Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 69 of 124
Batuul kam bayan ta saka pad d'in sai da ta leqo kanta taga ya bar d'akin sannan ta sauk'e ajiyar zuciya ta fito dan mugun yunwa takeji, direct wajen ledojin ta nufa ta tsugunna wajen ta shiga bubbud'esu, na farkon drugs d'inta ne ciki, matsar dasu gefe tayi ta bud'e sauran, da murna ta shiga bud'ewa ganin abincin favorite restaurant d'inta Gordon Ramsay, pack d'in ta bud'e taga roast chicken, lavender, apricot, honey, d'ayan bowl d'in ta duba taga starter ne green apples, turnips sai watercress, wani irin farin ciki kawai takeyi, d'ayan pack ta sake dubawa pasta ne with shrimps kebab, babu b'ata lokaci ta tashi ta wanko hannunta, ko using spoon d'inma baza ta iya ba, sai da taci ta k'oshi ta maida ledojin gefe ta tashi ta cire kayan jikinta ta fad'a toilet, ko ta kan Maganin ma bata bi ta shiga tayi wanka abinta, ta fito kenan d'aure da towel taji an turo k'ofan d'akin, a razane ta d'ago kanta warce ta gani tsaye bakin kofa yasa hanjin cikinta mugun k'adawa, Ajiddeh ta karaso tana murmushi tace "Sannu sister ya jikin?" K'asa cewa komae Batuul tayi sae kallonta take, kuma da ganinta kasan a tsorace take, Ajiddeh bata damu da hakan ba sae ma murmushi da take tace "Amma kina da pad kuwa ko in dauko maki a daki" Batuul ta sunkuyar da kanta da kyar tace "Ina da shi" Ajiddeh tace "Toh Allah ya sauwake, kin sha magani kuwa?" Batuul tace "Ynxu xan sha," Ajiddeh tace "Toh sannu, ni na tafi in kwanta sae da safe" Batuul ta kalleta don har lkcn ta k'asa yarda Ajiddeh ce, a hnkli tace "Toh sae da safe na gode" Ajiddeh tace "Yauwa" sannan ta fice, Batuul ta sauke ajiyar xuciya ta isa inda kayanta yake cike da mamakin Ajiddeh, lotion ta shafa, snn ta shafa turarrukanta masu sanyi kamshi ta fiddo wani sabon sleeping gown dinta mara nauyi me d'an karamin hannu ta sa, ta xura gashinta cikin net, ledan maganinta ta bude ta fiddo magungunan ta sha snn ta ajiye su gaban mirror, ta nufi switch din dakin ta kashe wuta kenan don kwanciya xata yi aka bude kofar dakin, kin kunna wutan tayi don bata son ya ganta ba hijab kuma ta k'asa barin wajen, ya shigo dakin ya rufe kofar, da sauri ta nufi inda hijab dinta yake xata dauka yyi saurin fixgota yana mata wani irin kallo cikin duhun yace "Wae me kike boye min da ban sani ba a jikin ki, baki sanin muhimmancin Hijab sae na shigo dakin ki don rainin wayo koh?" Kokarin kwace kanta ta shiga yi a hannunsa yace "Stay still kar in mareki" sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba, a hankali yace "Ya cikin?" Kin cewa komae tayi ya D'ago kanta yace "Am talking" ta rufe ido kmr yana ganinta murya can k'asa tace "da sauki" yace "Sure?" Shiru tayi bata ce komae ba, yace "ko kina son a maki massaging Abdomen..." Da sauri tace "No na samu sauki" murmushi yyi yana kallon d'an karamin bakinta dake motsi a hankali, yace "Sure?" Runtse ido tayi ta janye hannunta xata bar wajen, ya fixgota jikinsa, wani irin faduwar gaba taji jinta a jikinsa, suka ji an bude kofa can corridor, saketa yyi da sauri ya juya ya nufi kofa.
[8/22, 2:27 PM] .: 馃挅馃æŒÂBATUUL馃挅馃æŒÂ
54
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Yana fita d'akin Batuul a corridor ya tarar da Ajiddeh a tsaye, wani irin kallo ta bishi dashi ganin ya fito d'akin Batuul, bak'in cikinta ta shiga dannewa dan batason tayi anything stupid, murmushin yak'e tayi tace "Baby naga har na fara bacci baka shigo ba shine nace bari in fito in dubaka, ashe kana d'akin Sis dinmu", ta fad'i da wani irin expression shimfid'e fuskarta ta sake kallon d'akin, hannunta ya kamo yace "Yeah ita na shiga dubawa, kinsan batajin dad'i", tace "hakane, nima saida na shiga na dubata before in shiga ciki", yace "kin kyauta", ya rungumota jikinshi suka shiga ciki. Batuul kam yana fita ta tabe baki ta fad'a gado, ko yunk'urin rufe k'ofarta batayi ba tayi kwanciyarta dan ko ta rufe in ya tashi bud'ewa yakeyi, addu'ar bacci tayi ta tofe jikinta da d'akin taja duvet ta kwanta, bata fi minti goma a kwance ba bacci ya d'auketa, k'arfe biyar daidai ta tashi da addu'a bakinta, tana zaune kan gadon har biyar da rabi, sai da taji an idar da sallah ta mik'e ta shige toilet, wanke toilet d'in ta farayi tukunna tayi wanka, mayukanta ta shafa ta gyara gashinta ta tufke da ribbon sannan ta isa closet d'in kayanta, tsayawa tunani tayi na kayan da zata saka, wani gown d'in atampa ta ciro ta saka, ta fesa turarruka sannan ta d'au vacuum cleaner ta tsaftace d'akin tsaf, ta gyara gadonta ta kunna electric burner ta saka turaren wutan, lokaci d'aya d'akin ya d'au k'anshi, sakkowa tayi k'asa ta shiga kitchen, wutan ta kunna taga kitchen d'in na nan yanda ta barshi, shiga tayi ta gama examining komai taga mey zata dafa, fridge ta bud'e , nama ta ciro ta shiga had'a lasagne, tayi peanut butter smoothie, Garlic egg Muffins, sannan tayi offals pepper soup, Abuturrab na dawowa masallaci yaga wutan kitchen a kunne sai dae bai bi ta kan kitchen din ba ya wuce sama dan a tunaninshi Ajiddeh ta sauk'o tayi wani abin, 7:30 Batuul ta gama duk abubuwan da zatayi ta jera komai kan dinning, gyara gidan tayi, takwas dai dai ta gama ta saka turaren wuta gidan ya bade da kamshi me ddi, tea ta hada jin cikinta ya fara ciwo don ta samu ta sha magani, tana gama sha ta haura sama ta dauki magungunan ta sha snn tayi kwanciyarta don sae goma take da lectures, abinda zatayi ne ta rasa kawai ta janyo macbook d'inta ta shiga kallon Boss Baby.
8:30 Abuturrab ya fito sanye da pyjamas d'inshi, tun daga bakin kofa yake jin k'anshin masu dad'i sun had'e gidan, kanshin turaren wuta da na abincin da ta dafa, sauk'owa kan stairs d'in yayi, yadda gidan ke shining ya bi da ido har ya k'araso dining, da mamaki yake kallon kan dinning d'in ganin anyi arranging abinci Kai, k'arasowa yayi ya bubbud'esu, aroma din abincin ya bugi hancinshi, maidawa yayi ya rufe, for the first yaji Batuul ta birgeshi, yasan training d'in Aunty ce ita din, murmushi yayi ya haura sama, d'akinta ya nufa ya tura kofar ya shiga, kwance ya ganta kan gado a kife, bayanta kawai yake gani sai screen din computer, ya karasa cikin d'akin don ganin abinda take kallo, har yazo bakin gadon bata sani ba sai tuntsirar dariyar da take ta faman yi, jin mutum ya zauna kan gadon yasa ta saurin mik'ewa zaune, matsawa tayi daga kusa dashi ta koma can k'arshen gadon, kallonta kawai yake, haka kawae ya samu kansa da murmushi, a hankali ta d'ago idonta taga ita yake kallo, maza tayi ta d'auke nata idon cikin sanyi tace mishi "ina kwana" ya bude ido yace "Morning! Ashe kin iya tashi da wuri?" Kauda kai tayi tace "Eh!" Yyi shiru yana kallonta, satan kallonsa tayi jin shiru suna hada ido ta dauke nata da sauri, ya d'aga kafada yace "Ya dysmenorrhea, ko dama na kwana daya yake maki?" D'an turo baki tayi ta juya masa baya, yyi murmushin da bae san dalilinsa ba, bae kuma ce mata komae ba ita ma bata juyo ba sae dae addu'a kawae take ya tashi ya tafi, wayarta ne dake gaban mirror ya shiga ring, ta mike a hankali ya bita da kallo har ta isa gaban madubin ta dauki wayar, wara ido tayi tana murmushi ta d'aga, sae kuma ta hade rai tace "Kin ban mamaki farida friendship din kenan dama sae yau kika san za ki kira ni koh?" D'aga daya bangaren farida tace "Wayyo Afuwan Besty, kusan kullum sae nayi xancen ki gun Ammah I just don't want to call ki fara min kuka ne wllh, waow hope you are enjoying ur new home, tell me how it is over there, have you made friends? Ina jarababbiyar matar ya Abu, how are you coping with her, hope she isn't giving u tough time...." Batuul ta xaro ido tace "Kai farida spare me those questions, hakuri ya kamata ki fara bani da yawa" Farida ta fashe da dariya tace "Ohhh yhu need to see how happy I am besty, ur voice is so lively, from all indication I guess u are enjoying it over there...." Batuul tayi murmushi a xuciyarta tace uhm lallai kam, ko ba enjoy ba, a fili tace "Ni dae ina Ammah fa?" Farida tace "Tana daki wllh let me put her on the line" Batuul tayi murmushi tace "Alryt!" Juyawa tayi tana kallon Abuturrab da ya kafa mata ido tayi maza ta dauke kanta, muryan Ammah ta ji da fara'a tace "Bitti?" Batuul tayi murmushi ta sulale nan k'asa ta xauna a hankali tace "Na'am Ammah ina kwana?" Ammah tace "Lfya lau Bitti ya gida? In ji ba matsala dae koh? Kar fa ki boye min don Allah" Batuul tace "Babu Ammah ya su Abui?" Ammah tace "Lfya lau suke, ya karatu kina xuwa dae koh?" Batuul tace "Ehh ina xuwa Ammah" Ammah tace "Ma'sha Allah! Ina Abuturrab din" kallonsa tayi taga ita yake kallo, a hankali tace "Ga shi nan, in bashi?" Ammah tace "Bashi!" Hade rae yyi yana kallonta, ta sunkuyar da kanta ta mike a hankali ta isa gabansa ta mika masa wayar, karba yyi ya fixgota lkci daya ta fado jikinsa tun kan tayi k'aran da take shirin yi ya rufe fuskarta a kirjinsa, tayi lamo tana shakan kamshin jikinsa me dadi, wayar ya kai kunne yayi ma Ammah sallama sannan ya gaisheta, da fara'a ta amsa masa don ba karamin dadi taji ba jin suna ma tare, tambayarsa Ajiddeh tayi yace tana dakinta, nan dae ta dinga masa nasiha kamar yanda ta saba a kan yaji tsoron Allah ya xama me adalci tsakanin matansa, dama irin abinda yake gudu kenan shi, don jikinsa sanyi yake, lumshe ido yyi yana sauraranta, ta kusa minti goma tana nasihan nata har lkcn kuma Batuul na jikinsa yaki saketa gabanta sae faduwa yake don she's not use to that, daga karshe ce masa tayi ya ba Batuul wayar, mika mata wayar yyi ta karba ta shiga kkrin kwace jikinta amma ya ki saketa, k'ara wayar a kunne tayi, Ammah tace "Kina jina Batuul" a hankali tace "Eh Ammah" Ammah tace "Kiyi ta hakuri kin ji Bitti, bbu ruwan ki da Abokiyar xaman ki tsakanin ki da ita sae girmamawa, ki kula da ibadun ki, ki xama me tsafta duk da nasan kina da amma ki kara kan na da, ko da yaushe dakin ki da jikin ki ya kasance cikin kamshi kin ji, Farida na nn xuwa idan sun yi hutu" Batuul ta wara ido cike da murna tace "Toh Ammah nagode, Allah kara girma" Ammah tace "Ameen Bitti sae mun kuma waya" nan suka yi sallama Batuul ta d'aga kai tana kallonsa ta ga idonsa lumshe, kokarin xame jikinta ta shiga yi ya bude ido yana kallonta, ta hade rae tace "Makaranta xan tafi ni" saketa yyi ya mike sanin lkcn tashin Ajiddeh yyi, ya fice daga dakin, bin sa da kallo tayi kafin ta lumshe ido ta kwanta kan gado.
Karfe Tara da wani abu ta sakko da shirin tafiya makaranta, xaune ta same su shi da matar tasa kan dinning suna breakfast, Ajiddeh na ganinta ta sunnar da kai don bata so ta sakko ta sameta tana cin girkin ta ba, idon Abuturrab na kanta har ta karaso falon kanta a k'asa ta ce "Ina kwana Anty" Ajiddeh ta kirkiri murmushi tace "Lfya lau sister, ashe kin tashi, nace Aliyu ya shigo ya dubo ki muyi breakfast yace wae ba kya tashi da wuri" Batuul dae bata ce komae ba sae kofa da take kallo, Ajiddeh tace "Toh ki karaso ki karya mana" girgixa kai Batuul tayi tace "A'a na sha tea tun daxu" Ajiddeh tace "Ohk," kofa Batuul ta nufa jin Abuturrab bae ce komae ba, yana ganin hka yace "Ki jira ni gun mota, na aiki driver" toh kawae tace ta fita, Ajiddeh da mood dinta ya canxa lkci daya ta sunkuyar da kai kar ya lura, da sauri ta D'ago tace "Honey ko kuma in kai ta kawae tunda motar biyu ne kar ka makara" ba tare da ya kalleta ba yace "Ae ita ma ta iya driving din, Akwae kudin da xan bata ne shi yasa nace ta jira" Ajiddeh taji kmr ta kwala ihu, wato har kudi xae bata, murmushi ta kirkira tace "C'mon babe nima ae kanwata ce, nawa xaka bata in bata kawae?" Ajiye cup din coffeen hannunsa yyi yace "Don't bother suna da yawa kudin" mikewa yayi yana goge bakin sa da tissue yace "Na tafi babe, sae na dawo take care of ur self for me" yana kai wa nan ya nufi kofa, bin sa da kallo tayi xuciyarta na tafarfasa, tana ganin fitansa ta mike da sauri har tana neman faduwa ta nufi kitchen don lekawa ta window ta ga inda Batuul xata xauna a motar, ae ko dai dai lkcn da Batuul ta bude front seat ta shiga, shi ma ya xaga ya shiga maxaunin driver, ta fashe da kuka da karfi wani mugun tsanar Batuul na k'aruwa a xuciyarta, anya xata iya ci gaba da yin abinda momy tace tayi kan Batuul kuwa, ynxu idan Abuturrab ya ji tana burgesa d'an girkin nan da ta iya ya xata yi da rayuwarta ita da ko indomie ba lallai ta dafa shi ruwa bae yi masa yawa ba, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka ta fito kitchen din tana rerawa. 馃挅馃æŒÂBATUUL馃挅馃æŒÂ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.