Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 27 of 124
22
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Shiri suka hau yi bayan sunyi isha da magariba, 膹akin Ammah suka zauna suna dudduba kayan, lace ne purple mai 膹an ratsi ratsin grey mai kyau, 膹inkin ya amshsu soaai, iri 膹aya akayi musu, sai da suka gama Ammah ta dubi Batuul "Bitti kunyi kyau, amma babu sark'a da 膹an kunnefa, ke Farida ya baki bata ba, sai ki saka keh ka膹ai", hararan Batuul Farida tayi sannan tacewa Ammah "Ammah kiga jewellery box 膹in mafa a gabanta yake, nace ta zab'i wanda zata saka tak'i wai baza ta saka ba", Ammah cewa tayi "A ah Batuul bazai yiwu ba, ina aka tab'a gaye babu 膹ankunne", mik'ewa tayi ta bu膹e closet 膹inta ta fiddo wani 膹an akwati k'arami mai kyau kmar chest box na katako, sai da ta zauna ta bu膹eshi ta fiddo wasu set 膹in y'an kunne da sark'a masu kyau da abun hannu da zobe na azurfa harda agogonshi ta mik'awa Batuul, "ungo maza saka wannan", a kunyace Batuul ta karb'a ta saka, kamar wasu diamond ta saka haka ya dinga haske sabida tsabar kyan da yayi, sai da ta saka Ammah ta dubeta tace "Masha Allah ko kefa", wasu matane suka shigo dukkansu sunyi shiga ta alfarma cikin kayansu masu kyau, harda Aunty Amna a cikinsu, zuwa tayi kusa da Ammah sannan tace mata "Ammah motocin sunxo sunce a shirya a fito, tace toh sai kije ku fara tafiya, ni Sadiq ne zai kaini ku tafi tukunna", Farida ce ta fara fita, motan farko tabi, Batuul dake 膹ingisawa kamin taje motocin sun k'are, dawowa tayi tacewa Ammah babu motocin suntafi, a ranta tana murna Allah yasa babu wanda zai dawo, "ba damuwa, bari in Sadiq yazo sai mu tafi tare", tace "toh", ta hau gado ta kwanta, Takwas da kwata Sadiq ya k'ira Ammah uace mata ya iso, yana jiranta, wasu y'an matane sunsha kyau suma zasu wajen dinner suka ce mishi, tafiya zaiyi yace ehh amma Ammah yazo 膹auka, suka ce mishi tunda ita ka膹ai ce bari su shiga dan har yanxu motocin suke jira su dawo, gaba 膹aya bayan sunyi occupying saura seat 膹in gaba kawai, tare da Batuul Ammah suka sauk'o, rik'e da hannunta a hankali suka taho sabida ciwon da taji, sai da suka zo Ammah taga mota a cike, ce mishi tayi "Sadiq ya akayi haka, ina Batuul 膹in zata zauna", "Ammah bansan da Batuul ba shiyasa na 膹aukesu", "Shikenan kuje da Batuul 膹in , bari in k'ira Alai yazo in ya sauk'e mutanen da ya kai ya dawo ya 膹aukeni, Bitti shiga kuje", Batuul dai na tsaye tana ta addu'an Allah yasa ma kar a samu space 膹in, cewa Ammah tayi "a ah Amma, ke ki fara tafita ni sai a sa driver ya kaini ko Ahmad ne sai in k'ira ya kaini", bata rufe bakinta ba Ammah ta hango Abutturab yana tahowa, cikin tafiyarsa ta kasaita ya nufo inda suke yana gyara hulan kanshi, k'amshin turarenshi gaba 膹aya ya baza wajen, baima lura dasu a wajen ba, sai da ya k'araso yaji muryan Ammah ya 膹ago ya dubi inda suke, ce mishi tayi "yawwa Abu ka shiryako", yace "ehh Ammah yanxu zan wuce sunata jirana" ce mishi tayi "toh ga Batuul nan ka tafi da ita, bana son barinta ita ka膹ai a gida ni zamu tafi tare da sadiq", Batuul da kanta ke sunkuye a k'asa tana wasa da abin hannun da Ammah ta bata 膹azu tayi saurin 膹agowa ta dubeshi jin abinda Ammah tace, ido hu膹u sukayi ya daka mata harara tare da 膹auke idonshi daga dubanta, marairaicewa yyi yace "Ammah sai fa naje hotel mun ha膹u dasu Massa da sauran friends 膹ina tukunna mu biya in 膹auka Ajiddeh, tabi Sadiq kawae, ke sai mu tafi tare", Ammah tace "ka ji ka. ina ni ina wannan yawon da ka lissafa, gara dai itan, kuje da ita kawae, kuma ai Ajiddeh ba duka motar zata cinye ba da kake cewa zaka 膹auko ta, iyaka ta zauna a gaba, Batuul 膹in ta zauna a baya", wani irin b'acin rai yaji gaba 膹aya ranshi, wai mesa Ammah ke son ha膹a shine da yarinyar nan ko da yaushe, a tak'aice yace "muje", snn ya juya ya nufi wajen motarsa, Ammah ta cewa Batuul dake tsaye a wajen ta rasa mey ke mata da膹i "Bitti kuje kinji", a hankali ta fara 膹ingisa k'afarta ta isa wajen motar, wani tsaki yaja ganin yadda take tafiya kamar mai tausayin k'asa, sabuwar lambo ce bak'a k'irin mai tint glass, bu膹e gidan gaba tayi ta zauna , yadda ya fizgi motan ne ya tsorata ta tayi saurin sa hannunta 膹aya a jikin k'ofa 膹aya a wajen hand brake tana neman wani abinda zata rik'e, jin hannunta tayi kan nashi, da sauri ta janye nata hannun ta dafa gaban motar, sai da suka fita tukunna Ammah ma ta shiga na Sadiq suka fita
Gudu yakeyi akan titi kamar shi ya shimfi膹a, tsabar tsoro har wani zazzabi ne taji yana son kamata, sanyi takeji sosai, hannu ta saka ta rage Ac dake aiki a motar, ganin ta rage Ac ne ya sashi juyowa ya dubeta yace "hw dare yhu! inamiki wasa ne zaki tab'a min mota, ko dan kin ganki a ciki" wayanshi ne yayi ringing ya duba yaga mai k'iranshi, bai 膹auka ba har ya tsinke, haka ya dinga ringing wayan baya 膹auka , daga k'arshe ma ya sata a silent, ita dai bata ce mishi komai ba, tunda abunda ke daminta ma ya isheta, ganin ya juyar da kanshi bai k'ara magana ba ta 膹an kwantar da seat 膹in motar ta 膹anyi relaxing tare da lumshe ido dan kanta ya 膹an fara ciwo , a hankali ya juyo ya dubeta yaga yadda ta jingina amma a takure, fuskanta ya kalla, idonshi ya sauk'a kan 膹an k'aramin bakinta da aka sa mata purple ombre lipstick, kyabe baki yyi tare da 膹auke idonshi daga kallonta yaci gaba da tuk'in shi, can ya sake juyowa ya dubeta, lashes 膹inta da suka kwanto fuskarta ya kalla this time around, kamar zatayi magana ta 膹an motsa bakinta, bin bakin yayi da ido, bu膹e idonta tayi taga idonshi akanta, da sauri ta mik'e ta gyara zamanta, shi kuma yyi saurin 膹auke idonshi yayi ya mayar kan titi tare da jan tsaki, haushin kanshi yaji da ya tsaya kallonta har ta bu膹e ido ta ganshi, kuma fa ba wae tayi masa kyau bne, gyara zamanta tayi ta janyo kujeran, ta jingina kanta a glass 膹in window tana kallon waje, a k'ofan hotel 膹in yaja yayi horn aka bu膹e mishi ya sa kai ciki, motoci dayawa ya tarar na abokanshi suna jiranshi, duk sun shirya sunyi kyau, sauk'e glass 膹in motar yayi tareda fitowa waje, inda suke ya isa, Massa ne ya fara tareshi "Kai fa wulak'ancinka dayawa Aliyu, ya zayi kazo ka bar mutane suna ta jiranka, kainefa da kanka kace babu african time 8 dot muna wajen , ana ta k'iran wayanka ma baka 膹auka, har matar taka ma baka 膹aukan wayanta tana ta damuna, har na rasa k'aryar da zan shirya mata ma ta yadda daga k'arshe", duk maganan nan da yakeyi Abutturab baice mishi komai ba, idon Massa ne ya fa膹a kan motar da Abutturab yayi parking , ce mishi yayi "Man ba cutie bace a motan can, mey takeyi a motan ka kuma", ba tare da ya kalleshi ba yace satota nayi zanje in saida ta, ya k'arasa wajen sauran abokan yana mik'a musu hannu, sai da suka gama gaisawa yace musu "kuyi hak'uri na b'ata muku lokaci, something came up, muje ko", kowa motarshi yaje ya bu膹e ya shiga, photographers na ta 膹aukansu hotuna da video, bin Abutturab Massa yayi wajen motanshi yace "na tambayeka ya akayi ka taho da cutie kai da zakaje 膹auko matarka ku wuce, ina zaka da ita, a hasale Abuturrab yace "bakaji bane, nace maka saidata zanyi" ya k'arasa wajen motansa, massa yace "Man i aint joking, am damn serious", yaje ya tsaya dab da widown da Batuul ke zaune yace "cutie", da hanzari ta 膹ago ta dubeshi, ce mata yayi "fito in kaiki a motana, tare zamu tafi", juyawa tayi ta kalli Abu, wani mugun harara da ya kada hanjin cikinta ya sakar mata, lkci daya ya dauke kanshi kamar bai san abinda suke fa膹a ba, da kyar ta iya bude baki tace " yaa Abu Bari in bi Yaa Massa tunda kaima zakaje....." tana k'ok'arin bu膹e k'ofa, cikin dakewa yace "come on get back, da kinsan da Massan kika tsaya sai da kika biyoni, kai kuma ka bari in na maidata kaje ka 膹aukota ka kaita koma ina zaku, just follown Ammah's instruction" yana kai wa nn ya tada motarshi yaja ya bar sa wajen, tsayawa Massa yayi yabi motar da ido, toh mey Abutturab 膹innan ke nufine akan Batuul, haka rannan a wajen wushe wushe ya hanashi sakat, yau kuma ya hanata binshi, yasan kuma ba sonta yake ba, ina! dama ai babu batun so, kafa膹a ya 膹aga yayi hanyar motanshi, koma dai menene zaiji bayan bikin, shima convoy 膹in motocin da akayi yabi a baya
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.