Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 111 of 124

聽 聽 聽聽 Tunda Ajiddeh ta shiga d'aki bata fito ba sai washegari da safe, tasha kuka har ta godewa Allah, da yamman ranan ta fito daga d'akin da ta kwanta ta taga masu aiki sai kai kawo suke wani d'aki, k'arasawa tayi taga waye cikin d'akin, ta manta da sam Mummy tace mata akwai matar da Daddy ya kawo gidan, wata mata ta gani da bandage d'aure jikinta, sai kuma a kanta, sosai ta tsaya tana kallon matar snn ta tab'e baki ta juya ta koma d'akin da ta kwana ciki ta ci gaba da zamanta, ko sau d'aya Mum bata lek'o ta ganta ba sai masu aiki da take tura mata, wayarta da Mum ta bada a kawo mata ta d'auk'a ajiye nan kan gadon, samun kanta tayi da logging wajen calls da neman sunanshi, a hankali ta shafa sunan hawaye na zubowa idonta, tana son Aliyu amma abinda tayi mishi bata tunanin zai yafe mata shi, dialling number tayi, tun kamin yayi ringing tayi maza ta katse k'irar, gallery ta shiga tana kallon hotunansu da sukayi a tare, tana jin inama ya saurareta ko sau d'aya ya bata chance d'in nuna mishi she has changed for good, koda bazai sota ba ita zata soshi, tana cikin tunanin nan ta jiyo tafiyar Dad, sai a lokacin gabanta ya shiga fad'uwa, batasan mey zata ce mishi ya dawo da ita, tashi tai zata shige toilet ta b'oye daidai nan ya hangota, da mamaki k'arara a fuskarshi yake kallonta da ta k'ame waje d'aya hannunta rik'e da knob d'in k'ofar, da mamaki a muryarshi yace "Hauwa, yaushe kika dawo gida?", a hankali ta shiga takowa gabanshi hawayen da take k'ok'arin maidawa na zubowa, a hankali ta k'araso tace "Daddy ina wuni", kallonta kawai yakeyi da ganin yanayinta snn mey take nema side d'in nan, "lafiya", abinda yace kenan snn yace "Tun yaushe kike gida haka, tareda Aliyun kuka dawo?", kai ta shiga girgizawa ta fashe da kuka mai tsanani da k'yar ya lallasheta tayi shiru snn ta da kyar tace, "jiya muka zo shine banajin dad'i nazo gida", kallonta kawai Dad keyi yasan there is more to wannan maganan ba abinda ya faru kenan ba, yace "Shine da shirme da bakida lafiya zaki taho gida, mu lafiyan zamu baki anan gidan d'in kome?", jiki a sanyaye ta rik'o hannun Dad tace "Dad kuma ina missing d'inku shiyasa fa nazo, kayi hak'uri zan koma gobe", tanayi hawaye na ci gaba da zubowa, yace "Its okay, bar kukan, but next time kar ki sake wannan wautar, bakida inda yafi gidan mijinki daraja, yaron kirki mai mutunci ma da yasan darajar mutane, he calls me every two weeks and kowane Sallah da previous azumi in zai bada Sadaka, sai ya k'aramin da wanda zan bawa mutane, he is a good son really, ki kula dashi sosai Hauwa kinji, I don't want you to be like your Sister da ta zama kamar itace k'anwarki, kiyi hak'uri kiyi zamanki gidanki, Allah ya miki albarka", wani kuka taji yaxo mata da batasan yana shirin zuwa ba ta rungume Dad, murmushi yayi ya d'agota yace "Karki damu, my prayers are always with you", ya kamo hannunta yace "I got a patient a wannan d'akin, muje ki gaisheta", suna tafiya yana bata labarin yanda accident d'in nasu ya faru, har suka k'arasa d'akin, ko da sukaje zaune suka tarar da matar da Qur'an gefenta alamar karatu ta gama yanzu, bayan sun gaisa yayi mata ya jiki yace "Ajiddeh wannan itace Kulthum, Kulthum ga d'ayar y'ar tawa sunan ta Hauwa", da murmushi matar tace "Masha Allah, Allah ya rayata, d'azu naga ta lek'o banma san itace ba", Dad yace "Toh ni zan koma inda matsala sai a nemini, Ajiddeh stay here with her for today, keep her company", kai ta kad'a ya fita daga d'akin, kallon Kulthum Ajiddeh ta tsayi, mata mai kyau da ita ko ina y'an uwanta suke, baki ta tab'e ta nemi guri ta zauna dan tunanin nata matsalar

聽 聽聽 Koda aka kawo musu abincin, babu wanda tayiwa ci biyu, shake d'in nema tasha da d'an yawa, sudai da mamaki kawai suke kallonta, Su Yusra ne sukace sunason a kaisu XD cinema, Farida da Sadiq sukace su tashi su kaisu, Batuul dake shan shake d'inta Farida ta duba tace "You going?", d'auke kanta tayi tace "Kuje, kaina zaimin ciwo in na shiga wajen nan, harara Farida ta sakar mata tace "Kedai kyaji dashi, you and your unending problems", had'e rai tayi ta聽 kalli Abu snn ta kalli Farida zatayi magana Abu yace "Farida!!!, ta zumb'uro baki ta kama hannun yaran tace "Kunga kuzo mu tafi, mulki take ji dashi yau d'innan", daga haka suka k'ara gaba abunsu, Abu ya kalleta yayi murmushi yaci gaba da danna wayarsa, sau biyu tana kallonshi taga danna waya kawai yakeyi yana murmushi, yana zaune bai lura da聽 lokacin da ta tashi daga kujerar ta bar wajen ba, wasu mata ne suka zo suka zauna kan kujerun, da mamaki ya d'ago yana kallonsu jin wasu muryoyi daban, kallonsu ya tsaya yi yana so ya tuno inda ya sansu, they look familiar, d'ayar ce yaji tace "AAK, ashe聽ana ganinku a gari, tun daga makaranta shikenan kun b'uya ba a jinku, though kwanaki naje ance ka auri wannan yarinyar Ajiddeh, ya kk ya kwana biyu", sai a lokacin yayi recalling faces d'insu amma bazai ce ga sunayensu ba, kallonsu yake d'aya bayan d'aya snn yace "Excuse me Dan Allah, baku had'u da wata zaune nan kujerar ba?", tab'e baki sukayi sukace, "No we didn't meet anybody gaskiya, ya kk toh ya matar taka?", gaba d'aya hankalinshi baya kansu yace "Yeah she is fine, sorry excuse me, I need to go now", daga haka ya mik'e ya barsu nan zaune, ransu duk ya b'aci amma inda sabo sun san halinshi ne hakan, wayar Batuul ya shiga k'ira amma bata d'auka daga baya ma kasheta akayi, hankakinshi gaba d'aya ya gama tashi, su Sadiq ya k'ira yaji ko tana tare dasu sukace mishi bata zo ba, ya ma rasa ina zai fara nemanta, itakam bakin wani pond taje ta zauna tana kallon swans d'in dake cikin ruwan, sosai suke birgeta, tana daga zaune lokaci lokaci take kallon shi taga yana zaune abunshi, ita da kanta bata san haushin mey take ji ba, wani irin fad'uwa gabanta yayi lokacin da ta hango matanan nan zaune wajenshi, da sauri ta d'auke idonta daga kansu amma curiosity ya sata juyawa ta sake kallonsu, dariya taga sunayi, da sauri ta sake juyawa sbd yadda taji zuciyanta na bugawa, hawaye ne taji ya tarar mata a ido, tana ganin kiranshi tasa wayar a silent, daga baya ta kasheshi gaba d'aya, duk inda yasan zai ganta sai da ya zaga, duk abin nan da yakeyi idonta na kanshi, yana d'aga ido ya fad'a kanta, tana zaune tana kallonshi, da wani irin hazari ya k'araso wajenta tareda fizgota yana k'are mata kallo ya tabbatar if she is fine, wani irin kallo ya bita dashi yace "kinada hankali kuwa?, mey ya tadaki daga wajen da kike, are you even okay wai?, mey ke damunki, tell me now", d'auke kai tayi ta ki yadda ta had'a ido dashi sai da ya sake dad'a k'arfin rik'on yace "I will slap you right away, ina miki magana kina d'aukemin kai, what's wrong with you?", wani irin kuka tasa da yasa jikinshi yayi sanyi, d'an tsaki yaja yasa hannayenshi duka cikin gashinshi ya bajesu, d'aukarta yayi cak ya nufi hanyar mota da ita, lamo tayi jikinshi gabanta na fad'uwa, sai da ya bud'e mota ya sakata ciki snn ya kira Sadiq a waya yace "Sadiq you can take the kids home when they are done, daga nan sai a kaisu gida", bai jira mey Sadiq zaice ba ya kashe wayan
[12/1, 15:42] 80k: 馃挐BATUUL馃挅馃挐

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.