Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 124
Sun fito kenan sun karasa dining area mai dauke da round dinning table mai adon royal gold, kan dinning table din dauke yake da abinci na alfarma irin su *ndalayi*, *kisre* (sinasir) *k锚moniye*(farfesun kayan ciki) *ngaji*(burabusko) miyar kubewa, yakuwa, peppered chicken sai kunun gyada. zagaye table din yake da kujeru guda sha biyu sunja kujerun zasu zauna kenan wata yarinya fara kyakyawa da baza ta wuce 16 yrs ba ta fito 脿 guje tana fadin Ammah wanne zan sa........bata karasa maganar ba tayi shiru tareda da riqe baqi tace ooops Yaa Abu ina kwana ya dubeta yace kin tashi lafiya tace ehhh Alhamdulillah ta juya ta kalli mamansu tace Ammi Yaa Abu ba ya tafi Umara ba ? Sadiq ya juyo yana dariya yace bai tafi kuma da shi zaki tafi masallaci tace amma lokacin da mukayi waya da ina school ai kace ya tafi, Sadiq ya sake murmushi yace toh ya fasa tace toh ta sake duban Ammanta tace Amma *ndaso yik锚kin* ? (wanne zan saka ?) Ammah tace mata ki saka blue din tace toh ta juyo ta dubi Yaa Abu tace da Abui zaku tafi masallaci ? Kanshi 脿 duke yana danna waya ba tare da ya dago ba yace mata ehhh Ammah da Sadiq basuce komai ba sai tsayawa da sukayi suna kallonta dan suji dalinlinta na tambaya amma bata ce musu komai ba ta koma jikinta a sanye tana fara tafiya taji yace Farida tace naam Yaa Abu yace mata saura ki tsaya kwalliya ki bata min lokaci ba tare da cewa komai ba ta juya taci gaba da tafiya har taje daki sannaan ta zauna akan makeken gadon dake dakinta ta fara yiwa kanta magana tana cewa Yaa Abun nan kullum wai sai da Abui zai tafi dan yasan kullum Abui nake bi shine kuma yace shima dashi zaije kuma ya dinga hana mutane magana wai shi bayason surutu, Ni nan gaba zan dena bin Abui ina bin Ammah
Ammah ce ta kira daya daga cikin masu aikin gidan tace Fanne ba a kawo shayin Abu ba da sauri mai aikin taje dauko flask din ta ajiye ta juya ita kuma Ammah ta tafi bawa mijinta abincinshi , ya dauki flask din tare da zubawa a cup yana kurba kadan kadan kanshin shayin ne ya sani matsawa baya saboda in naci gaba da shaqa toh sai nace musu su zubamin, kanshi ne da ya hada na lemon grass, na'na',citta, kanumfari da cardamom seeds da mint leaves.
Bayan ya gama shan shayin ne ya dauki saucer ya Saka kisre guda daya da miyar kubewa danya da yaji naman kaji 脿 ciki. Ahankali ya dinga ci har ya gama sannan ya miqe ya yaje wajen hand wash basin din dake dinning area din, ya wanke hannunshi ya tsane da towel sannan ya bude fridge ya dauki robar ruwan faro, ya juyo ya tambayi sadiq bayan ya kurbi ruwan Sadiq wane masallaci zakuje da Ammah ? Yace filin polo zamuje kasan bata cika Son zuwa Ramat square dinnan ba yace Toh ni zan wuce bari inje inga ko Abui ya gama sai mu tafi Allah ya kaiku lafiya sai kun dawo ya sake cewa Sadiq kayi tuqi 脿 hankali dont play rough with my life on road Sadiq yayi dariya yace she is mine too y'a karasa falon ya tarar Abui ya gama cin abinci har ya miqe yana saka babbar rigarshi Ammah kuma na fesa mishi turare sannan ta gyara mishi hula Abu yayi murmushi yana son yanda suke kula da junansu dukda Sun tsufa. Abui ne ya juyo ya kalleshi yawwa Abutturab muje lokaci ya kusa kurewa sai kuma ya tuna ashe sarkin rigimar tasa ba ta fito ba ya bude baki kenan zaiyi magana sai gata ta fito da murmushinta mai kyau ta saka riga da skirt din super yellow mai shudin flower ta saka hijab shima blue hannunta riqe da jakar cardio baqa ta karaso taje ta rungume babanta sannan ta tambayeshi Abui *shawang锚na*(nayi kyau)? Yace mata sosai mamana kinyi kyau muje ko ? Tace okay su ukun suka fita su kaje inda motar take pake Abu ya budewa baban nasu mazaunin dake gefen driver farida kuma ta shiga baya. kamin su fita Ammah ma suka fito ita da Sadiq tana sanye da laffaya green and red suka nufi GLK din dake pake 脿 wajen parking mota, sai da suka shiga suka tada suka fita tukunna Abu ma yabi bayansu, su sukayi hagu ta su Sadiq kuma tayi dama.
3
Dedicated to *KHALLESAT HAYDAR*
Tuki yake cike da nutsuwa da kwanciyar hankali kan titin Kashim Ibrahim Road ba a jin komai sai karar AC dake busa iska mai kanshi da dadi har suka karasa masallacin suna ta fadin (Allahu Akbar Allahu Akbar Laillaha illalah Allahu Akbar kabira wal hamdulillahi kasira wa subhanallahi bukratan wa asilaah wa sallalahu ala nabiyina Muhammad wa ala alihi wa sahbihi wa sallama tasliman kabira) Abinda suke ta maimaitawa har suka isa masallacin kenan suka samu waje suka yi parking sannan ya fito ya budewa Abui kofa Farida ma ta bude ta fito ta miko mishi Sallaya daga bayan mota sannan ta kalli Abui tace bari in karasa side na mata Abui yace okay mamana
Bayan idar da sallah ne Aunty ta dauko jakarta ta ciro rafar yan dari biyar sabbi fil ta mikawa Batuul tace gashi ki bayar sadaka ai baba ya baki naki ko ? Batuul tace ehh sannan Aunty ta sake cewa Ni zamu Je mota dasu dasu Yusra dan Aabid ya fara jin yunwa in kin gama ki samemu tace toh Aunty ta karbi kudin ta saka è„¿ jaka tace sai nazo su kuma suka tafi
....Hajiya Allah yasa anyi è„¿ sa'a Allah yasa muna da rabon ganin badi Hajiya è„¿ taimaka Fisabilillahi
Batuul ce ta karasa inda mutanen nan da Almajirai suke a zaune ta ciro kudi daga jakarta na bandir din dari biyar da na dari biyu ta fara rabawa bayin Allah dake wajen su kuma suna ta yi mata addua tana cikin rabawa ne wani iska mai hade da ruwa ya fara saukowa take ba tare da shiri ba ta zube musu kudin dake hannunta ta juya zata bar wajen kenan taji tayi karo da mutum, ta dago kanta da iska ke kokarin cire gyalen da sauri tana fadin Hey am sorry, bata samu karashe maganar ba sabida yadda taga mutumin ya tsaya yana kallonta dogo ne sosai dan sai da ta mikar da kanta sosai kamin ta karashe ganin tsawonsa , kyakyawa ne sannan ba fari bane baqi ne amma baqin shi mai haske ne, yana da side burns sannan yana da dogon hanci da mitstitsin baki dake zagaye da millionnaires belt duk da akwai hula akanshi sai da ta hango gashin kanshi kanannadadde da hulan bai rufe ba haka ma gashin gira da lashes dinshi bakake ne, cikin seconds da basu fi uku ta gama kare mishi kallo tayi sauri ta saukar da kanta kasa dan hawaye taf ya cika idonta, bugun zuciyanta ya karu kamar zai fito
ya bude baki kenan zaiyi mata magana cikin sauri ta matsa baya daga wajen bata tsaya yin komai ba ta juya cikin sauri sauri da dan gudu ta karasa inda tayi parking BMW 8 s茅ries ta bude ta shiga ta jefa jakanta baya , tana zama tayi ajiyar zuciya Aunty ta juyo ta dubeta tace lafiya kike ajiyar zuciya ? Tace Aunty ruwan nan da nayi escaping bai jikani bane ya sani yin ajiyan zuciya Aunty tace toh ni yanxu karbi key mu tafi gida Yusra ta Ce min yunwa takeji, ga Aabid ma na rigima Batuul ta juya bayan motar ta kalli wacce aka kira da Yusra tace ba sai da nace kici abinci ba kamin mu fito ba kika ki wai ke sai kin dawo Batuul ta juyo ta dubi Aunty tace Janet fa har binta ta riqayi da abincin kamin ta saka mata kaya taqi shine yanxu zata cewa mutane wai tana jin yunwa bata ce komai ba Yusran sai zumburo baki da tayi Batuul din ta sake ce mata ki bude jakana akwai TWIX ki dauko kuci ke da Hafix (Babich) ki bawa Fa'iza ma sannan ta juya ta dauki tissue 脿 gaban motar ta goge fuskanta da ya jike da ruwa, ta bude pidgin din motar ta dauko orbit mai flavor din pepper mint ta jefa 脿 baki sannan ta gyara gyalen ta daura shi kamar dankwali sannan tayi igniting motar ta tada suka tafi
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.