Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 95 of 124

Washegari kamar kullum da ya tashi sllh saida ya tashi Ajiddeh amma bata tashi ba, shi kam daga masallaci d'ayan gidan ya wuce, a kitchen ya taddasu su biyun duka Farida har ta shirya, k'arasowa yayi cikin kitchen d'in yana amsa gaisuwan Farida ya isa inda Batuul ke jingine jinkin Fridge, yana zuwa ya jawota jikinshi ya d'aura hannunshi kan mararta a hankali, da sauri ta d'aga ido taga ko Farida na kallonsu, ai kuwa ido hud'u sukayi da Faridan, maza tayi ta d'auke idonta cike da kunya snn ta riqe mishi hannu, rankwafowa yayi daidai wuyanta da muryan shagwab'a da ya sauqe mata kasala gaba d'aya yace "Ina duba Baby na", cike da jin kunya a hankali tace "Yaa Abu Farida fa na nan" kallon Faridan yayi, suna had'a ido ya sakar mata wani irin kallo, babu shiri ta bar abinda takeyi ta rage wutan stove d'in tayi waje da sauri, tana fita ya juyo da Batuul d'in, y'ar rigar dake jikinta ya d'age ya shiga making circles a flat tummy d'inta da yasata jin wani sabon feeling na daban na ratsata, a hankali yace mata "Meh zaki bawa Farida?", sai lokacin abin ya fad'o mata d'ago kai tace "Nima ban sani bafa, kawai zan bata kosu bracelets d'ina ko?", ta tambayeshi, murmushi yayi ya janye hannunshi cikin rigan nata ya kamota yace "muje ki gani sai ki duba ki ga In yayi a bata", babu musu ta bishi a baya suka fita waje, Farida na ganin fitansu ta koma kitchen taci gaba da abinda takeyi tana murmushi cike da jin dadin irin xaman Bestyn nata da yayanta, suna shigowa daidai nan Faridan ma ta fito riqe da bowl d'in oat a hannuta tana jujjuyashi, a nan ya bar Batuul ya haura sama, ba a jima ba ya sauko yace su wuce, cikin y'an minutes suka isa airport, sai lokacin Batuul ta dad'a tabbatar da tafiyan Farida, kamar kar su rabu harda k'wallanta, k'ok'arin fitowa ta shigayi daga motan zata raka Farida yayi maza ya rik'ota yana kallonta yace "Ina zakije haka?" , zumb'uro mishi baki tayi cike da shagwab'a tace "zan rakata mana", kai ya girgiza yace "kinada hankali zaki fita a haka ko mayafi babu?, dubi kayan dake jikinki?", kallon kanta tayi taga koh kayanta are, wandone jikinta sai jacket iya gwiwa da hood amma yake fad'a mata wai kada ta fita a haka, rai b'ace ta koma ta kwanta sai Faridan ce ta zagayo tayi hugging d'inta, dan takaici kasa magana tayi sai hawaye da ta dinga yi, shi ya d'auki jakan tsaraban ya rakata dashi yace mata inji Batuul, ya k'ara mata da kud'i masu yawa, har saida yaga ta shiga jirgi sannan ya juyo, a mota ya tadda Batuul har tayi kukanta ta gode Allah, ko sau d'aya bata kalleshi ba bayan ya dawo, haka ya k'arashi surutunshi suka isa gida, yana parking ta bud'e mota ta fita a guje, a gujen shima ya bita dan har ranshi yakejin gudun nata snn gashi ba lafiyane da ita isasshe ba, daidai takai k'afanta kan 5th stair case ya cimmata, wani razanannen k'ara ta saki da yasata durk'ushewa k'asa, binta yayi ya kamota jikinshi yana mata wani irin kallo yace "Fatima ban hanaki tsalle ba?, bakida hankali koh?, next time you try this shit I will slap you", gaba d'aya bata sanma mey yake fad'i ba sai yarfe hannu da takeyi, kuka sosai ta shiga yi tana k'iran sunan Auny tana riqe da cikinta, rud'ewa yayi ganin da gaske take ya d'agota yace "Batuul talk to me, cikin ne?", a hankali ta shiga gyad'a mishi kai a wahalce, duk ya rasa mey ma zaiyi dan duk ya rud'e, cak ya d'auketa sukayi asibiti, ikon Allah ne kawai ya kaisu lafiya dan baisan irin driving d'in da yayi ba, likitocin this time ma cikin gaggawa suka amsheta, sai kukan wahala take tana k'iran sunan Aunty, har dare likitocin na kan Batuul sun kasa gano Ina matsalar take gashi duk wani taimako da zasuyi sun mata shi amma babu wani ci gaba, Abu kam tsayawa kawai yayi yana kallonsu ya kasa cewa komai, kamar shi ke ciwon har fad'awa yayi daga yini d'aya. Sai karfe takwas da wani abu na daren bacci ya dauketa shi ma sai juye juye take, Abuturrab dake xaune gefenta ya tsura mata ido cike da tausayinta ganin yanda ta wani rame daga safen xuwa dare, mikewa yayi da kyar ya nufi office din likita, nan ya shaida ma likitan in dai cikin xai bada matsala kawai a cire sa, ficewa yayi daga office din ya nufi gida kafin ta tashi don dauko wayarsa, Ajiddeh na xaune parlor kamar ko da yaushe, yau dai sai ya gaya mata ma'anar fitar da yake da asuba ko sallama babu baxa kuma ta kara ganinsa ba sai dare, bin sa da kallo tayi ganin ko kallonta bai yi ba ya haura sama, mikewa tayi ta bi bayansa, xaune ta samesa gefen gado, da ganinsa kasan akwai matsala, ta karaso da sauri ta xauna gefensa tace "Me ya faru babe? What's wrong?" Rike kansa yayi bai ce komai ba, ta dago kansa tace "Talk to me mana, me ya faru" Da kyar ya iya bude baki yace "Batuul!" Ji tayi kamar ya soka mata mashi, lokaci daya xuciyarta ya shiga tafarfasa, ta dake tace "What about her?" Cike da confusion yace "I just don't know, tana asibiti" wani farin ciki ya lullube Ajiddeh, sai dai cike da damuwa kamar gaske tace "Ayya, Allah ya bata lafiya" mikewa yayi da kyar ya dau wayarsa xai fita, tace "plss xan bi ka muje in dubata babe" bai tanka ta ba ya fita, ta mike cike da murna ta dau hijab ta sa ta bi bayansa da sauri, har ta shiga motar bai ce mata komai ba ya tada suka kama hanyar asibitin, ba karamin tashi hankalinsa ya kuma yi ba ganin likitoci a kanta, su Ajiddeh kamar na kirki ta dinga kwantar masa da hankali wai she will be fine. Likitocin na fita ya shiga Ajiddeh na biye da shi a baya, rungumeta yayi ta kankamesa tana kiran sunansa cikin kuka, a rikice yace "Don't worry Fatima xa a cire babyn ki huta kin ji" girgixa masa kai kawai take tana kuka sosai, Ajiddeh ta xauna gefenta tana mata sannu, rike hannunta Batuul tayi ta fada kanta tace "Wayyo Mutuwa xan yi Anty ki taimake ni cikina" shiru Ajiddeh tayi tana kallonta lokaci daya jikinta yayi sanyi jin ta ambaci mutuwa.
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

78

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

A hankali Ajiddeh ta shiga girgixa kai da kyar tace "No! Baxa ki mutu ba, Allah xai baki lafiya kin ji" Abuturrab da ya gama rudewa jin abinda tace ya rike hannayenta yace "Noo no baxa ki mutu ba Fatima, don't worry xa a cire babyn ki huta, bana so kuma, xa a cire soon kin ji, kar ki kuma cewa xa ki mutu plss" ko kadan Batuul bata san abinda suke cewa ba don ita kadai tasan abinda take ji a lokacin, tayi wani kara da ya kuma rudar da Abuturrab da Ajiddeh tace "Don Allah Anty ki ce ya kai ni gun Antyna nasan mutuwa xan yi, wayyo cikina" Abuturrab ya rungumeta a rikice yace "Stop this Fatima, ki daina kiran mutuwa plss" hawaye ne ya ciko idonsa yace "No! Baxa ki mutu ba wife, baxa ki mutu" Ajiddeh da duk jikinta yayi sanyi ita ma ta shiga hawayen a hankali tace "Baxa ki mutu ba, Allah xai baki lafiya" mikewa tayi da kyar ta fice daga dakin, ta tafi nesa da ward din, layin Mum dinta ta shiga kira, bugu uku aka daga, bangaren Mum tace "yauwa 'yar gari dama yanxu nake kokarin kiran ki, ya ake ciki kin ga alamar...." A sanyaye Ajiddeh ta katse ta tace "Mum kinsan me? don Allah kice a dakatar da aikin nan tukun....." Cike da mamaki Mum tace "A dakatar da aiki? Saboda me?" Da kyar Ajiddeh muryarta na rawa tace "Mum kinga fa kila mutuwa xata yi, kuma..." Sai ta fashe da kuka tace "Mum ni dai a dakata tukunna....." Wani uban ashar mum ta kunduma mata a fusace tace "Shegiya sallamammiya, kin san nawa na kashe 'yar abu kaza kaza, a dakatar da aiki??? Wani irin zagi Mum ta kuma k'undumo mata da har saida ya tsorata ta, a fusace ta diro daga kan gadon da take cikeda masifa tace "Keh kinsan mey kike cewa? to kinyi kadan Ajiddeh, a xuri'armu bbu warce ta taba zama da kishiya, baxa kuma a fara a kan 'yar cikina ba, Aliyu naki ne ke daya don ubanki, Ajiddeh cikin kuka tace "Mum nifa bance zan zauna da ita ba, kawai dai bana son ta mutune", Fusata Mummy ta sakeyi har wani gumin masifa ke tsattsafo mata a goshi, rai a b'ace tace "keh don ubanki ki fita idona kinaji, shegiyar yarinya da bata san abinda takeyi ba, zur'armu kaf babu wacce ta zauna da kishiya, mey ma za ayi da zama da kishiya, Allah bai d'aura mana ba kema kuma baki zama da ita, ita da take gantalalliyar kishiya ma har aka munafurce ki akayi komai shine kike tausayinta, indai ni haifeki kika kuma tausayin yarinyar nan sai. na tsine dan haka in zaki dawo hankalinki tun wuri ki dawo kisan inda dare yayi miki, wawiyar yarinya kawai, kina abu sai kace bani na haifeki ba, K'anwar uwarki ce yarinyar da zakice mituwa zatayi ko kuma in ta mutun asara ne dake, mutuwa kuma kamar tayi shi daga ita har shegen dake cikinta, kaji min wahalalliya mara wayo, to kin yi k'adan yanxu ma shiri nake xan koma kauyen don ba a gama aikin ba" Ajiddeh ta fashe da kuka sosai tace "Allah mum ni dai ba ruwana, kar ta je ta mutu...." Wani raxanannen tsawa Mum ta daka mata ta dinga kunduma mata zagi tace ", Ajiddeh ta katse wayar ta jingina da bango hawaye na sakko mata, da kyar ta ja kafa ta koma ward din, hankalin ta ya kuma tashi ganin halin da Batuul ke ciki, likitoci biyu a kanta, karasawa tayi da sauri ta xauna kusa da ita jin abinda take ta cewa, ta rike hannunta hawaye na sakko mata tace "Baxa ki mutu ba, sai lokacin ki yayi" Abuturrab dake xaune ya rike kai ya d'ago da kyar yana kallonsu da idanuwansa da suka kada, ya karbi wayar Ajiddeh don bai ma san inda nasa yake ba, ya fita don kira Ammah shi da likitocin xa su ji ta nasa da an cire cikin a nn take kawai amma sun ki wai sai bayan awanni idan suka gama binciken da suke, rungume Batuul Ajiddeh tayi, sai ce mata take cikinta, dubara ne ya fado ma Ajiddeh ta shiga tofa mata addu'a a hankali, Abuturrab na fita ya kira Ammah, tana d'agawa ya kasa ce mata komai, tayi sallama yayi uku kafin da kyar yace "Ammah, Batuul...." Jin muryarsa Ammah tace "Abuturrab, lafiya me ya faru" da kyar ya kuma cewa "Batuul..." Nan hankalin Ammah ya tashi ba kadan ba tace "Kayi min magana mana Aliyu, me ya samu Batuul din" k'asa bata amsa yayi hawaye na sakko masa, nan hankalin Ammah ya kuma tashi barin da taji yayi shiru kuma tasan hawaye yake shirun nan, don ita ta haifi abunta, tsawa tayi masa tace "Kana da hankali kuwa Aliyu, baxa ka fadi abinda ya samu Batuul din ba" da kyar ya bude baki yace "Bata da lafiya ne" tayi kokarin boye tashin hankalinta tace "Subhanallah! Tun yaushe?" Yace "jiya" sosai hankalinta ya tashi don tasan ba abu kadan bane Abuturrab xai ma hawaye, tace "Me ya sameta?" Ya girgixa kai bai ce komai ba, Ammah tace "ka bude baki ka min magana Aliyu, farida fa?" Da kyar ya iya cewa 'Daxu na Kai ta airport " Ammah tace "Dawo min da ita immediately" "toh" kawai ya iya ce mata ta katse wayar hankali tashe tayi part din Abui. Juyawa yayi ya koma ward din, har lokacin Batuul na jikin Ajiddeh idonta lumshe, sai dai a hankali take kukan yanxu sai ajiyar xuciya da take saukewa jin kamar an xare mata ciwon, ita ko Ajiddeh bata fasa to fa mata addu'a ba, don bata ma san Abuturrab ya shigo dakin ba, tsaye yayi jikin bango yana kallonsu hankalinsa ya d'an kwanta ganin Batuul ta nutsu, karasawa yayi gun gadon ya xauna gefensu ya kamo hannun Batuul yana kallonta, a hankali ta bude rinannun idonta tana kallonsa, Ajiddeh ma ta juya tana kallonsa, kauda kai Batuul tayi, murya can kasa tace ma Ajiddeh xata je bayi, Ajiddeh ta mike ta d'agata ya bi su da kallo har suka isa bayin, a nan bakin kofa Ajiddeh ta jira ta tafito ta kuma kama hannunta suka koma kan gadon, A hankali Abuturrab na kallon Batuul yace "Ya daina cikin?" Kai kawai ta gyada masa, ya kalli Ajiddeh yace "We are leaving for Nigeria gobe" ita ma ta gyada masa kai kawai. Wayarta ne ya shiga ring a hannunsa ya mika mata ta karba ta ga Jainaba ce, gabanta ya fadi ba kadan ba taki d'agawa ta ajiye, ta juya tana kallon Batuul da ta rufe ido har bacci ya fara daukanta ta ci gaba da mata addu'a a xuciyarta, Abuturrab ya mike ya fita, ba a dau lokaci ba ya dawo, yana kallon Ajiddeh yace "Xa a cire cikin yanxu, it's time" Ajiddeh tayi shiru tana kallonsa sai kuma tace "saboda me?" A hankali yace "She's suffering babe" girgixa masa kai tayi duk da wani abu da taji ya tokare xuciyarta tace "No! Allah xai bata lafiya a bar mata" a sanyaye yace "A'a gwara a cire mu samu rest of mind" da kyar Ajiddeh tana kokarin maida hawayenta tace "if dat's ur only child or hers a duniya fa," d'an murmushin karfin hali yayi yace "baxan iya jure ganin tana wahala haka ba, ke kya haifa min masu yawa idan Allah ya yrda" duk yanda Ajiddeh ta so convincing dinsa a bar cikin kin yarda yayi, mikewa tayi daga karshe ganin da gaske cire cikin xa ayi, ta dau wayarta ta fita, Ammah ta kira yana fara ringing ta d'aga, sama sama Ammah ta amsa gaisuwarta don tun kiran Abuturrab bata da nutsuwa barin da ta kira can Maiduguri taji ciwon Batuul har da sa hannu, Ajiddeh da ta ma rasa abinda xata ce a hankali daga karshe tace "Ammah dama wai Batuul ce ba lafiya kuma laulayi take, shine Aliyu wai a cire cikin nayi masa magana ya ki saurarata" tana maganan ne da kyar don wani tukuki take ji a xuciyarta ta rasa dalili, a dakile Ammah tace "Toh don uwarsa tunda bashi da hankali ba sai yasa a cire ba muga, wawa da shi ba xai rike addu'a ba an tasa shi da iyalinsa a gaba sai haukan banxa shi d'an boko, ni ban taba gani soko mara wayau kamar Aliyu ba, kuma yana tare da wahala in har baxai rike addu'a ba, Batuul kuma ta Allah ba ta mutane ba, bbu abinda xai sameta sai Wanda Allah ya rubuto mata, babu abinda aka isa ayi mata, ciki kuma sai ta haifesa lafiya idan Allah ya yrda, ki bani gantalallen" jikin Ajiddeh yayi sanyi ba kadan ba lokaci daya hawaye ya cika idonta ta ja kafa da kyar ta koma ward din ta mika ma Abuturrab wayar, hannu yasa ya karb'a batareda yasan ko waye ba ya kara wayan a kunnenshi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.