Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 106 of 124
Lokacin da Mum ta haura sama, d'akin da Ajiddeh take mai aikin tayi mata jagora ta kaita snn ta juyo k'asa kawo mata ruwa, har Mum ta shiga d'akin Ajiddeh batan sani ba tana nan kife kan gado sai kuka takeyi, saida taji k'aran rufe k'ofar Mum snn ta d'ago ganin waye, dasauri ta mik'e har tana k'ok'arin fad'uwa ta k'araso gaban Mum tana leqen ko da wani bayan Mum d'in, cikin kuka Ajiddeh na girgiza kai tace "Na shiga uku Mummy, mey kikazo yi kuma, shikenan in auren nawa kikeson kashemin sai ki nemi waje ki zauna, dama gab asirinmu yake da ya tonu, tun daga Maiduguri aka d'auko Malamin da zai duba yarinyar nan kuma yau za a gama, saida nace miki a lalata aikin nan kikaqi gashi yanzu asirinmu zai tonu, Mummy kiyiwa Allah kiyi min rai ki bar gidan nan" ta k'arasa maganan tana mai tsananta kukanta, Mum da ta gama sauraren Ajiddeh ta wara ido tace "Keh don uwarki wasa kike, wane malamin aka kawo mata, ni Zuwaira naga rayuwa, ka haifi d'a baka haifi halinshi ba, Ajiddeh wai mey ke damun kwakwalwarki ne anya kinason gamawa da duniyar nan lafiya kuwa, yanzu har ke da bakinki kike cemin an nema mata mai magani amma baki sanar dani ba sabida ga kanwar uwarki Jainaba ake wa magani ko" Ajiddeh ta d'ago tace "Mum nifa mutuwan ne banaso tayi, mey zamu cewa Allah idan munje gabanshi, mey rayuwarta ta tsaremana da zamu karar mata da kwanakinta, tunda wuri saida nace miki ba kasheta za ayi ba amma kika qi ji", kuka Mum ta fasheda tana "Na shiga uku ni Zuwaira, Hauwa wlhy Allah ya isa haihuwarki da nayi, duk rayuwata ta k'are akan nema muku farin ciki keda y'ar uwarki amma yau bud'ar bakinki nayi abu kike cemin banyi daidai ba", jikin Ajiddeh ne yayi sanyi ganin Mum na kuka tace "Mum nifa ba abinda nake nufi kenan ba, wlhy duk ranarda Aliyu da iyayenshi suka san inada sa hannu cikin ciwon nan nata wlhy sai ya rabu dani Mum, Mum ko bashi ba iyayenshi bazasu yadda ya zauna dani matsayin matarsa ba, Mummy kinfi kowa sanin irin son da nake mishi, rabuwa dashi na nufin rabuwa da farin ciki na kuma bani kad'ai ba har Ku ba bari zaiyi ba dan ko yau da safe saida ya dad'a jaddadamin cewa in ya samu wad'anda suka yi mata wannan aiki toh hukuma ce zata rabasu dashi", Mum da ta fara tsurewa jin har su Abu sunsan asiri ne akayiwa Batuul yasa ta sake matsowa kusa da Ajiddeh tana wara ido tace "Shirman banza, waye yace musun asirine ke sata wannan ciwon", Ajiddeh tace "Yanzu haka fa Mum magani ake mata kumafa na fad'a miki yau d'innan za a gamashi kinga kuma dole komai ya bayyana", Tsaye Mum ta mik'e tana cire mayafin kanta dukda Acn dake aiki cikin d'akin amma gumi takeyi tace "Inaaa!, bazai yiwu ba, Wace irin masifa ce wannan da take shirin kunno min kai lokaci d'aya haka, karya sukeyi wlhy dukkansu sunyi kad'an, bokan nan saida yayi assuring d'ina mutuwa zatayi kuma babu wani wanda zaisan sukeda sa hannu", cikin hanzari ta lalubo wayarta ta shiga k'iran layin Jainaba, bata d'aga ba har ya katse, tsaki taja gaba d'aya jikinta sai rawa yakeyi taci gaba da k'ira, sau uku yana katsewa kamin aka d'aga, Ajiddeh dai kallon Mum kawai takeyi tana fatan Allah yasa kada asirinsu ya tonu, gaba d'aya hankalinta ya gama yin inda akewa Batuul magani, so kawai take taji mey ke faruwa taji meye makomarsu, Mum najin an d'aga waya tace "Jainaba kome kikeyi ki biyo jirgi ki shigo Abuja yau, abin ya min yawa nikad'ai, komai dad'a lalacemin yakeyi", sheshek'ar kuka taji daga d'aya b'angaren, Jainaban dake kuka tace "Yaya kizo ki fitar dani cikin wannan masifa, na gaji da zaman gidan Idrees", Mum ta katseta tace "Mey kuma ya faru bayan wanda kika fad'amin", Jainaba na kuka tace "Banda duka babu abinda nakesha gurinshi, yasa masu gadi sun hanani fita daga gidan, duk ma'aikatan gidan ya koresu babu kowa cikin gidan nan sai ni kad'ai sai kace mayya, yaran ma ya kwashesu bansan inda ya kaisu ba gashi babu kud'i wajena bare in siya kati in miki waya kiji halin da nake ciki, kwakwaran motsi ban isa inyi shiba yanzu zaki ya fara hantara yana tamin habaici kan matar da zai aura", Mum da k'afafunta suka fara rawa jin bayanin Jainaba dawowa tayi kan gadon ta zauna taci gaba da cewa "Yaya ki taimaka kiyi koma menene cikin yau d'innan in samu in fito daga gidan nan, in yaso daga baya musan yadda zamuyi dashi", Mum da abu suka fara cakude mata tace "Ki kwantar da hankali Jainab kina jina, yanzun nan zan fita in San abin yin akanshi, yanzu haka ina wajen shashar nan, daga nan zamu wuce tareda ita, kwantar da hankalinki komai ya kusa zuwa k'arshe", Jainaba tace "Shikenan Yaya ina jira", da haka suka katse waya ta dafa kanta tana tunanin yadda abubuwa sukayi mata yawa lokaci d'aya, can ta juyo ta dubi Ajiddeh dake ta hawaye tace "Ki tashi yanzun nan muje musan abinda za ayi tunda kince yau za a gama mata maganin, Ya Allah mey nayi nake cin karo da masifu iri iri a cikin kwanakin nan", Ajiddeh tace "Mum bafa masifar da kike ciki, in ta tawa kike kije....", Mum cike da fusata tace "Dan uwarki bakida hankali ko?, ganin ina binki a hankali yasa kika fitsare har kike ce min indan taki masifarce in rabu dake ko toh bari kiji, mijin Jainaba aure zai k'ara kullum narka mata duka yakeyi a gida, Wanda zai auri Zainab ya fasa , matarsa da mukayi sanadin fitanta daga gidan ya maidata, Babanku yazo da wata mata gida yasa an gyara mata part guda ya zube mata y'an aiki, bansan tsakaninshi da ita kullum hankalina a tashe na tambayeshi wacece ita yace wannan ba matsalata bace snn gaki, akan wata can banza kikeson b'ata min rai, komai dan ku nake yinshi dan Ku samu farin ciki mai d'orewa amma bakya ganin k'ok'arina, yanzu babbar matsalar da muke ciki duk akanki sbd kin fifita miji da danginsa akanmu, har a samo mai magani bakiyi tunanin sanar dani ba", Mum ta fashe da kuka tace "In sha Allah na barwa Aliyu ke Hauwa, kafata ta bar d'akin nan toh ki manta kinada wata uwa", ta miqe ta zari Jakarta tayi hanyar waje, tana kaiwa bakin k'ofa zata bud'e taji an turo k'ofar, Abutturab ne tareda da Ammah suka shigo d'akin a tare, Ajiddeh na ganin yanayin sa durk'ushe a wajen ta saki wani irin kuka, cikin d'akin ya k'arasa shigowa, Mum da duk yan hanjinta sun kad'a ta dake ta dubi Ammah tace "Yanzu nake shirin inje in duba mai jiki, yarinyar nan ce take ta kuka nace addu'a zatayi mata", ko kallonta Mum batayi ba, Hannun Ajiddeh dake durk'ushe tana kuka ya kamo ya mik'ar da ita, cikeda kuka kamar ranta zai fita tace "Aliyu tsaya kaji Dan Allah, Let me explain kaji, wlhy Allah....", wani irin fizga da yayi mata yasa ta toshe bakinta da d'aya hannun nata, Mum da ta tunkarosu tana "Kai banza ina zaka kaimin y'a kake fizgarta haka", wani mugun kallo da ya jefeta dashi yasa tayi shiru ta matsa da baya, Har ya fita da Ajiddeh daga d'akin baice komai har saida ya kaita d'akinshi da yakeyin ayyukanshi kamin yayi aure, sake hannunta yayi yana kallonta da idanunshi da suka rine yace "Hauwa did you really hurt her? Kune behind suffering din Fatima all this while?", shiru yayi yana jiran jin amsar da zata bashi, ganin tayi shiru tana kuka yasa shi daka mata wani mugun tsawa yace "Answer me" har saida yasa Ammah yiwowa wajen tareda Mum, a kid'ime Ajiddeh ta kalleshi tana kuka tace "Am sorry, am so sorry, I wanted telling you Dan Allah kayi hakuri wlhy sharrin shaid'an ne, forgive me pls Aliyu", wasu hawaye ne masu d'umi ya shiga zirarowa daga idonshi, lumshe ido yayi ya bud'e ya kalleta snn yace "Get out of my sight, don't you ever cross my way not now not ever", tsananta kukanta tayi tana girgiza kai ta shiga matsowa kusa dashi tana "Aliyu you know I love you, karka horani da rashinka, I can't endure ko wane irin punishment amma banda rashinka dan Allah kayi hak'u.....", wani mugun kallo ya jefeta dashi da ya sata had'iye maganarta ya daka mata tsawa yace "I said get out", ganin yanayinshi tasan komai zai iya faruwa a lokacin, toshe bakinta tayi ta juya ta ruga a guje ta fice daga d'akin.
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃æŒÂBATUUL馃挅馃æŒÂ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.