Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 92 of 124

A bangaren Ajiddeh kuwa kuka ta dinga risga kamar an aiko mata lbrn mutuwa, ganin kukan ba taimakonta zaiyi ba ta d'auko waya ta shiga neman layin Aliyu, har ya gama ringing bai d'auka ba, bata dena k'iran ba har saida taji an d'auka snn ta fashe mishi da wani matsanancin kuka tareda sakin wani razananne k'ara da ya sashi rintse ido, kuka takeyi sosai ta shiga koro mishi jawabin k'arya da gaskiyan abinda ya had'ata da Farida kuma yazo ya fita da Farida inba haka ba zata bar mishi gidanshi, shi yasan Farida bataji amma bai tab'a kawowa har zata iya yiwa Ajiddeh duka ba, ce mata yayi gashi nan zuwa, kan gadon ya koma yana tunanin barin Batuul ita kad'ai a gidan, gaban desk top d'inshi yaje yayi activating CCTV snn yayi securing gidan, pecking d"inta yayi snn ya fita ya bar gidan, cikin minti kad'an ya isa gida, kai tsaye d'akin Ajiddeh ya isa ya tarar da ita xaune kan gado sai kuka takeyi duk bakinta ya kumbura, nan taci gaba da shirgo mishi k'arya da gaskiya, ba karamin baci ransa yayi ba ya shiga rarrashinta, ganin yadda ranshi ke b'ace ta fara murnan zai yiwa Farida koran kare a gidan, da murna ta biyo bayanshi, k'ofan d'akin Batuul ya tura, Farida na kwance kan gado tana playing Word Crush a wayar Batuul, mik'ewa tayi xaune tana kallonsu duk da yanda gabanta ke faduwa ganin yanayin fuskanshi hakan bai hanata daure fuska ba, ta mike tsaye tace "Yaa Abu tun d'azu fa na dawo ina ta nemanku, ina Besty na take itama bata nan", ta shiga lek'a bayanshi ko zata hango Batuul, sai lokacin ma Ajiddeh tasan Batuul bata gidan ashe, fizgota yayi yace "in the next 5 mins ki tabbatar kin gama tattara kayanki you are going back home", ganin murmushi shimfid'e fuskan Ajiddeh ta had'a rai tayi kamar bataji mey yace ba tace "Yaa Abu kace ta bamu waje zanyi maka magana, bana son gayyar sa ido", wani tsawa yayi mata yace "Ba magana na miki ba?", had'e rai tayi tace "Toh Yaaa Abu mana, nifa hutuna bai k'are ba kuma ni ba wajenku nazo....", wani tsawan da ya daka mata yasa ta razana ta kasa k'arasa maganan, tace "Yaa Abu ni gun Batuul Ammah ta siyamin ticket nazo fa", gnin yana yiwowa kanta yasa ta fasa ihu ta isa wardrobe ta shiga had'a y'an kayanta, Ajiddeh duk da tana murna amma ba haka taso ba, taso ya rama mata dukan da Farida tayi mata yayi mata korar kare, suna tsaye Farida ta shiga had'a kayanta tana hawaye har ta gama tazo ta tsaya gabanshi tace "Toh ina Batuul d'in, mu jira ta dawo sai in tafi", bai kulata ba ya kamo hannunta ya shiga janta har suka sauk'o k'asa, Ajiddeh kam hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba dan dama so take a barta daga ita sai Batuul a gidan, har k'asa ta biyosu tana yiwa Farida habaici, itakam ko kallo bata isheta ba, suna shiga mota ya tada suka tafi.
[10/1, 06:12] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

76

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Har jirginsu Aunty Jainaba ya sauk'a Nigeria hankalinta yaqi kwanciya kan abinda Ajiddeh ta fad'a mata, inko gaskiya ne ai da sun kad'e dan kishiya ba abar so bace ko cikin mafarki, bazai ma yiwu bane, Aliyu ya raina musu hankali, amma koma menene zasuyi maganinshi maci amana kawai, so take kawai ta isa gida ta fesawa Mummy lbrn cin amanan da d'an matsiyatan nan yayi musu, Dan ba Ajiddeh kad'ai yayiwa ba, ko jiran driver batayi ba ta tari Taxi tayi hanyar gida, suna isa tacewa driver taxi ya jirata a kawo mishi kud'inshi ta shige cikin gida jikinta sai b'ari yakeyi kamar ita aka yiwa kishiyar, a hakimce ta tadda Mum d'in Ajiddeh zaune a parlour, da mamaki Mum ke duban Jainaba da ta fad'o cikin d'akin ko sallama babu tace "Keh kuma daga ina haka kamar ana tunkud'oki, mey ya faru kika dawo da wuri haka keda zakiyi har sati biyu", waje ta nema ta zauna jiki na b'ari, Mummy ta gyara zama tace "Keh ko lafiya haka, Ya Ajiddehn take?", gumin da takeyi ta goge snn ta shiga korowa Mummy bayanin duk abinda ya faru tun zuwanta har zuwa zancen cikin dake jikin Batuul da kuma abinda Ajiddeh ta fad'a mata kan cewa Batuul matar Aliyu ce, wani irin zabura Mummy tayi daga kan kujerar da take zaune ta dafe k'irji tana rafka salati tareda cire d'ankwalin kanta da ya bayyana gashin kanta mai tsawo da shek'i tana fifita dashi dan wani irin zafi takeji duk da Acn dake aiki, tace "Jainaba bana son zancen banza, wane Aliyun ne yayi aure?, ba dai na Hawwa ta ba, ina ba Aliyun Ajiddeh bane ya k'ara aure" Jainaba dake zaune ta mik'e tace "Shi d'in ne kuma ma dan wulak'anci irin nasa har ciki ke gareta yanzun, wannan tsinanniyar yarinyar wai itace matarsa duk ba a sani ba", Cikin d"aki Mummy ta shiga sai gata rik'e da gyale da jaka tana ta sababi tace "Ni Bilkisu zata wulak'anta, duk burin da naci kan Ajiddeh? Su da zaman lafiya saida su ga wasu nayi, shima munafikin Aliyun shine harda dukar min y'a ko?, toh duk sai sunci ubansu gabaki d'ayansu dan sai nasa sunyi kuka da idanunsu munafukai kawai, wannan ciki sai ya zama sanadin rushewar farin cikinsu baki d'ayansu, sai na nuna musu kan kishiya babu abinda bamayi, munfi k'arfin zama da ita koda tadda ta mukayi bare kuma an kawo mana ita a munafurce" ta fad'a tareda wani d'an guntun murmushin takaici ta kalli Jainaba da ta koma ta zube kan kujera tsabar gajiya tace "Yaya ina kuma zamu? Ni wlhy duk na gaji, in na huta sai mu tafi", ta watsa mata wani irin kallo tace "bakida hankali inaga, ace miki anyiwa Ajiddeh kishiya keh har lokacin hutu ke gareki?, ai in kinga mun huta to sai naga na d'agawa Bilkisu hankali itada Zuri'arta baki d'aya naga sun wulak'anta sun d'and'ani bakin cikin da suka jefa y'ata snn zaki samu damar hutawa, kan y'ay'ana biyun nan babu abinda bazanyiwa mutane ba, bare ma Ajiddeh wacce tafi komai soyuwa a gareni, duk burina yana kanta, sun jawowa kansu, maza ki tashi muje", Rai b'ace Jainaba ta mik'e da k'yar dan duk jikinta ciwo yake mata ga gajiya suka fita waje, Sadi driver na ganin Mummy ya washe baki tareda k'arasowa wajenta yace "Hajiya fita zamuyi kenan?", tace "Ehhh maza d'auko mota, Kuje zamu yanzun nan", Jainaba batace komai ba sai bin Mummy da takeyi a baya kamar wata doluwa, saida ya fita da motar bayan sun shiga sun zauna ta dubi Mummy tace "wai gun wa zamu a Kuje?" Mummy ta kad'a kai tace "wajen wani Malamin zamu mana, wannan ma yafi kowa iya aiki danshi baima San Allah ba, Matsafine sosai na bugawa ma a Jarida snn shi ba kowa yakewa aiki ba sai in kanada connection, kin dai San y'an cikin k'auyen garin Abujan nan da basu San wani Addini ba, toh gunshi zamu, Hajiya Ramatu ta dad'e da cemin zata kaini gunshi ban samu munje ba sai kwanaki ne dana rakata kuma naga aikinta ya kammalu in no time kinga har ta samu ta auri wannan Ambassador, matanshi kuma sun shiga gari yanzu daga ita sai y'ay'anta da ta kawo suke zama a can, y'ay'an mijin nata ma ta koresu kuma mijin bai isa cewa komai ba , yanzunma can d'in zamu, dan ni na tabbata banida mak'iyi kamar wanda zai tab'amin y'ay'a", a bakin gate suka tadda driver d'in taxi shida Mangal yanata mishi zuba, Sadi Aunty Jainaba tacewa ya bada kud'in motar ya ciro ya mik'a suka d'au hanyar Kuje, saida suka shiga can cikin k'auyen snn tacewa Sadi sun kawo, nan yayi parking suka fito suka isa y'ar bukkar hatsabibin bokan nasu mai suna Namurje

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.