Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 74 of 124
Sai da suka shigo gida hankalinta ya fara tashi, Abu kam ko a jikinshi kai tsaye ya shiga cikin gidan ta bi bayansa kamar munafuka, Ajiyar zuciya ta sauk'e ganin Ajiddeh bata palon ta nufi sama da gudu, murmushi yayi dan yasan gudun mey takeyi shima ya haura sama, dakinsa ya shiga ya fada kan gado ya lumshe ido, murmushi kawae yake ba tare da yasan dalili ba.
(Sorry 馃檱 for d short chappy sisters, I got test to write tomorrow, wish me luck 馃å´Â, I promise to update you guys tomorrow In sha Allah) 馃挅馃æŒÂBATUUL馃挅馃æŒÂ
59
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Da mamaki Ajiddeh ke dubanshi daga bakin k'ofa ganin ya dawo da wani kayan ba da wanda ya fita ba, kuma tun biyar ya fita yace mata yanzun nan zaije ya dawo amma sai Yanzu yake shigowa, ga shegiyar nan ma tun d'azu take mata knocking taqi bud'e mata k'ofa, tsaki tayi ta k'arasa shigowa d'akin, kai tsaye gadon da yake kai ta nufa ta zauna daidai kanshi ta shiga tashin shi, a hankali ya bud'e lumsassun idanuwanshi ya d'aura kanta, had'e rai tayi a dole ya b'ata mata rai tace "Aliyu tun yaushe ka fita ka barni gidan nan, daga cewa yanzu zakaje ka dawo shine ka shanya ni nan", murmushin shi mai narkar mata da zuciya yayi ya riqo hannunta ya janyota jikinshi, a hankali ya d'aura bakinshi daidai kunnenta cikin rad'a yace mata "keh wai baki iya kula da miji ba?, ba girki, ba gyaran gida, babu tsaftace ko ina sai kanki kawae, amma kinfi kowa iya mita, a haka ake nuna son?", jikin tane yayi sanyi jin abinda ya fad'a mata, toh me kuma ya kawo wannan maganan, d'ago kanta tayi ta kalli fuskanshi taga idonshi na lumshe ne har lkcn, rolling idanunta tayi a ranta tace kai ka sani, har lokacin idonshi lumshe ya sake jawota ta fad'o jikinshi yaci gaba da cewa "ko kinaso in samo wacce zata na yi min dukka wannan abun kinga kema sai ki koya gunta?", a firgice ta d'ago tana kallonshi tace "mey kake nufi Aliyu", sai a lokacin ya bud'e lumsassun idanunshi ya zuba mata su, murmushi yayi ganin expression d'in dake fuskanta ba tare da ya damu ba yace "sai in qara aure mana, kinga kin samu mai koya miki nima na samu mai bani abinci ba sai ina zuwa restaurants ba", gaba d'aya ji tayi iskan d'akin yayi mata kad'an, hannu tasa ta warware dogon gashinta mai tsayi da laushi tana mishi wani matsiyacin kallo cike da masifa tace "A ina d'in wai zakayi aure, ba dai ina gidan nan ba, wlhy Allah indai da raina baka k'ara aure, sai ina maka girki sannan zaka san ina sonka?, tun farko daga gidanmu ni ban saba da wahala ba shiyasa aka nema min masu aiki kace baka sonsu ka koresu to ya kake son inyi da kai? sai yanxu kuma kace min wani ban Iya komai ba, dama can meye auren, abun da yake ciki ai ina yi maka, shine yanzu zaka tsiro da zancen aure, duk shegiyar ma da tayi gigin aurenka sai na lahanta ta ta rasa mai aurenta wllh", tana huci ta kare maganar, da mamaki yake kallonta, dariya maganarta ya bashi sosae, wai in tans raye bai k'ara aure", kanshi ya kad'a yace "calm down, wannan hargowa tun banyi auren ba, ki bari in nayi sai kiyi using energy d'inki sai kiyi fad'an dagaske", idonta ne ya cicciko da hawaye jin abinda Aliyu ke fad'a mata, a fusace ta mik'e zata bar d'akin yasa hannu ya fizgota ta fad'o kanshi, kokawa ta shigayi dashi a kan ya k'yaleta amma yaqi, ta fashe da wani matsanancin kuka, a hankali ya d'aura bakinshi kan wuyanta ya fara kissing har ya gangaro kan lips d'inta, kasa resisting d'inshi tayi da kokawar da takeyi dashi, lkci daya ta hadiye kukan ta bada Kai.
Batuul na shiga d'aki ta fad'a gado, lumshe ido tayi tana tunanin abinda ya faru yau gaba d'aya, tunda ya sauk'e ta makaranta ya bata kud'i, bud'e mata k'ofa da kuma tafiyansu gidanshi mai kyau da abunda ya dinga yi mata yau, lumshe ido tayi tana tariyo duk event d'in da ya faru yau, wani iri ta dinga jin kanta, gaba daya ta k'asa daina tunawa, jiki a sanyaye ta mik'e ta cire Hijabin jikinta da kayan dake jikinta, jin k'anshin turarenshi jikin kayan yasa ta d'aura rigan kan fuskanta, wani irin weakness taji k'afanta ya fara, a hankali ta koma kan gadon ta zauna har lokacin rigan na fuskanta, a hankali ta cire ta ajiyeshi gefe, da kyar ta mik'e ta janyo towel ta d'aura ta fad'a toilet, nanma tafi 15mins cikin bathtub d'in da ta cika da ruwan zafi, sai da ta gaji da zama dan kanta ta mik'e ta fito daga ciki, alwala tayi ta canja pad d'inta sannan ta fito, gaban vanity table d'inta ta zauna ta shafa mai ta fesa turarukanta masu sanyin kanshi sannan taje closet d'inta ta ciro kayan bacci, short sleeping gown fari da fuskan Panda daga gabanshi ta saka, sai da ta karanta Qur'an a wayarta sannan ta kwanta bacci, ta dde kwance sae juye juye ta ke, da ta bude ido Abuturrab take tunawa, ta rasa dalili, sae kusan midnyt bacci ya d'auketa, washegari kamar yadda ta tashi jiya haka yau ma tayi, da kayan baccin nata ta sauk'o kitchen ta shiga had'a musu breakfast dan 8 take da lecture, pancake paste ta kwab'a sannan tayi strawberry syrup ta tafasa musu fresh milk ta juye a flask, a jikinta taji kamar ana kallonta daga bakin k'ofa, a d'arare ta juyo ta kalli k'ofan, wani irin k'ara ta saki zata bi k'ofan baya ta fita ganinshi tsaye bakin kofar yayi folding arms d'inshi yana kallonta, cikin hanzari ya k'araso cikin kitchen d'in yayi maza ya kamota, babu abinda jikinta yakeyi sai rawa gashi ta kasa barin su hada ido, a hankali ya jawota jikinshi ya rungumeta tsam ganin ta tsorata, patting bayanta ya shiga yi yana rad'a mata subhanallah kunnenta, har sai da yaga b'arin da jikinta keyi ya ragu sannan ya sassauta rik'on da yayi mata yana kallon kyakkyawan fuskarta da hawaye ya ziraro yace "sarkin tsoro, ni d'in kike tsoro, ina zakije da kika sa gudu, ko kamanni na ne ya canja maki?", ya sa yatsanshi yana share mata hawayen, d'an k'aramin bakinta ta turo snn ta d'ago kanta ta kalleshi tace "ni ba tsoro ka bani ba, meye xa ka tsaya a bakin k'ofa kana kallona", dariya maganarta ta bashi amma ya dake ya d'ago fuskarta da ta sauk'ar yace "jiya ma by this time kika tashi?", kanta kawai ta gyad'a mishi, saketa yayi ya koma inda burners d'in suke, pancakes d'in da ta fara soyawa ya tsaya yana kallo, "did you make all this?", ya fad'a tareda juyowa yana kallon fuskanta, a hankali ta gyad'a mishi Kai, d'ayan tukunyar dake kan wutan ya bud'e, aroma d'in ne ya sashi yaja d'an baya yana kallonta yace "wannan ya sunanshi?", wara ido tayi a hankali tace "cream in chicken soup", kai ya gyad'a yana murmushi don ji yayi ta burgesa ba kadan ba, dawowa yayi gabanta yana kallon fuskanta yace "who taught you all this", a tak'aice tace "Aunty", ya daga kafada don yasan amsan kenan, "What time do you have lecture today?", ya tambayeta yana kallonta, tace "8:00", waje ya samu ya zauna kan kujeran island din yana duba kitchen timer yace "and its 6:30 now" "kin iya kunu", mamaki tambayan ya bata a hankali tace mishi " Yeah na iya,wane iri?", murmushi yayi yace "any type", kai ta gyad'a mishi tace "Na iya kunun gyad'a, Mard'om, tsamiya, kanwa, alkama sai Kunun Accha", kai ya gyada alamun he is impressed yace mata "Na gyad'a nake son sha yanxu, zaki iya yi", d'an karyar da kai tayi tace "toh ai babu gyad'an yin kunun", bai ce mata komai ba ya tashi ya isa cabinet d'in ya bud'eshi sannan ya Ciro bucket d'in nik'akk'en gyad'a, da mamaki ta tsaya kallonshi, smiling yayi ganin irin kallon da take mishi yace "Ammah packed everything for me, I love traditional food yhu knw", tab'e baki tayi ta isa Inda bucket d'in yake ta bud'e tare da d'an duk'awa tana duba gyad'an, a hankali bayan ta d'ago ba tare da ta bari sun had'a ido ba tace mishi "zanyi", yana zaune yana kallonta cikin 25mins ta had'a kunun gyad'a mai scrippers, sai da yaga ta gama ta fara kaiwa dinning shima ya fito daga kitchen d'in ya koma Palo, shi yace basai ta share gidan ba yau tunda time ya k'ure, bata ce komae ba ta koma kitchen din don tsaftace ko ina.
Ajiddeh kam K'aran wayanta ne ya tasheta daga bacci, tsaki tayi ta jawo wayar, time ta fara gani taga k'arfe shida da rabi na safe, juyawa tayi taga Abutturab baya d'akin sannan ta d'aga wayan a tsorace ganin mai k'iranta at wannan lokacin, a d'arare tace "Hello Mummy" tana jin tsoron kar ace wani abun ne ya faru a gida, daga d'aya b'angaren Mum tace "kina jina, Malamin nan yace aiki fa bazai yiwu ba sai kina nan kuma yace Cikin kwanaki uku in baki zo ba komai zai iya faruwa da shi kansa bae gano ba, dan haka duk yadda za ayi kisan yadda zaki yi ki iso yau d'innan ba sai gobe ba", a tsorace da jin abinda Mum ta fad'a mata tace "Mum ban san ko zai bari inzo ba", inji Ajiddeh, "kina ma da hankali kuwa, nace miki komai zai Iya faruwa shine kike cemin bazai barki ba, toh koh bai bari ba bazaki taho ba inyaso a San abin yi daga baya", maganganun Abuturrab na jiya ta tuna, hankalinta a tashe tace "toh toh naji Mummy, yanzu zanje in sameshi ince mishi an min waya ance bakida lafiya kuma kinason ganina, nasan in yaji haka zai bari, sai kiyi all things possible yadda bazai gane ba", da haka sukayi sallama akan zata k'irata duk yadda akayi, tashi tayi tana matsar k'walla yadda zatayi pretending wa Abu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.