toh mey na kashe wayan, in ka shirya ka turo motan na fa膹wa su Mum sunce inje", ce mata yayi "okay yayi kyau, by five zaizo", ya katse wayan
K'arfe shida na yamma Aunty ta dawo gida lokacin har Batuul sundawo, a palo ta zauna ta k'irawo wayan Batuul tace mata ta dawo, sauk'owa tayi mata sannu da zuwa, zama tayi daga gefenta tace "Aunty ya gidan bikin", ce mata tayi "lafiya Batuul, masha Allah , gobe zasuje Maiduguri 膹aurin aure, har Baba ma zaije, amma shi sai ranan 膹aurin auren, jibi kenan", baki Batuul ta tab'e tace Allah ya basu zaman lafiya", "Amin" tace sannan tace mata tace "yaushe kuka dawo ne", "tun three thirty suka sauk'eni a gida ita kuma Farida ta wuce gida", ta sake cewa "Aunty maganan admission 膹in nawa kunyi da Baban, time yana wucewa", Aunty ce tace "ni na manta ma Batuul amma yau zamuyi maganan in sha Allah , Allah dai yasa kar in manta, "Amin ta amsa da sannan suka mik'e a tare sukaje yin sallah dan an fara k'ira, Batuul na 膹aki bayan ta idar da sallah ta zauna tana game a Macbook 膹inta, Yusra ce ta shigo tace mata "Yaa Batuul, Mama tana k'iranki tana 膹akinta", cemata tayi "kice ina zuwa", ta juya ta fita, tana fita ta 膹auke Macbook 膹in akan cinyarta ta mayar gefe, mik'ewa tayi tabi bayan Yusra, da sallama ta shiga ta tarar Aunty tana duba abu a closet 膹in kayanta, k'arasawa tayi cikin 膹akin tare da sallama ta zauna aka makeken gadon 膹akin, cewa tayi "Aunty gani", sai da gama dubo kayan da take nema sannan tace wa Batuul "kije ki shirya zamu tafi wushe wushen Aliyu, k'arfe 8 zamu fita, kije maza ki shirya", da sauri Batuul ta 膹ago kanta tana kallon Aunty, ganin Aunty ko noticing kallon da take mata ma batayi ba yasa ta cewa "Aunty wushe wushe kuma, nifa bazan je ba , tun 膹azu ma na fa膹awa Farida, kuma ma ban shirya bafa", ba tare da Aunty ta kalleta ba tace "ki tashi kije shirya, jama'a sai tambayana ina kike akeyi, wasu ma cewa suke ni ke hanaki fitowa bayan halinki ne na k'in jama'a yake hanaki shiga taro, ki tashi kije ki shirya" tana fa膹a mata tana warware laffayan da ta 膹auko, baki Batuul ta zumb'uro ranta a b'ace ta mik'e ta fita, 膹akinta ta isa ta zauna akan gado gaba 膹aya ranta a dagule, toh ita wane kaya ma zata sa , bayan angon ma ba son mutane yake ba shine za ace wani sai anje bikinshi, mik'ewa tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa ta fito, zama tayi shafe jikinta da mai sannan ta isa closet 膹in kayanta ta ciro abaya 膹aya a hanga na Al layl mai kyau da purple crystals a jiki ta sa, gashinta ta taje ta k'ara parking 膹inshi sannan ta shafa powder ta saka kwalli a idonta da chappete a bakinta, turarenta masu k'anshi ta fesa ta sauk'o k'asa tana jiran Aunty, Aunty na sauk'o zata cewa 膹aya daga cikin masu aikin ya k'ira mata Batuul ta ganta zaune a palo, ce mata tayi "Batuul bana son iskanci, kina jina, ince kije ki shirya shine zakije ki wani sako min doguwar bak'ar riga, dama naga ranki bai so ba shiyasa dole ki b'ata min rai ko?, toh ki wuce kije ki canza su kuma karki b'ata min lokaci, mik'ewa Batuul tayi tace "Aunty bansan kayan da zan saka bane", "duk kayanki kice min kin rasa na sawa, ba wushe wushe bane, ai kina da dongashua da zaki saka, ki wuce kije ki canja ki dena b'ata min lokaci", rafiya tayi ta haura sama ,kaya ta canja ta saka shadda duck mai blue da bak'i, 膹inkin riga robe da straight skirt, ta 膹auko k'aramin jan gyale ta yafa, ta saka sark'a da 膹an kunne suma ja da abun hannunsu, shoe Rack 膹inta ta nufa ta 膹auki slippers 膹inta louis vuitton mai ja da bak'i ta saka, tayi kyau sosai har ta fi da, sauk'owa tayi, Aunty batace mata komai ba tayi hanyan waje, Batuul ma ta bita a baya, mota Aunty ta bu膹e ta shiga, Batuul ma ta shiga gidan gaba, Fa'iza da ke rike da Aabid suka zauna a baya itada Yusra, Aunty ke tuk'a motan suka 膹au hanyan inda za ayi event 膹in, parking sukayi a wajen parking 膹in motoci , suna fitowa daga mota, sautin ki膹a ke tashi a wajen, tana fitowa daga mota wata rolls royce ta danno kanta wajen, daidai fuskan Batuul motan ya haska, tsayawa tayi mai motan ya gama iskancinshi na haske mata ido sai ta tafi dan bata gani, su Aunty har sunyi gaba sun barta, k'ofan motan aka bu膹e, iska ne ya buso mata k'anshi turaren, kanta ta 膹ago dan tasan mai turaren, kashen wutan motar akayi tana 膹aga ido, fuskan Abutturab idonta ya sauk'a akai, ba ka膹an ba yayi kyau, kaftan sky blue ya saka, yayi kyau sosai, shades 膹in ray ban ne mak'ale a idonshi, gani tayi yana tahowa hanyanta, tsayawa tayi ta kasa motsi sai bugun da zuciya ya fara
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.