Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 62 of 124

Tana zaune 膹akin har k'arfe 8 膹in dare, ga yunwa da ya addabeta, tsoron fita takeyi dan batason ko sake kallon Ajiddeh tayi, ta rasa mey zatayi ku膹in wayarta ma ya k'are da ta k'ira ko su Aunty taji da膹i, Affan 膹inma da ya k'ira 膹azu yaki k'ira har yanxu, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka tayi alwala ta tada sallah isha, sai da ta idar ta gama addu'anta tasha kuka ta tashi ta hau gado ta kwanta bayan ta kashe wutan, ta gwammace ta kwanta da yunwa da ta fito su ha膹u da Ajiddeh, jin an mur膹a k'ofan 膹akin yasa ta k'ara tsorata, a hankali ta sauk'o daga kan gadon zata shige toilet taga haske ya gauraye duka 膹akin, tsayawa tayi a tsakiyan 膹akin ta kasa motsi, k'arasowa yayi cikin 膹akin ya ajiye mata daya ledan dake hannunshi yace "in kin gama tsayuwan naki ga abinci ki 膹auka kici, you get ready gobe by 11 zan kaiki school and mind you kina rufe k'ofar 膹akinki da makulli", wani irin ajiyar zuciya ta sauk'e jin shine, bata juyo ba har ya gama maganan da zaiyi sai ji tayi an juyo da ita, "kina jina ina magana kika min shiru, na fara wasa da ke koh", a hankali tace "Ai naji", saketa yayi ya juya ya fita daga 膹akin tare da kashe mata wuta. Dakin Ajiddeh ya nufa rike da wani ledan ya murda kofar ya shiga, xaune ya sameta can karshen gadonta idon nn nata ya kumbura tsabar kuka, ya ajiye ledan hannunsa tare da sauke ajiyar xuciya ya nufeta, tana ganin hka ta mike da sauri xata bar wajen yyi hanxarin rikota tare da hade ta da jikinsa, ta fashe da kuka tana dukan kirjinsa tace " let me be Aliyu, ka kyaleni, 1st thing tomorrow morning am leaving yhur goddam house, with or without my divorce prove, bna auren kuma, ae ba kai kadai bne namiji a duniya, sae ka xauna da 'yar uwar taka....." Ya runtse ido yace "Stop this Jiddah, yhu pushed me into behaving the way I did, meyasa baki saurarata ne wae, na gaya maki Batuul is only here for sometime, karatu ta xo yi tana gamawa xata koma Nigeria, I love yhu Jiddah bana son duk abinda xae bata maki rai, had it been we are not this close da iyayen Batuul da baxan yrda da xaman ta gu na ba coz it's also a burden to me, plss nd plss Ajiddeh kiyi hkuri ki bar ta tayi karatun ta, her being here is nt for ever, if yhu love me do me this one favour pls babe," tsuke fuska tayi ta kauda kai, ya marairaice yace "Plss babe!" Kuka ta fashe da tace "Shine xaka mareni Aliyu" ya kuma rungumeta yace "Ohh! Am srry babe sharrin shaidan ne plss, idan kuma baki hakura ba ki rama" shiru tayi bata ce komae ba, kissing wuyanta ya shiga yi a hnkli yace "Say something mana babe" lumshe ido tayi don kiss din Aliyu na rikitata, cikin sarkewar murya tace "Naji" bae daina abinda yake mata ba yace "kin amince ta xauna gidan ki har ta gama karatun?" Runtse ido tayi tace "Yeaa!" Yace "Promise!" Da kyar tace "I do love" Kiss din bakinta ya shiga yi passionately tana mayar masa da martani, kan kace me sae ga su kan gado. 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

47

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Yana fita Batuul ta sauk'e ajiyar zuciya ta dawo kan gadon ta zauna, wayarta ta 膹auka ta haska ledan da ya ajiye mata taga tambarin Mc donalds a jiki, 膹an tsaki taja dan bata cika son abincin Mc donalds ba, amma tunda yunwa takeji babu yadda ta iya haka zataci, janyo ledar tayi ta shiga bu膹ewa, kwalin chips ne a ciki sai chicken wings da dip in sauce, sai wani cup da aka sa strawberry shake da ruwa da pine apple drink, ka膹an taci chips 膹in, shake 膹in kawai tasha da 膹an yawa ta tashi ta ajiye sauran da bataci ba kan fridge, toilet ta koma tayi brush ta fito ta kwanta, tafi awa a kwance amma bacci ya k'auracewa idonta, hawaye ne ya fara zirara a idonta, she have never been this lonely gaba 膹aya rayuwanta, dukda ba mai son surutu bace tafi son zama ita ka膹ai amma na yau ya dameta, ko ba komai a gida tana jin motsin y'an uwanta, amma yau hakan ma ya gagareta, tunanin gidane ya sata fashewa da kuka, wayanta ta janyo tana ganin hotunansu da shirmen da sukeyi, tanayi tana kuka wani kuma tayi dariya, tana nan zaune har k'arfe uku, yadda taga rana haka taga dare, gara ma da rana ta 膹an samu ta rintsa, amma yanxu baccin ma ya k'aurace mata, tashi tayi taje tayo alwala, sai da tayi nafilfili tukunna tayi karatun Qur'ani a wayanta, tana nan zaune kan abin Sallah har asuba, tana idar da sllh taji wani irin bacci na fizgarta, nan kan abin Sallah ta gyara tayi kwanciyarta, tana kwanciya bacci ya kwasheta, cikin baccinta kamar a mafarki taji k'aran bu膹e k'ofarta, a 膹an tsorace ta tashi ta zuba mishi lumsassun idanunta , k'arsowa yayi cikin 膹akin yana binta da kallo, sai da ya shigo tsakiyar 膹akin ya tsaya yace "wane irin bacci kikeyi anata knocking baki bu膹e ba", juyawa tayi ta duba inda ta ajiye makullin 膹akin taga yana nan, k'ofan ta sake kallo taga shima da makulli mak'ale a jiki, cikin tsawa yace mata "ba magana nake miki ba, ko bakiji lokacin da nace miki ki shirya zan kaiki school bane kika kwanta kina bacci", sai lokacin ta lura da kayan jikinshi taga har ya shirya zuwa farin shirt mai stripes 膹in bak'i da bak'in wando, windown 膹akin ta duba taga har rana na fitowa ta kalleshi taga ita yake kallo har lkcn, ta 膹auke idonta tace "ai bacci ne ya 膹aukeni bansan safiya tayi ba", ta fa膹a tana zumb'uro baki, k'wafa yayi yana kallonta yace "get ready and come down in the next 15mins", daga haka ya juya ya fita daga 膹akin, tab'e bakinta tayi a ranta tace masifaffe, daga haka ta cire dogon hijabin dake jikinta da rigar baccin ta shiga wanaka, ko minti biyar batayi ba ta fito daga toilet 膹in bayan tayi brush, akwatinan kayanta ta bu膹e ta shafa mai ta ciro wata doguwar riga blue mai dogon hannu ta saka, chappette kawai ta shafa a lips 膹inta ta taje gashin kanta sannan fesa turarukanta masu dadi'n k'anshi ta shafa, a hankali take sauk'owa daga stairs 膹in har ta k'araso cikin palon, yana zaune kan 膹aya daga kujerun palon, Ajiddeh na jikinshi sanye da wasu shegun kayan bacci da ya bayyana duk jikinta, ita ta fara hango Batuul, wani irin harara ta sakar mata kamar idonta zai zazzago ta k'ara shigewa jikin Abu dake k'ok'arin canja channel, cikin ra膹a tace mishi "baby i dont want you to leave", tana yi tana kissing wuyanshi, shima janyota yayi yace mata "dont you worry, i will b back for you, kinga school zan kaita ta fara processing", ita kam Batuul ko kallon inda suke batayi ba tazo ta wuce su zata fita waje, sai a lokacin ya ganta, da ido ya bita har ta fita daga palon sannan ya mik'e yana kallon Ajiddeh yace "Baby ki kula da kanki", ya manna mata kiss a bakinta, hade rae tayi tace " Babe ko gaisheni fa bata yi ba ta wuce" yace "ni din ma ae bata gaishe ni ba, kyaleni da ita" daga hka yayi waje, a bakin k'ofan palon ya tarar da ita tana tsaye, yace "Go back nd greet my wife" daga kai tayi tana kallonsa, ya hade rae yace "Do dat fast my frnd" juyawa tayi a hnkli ta koma falon, tsakiyar falon ta tsaya ba tare da ta kalli Ajiddeh ba tace "Ina kwana" a sanyaye tayi gaisuwan, Ajiddeh ta wurga mata hararan tsana tace "Da ban kwana ba kya gan ni, munafuka 'yan maula" Juyawa Batuul tayi ta bar falon ta fita waje, har lkcn yana tsaye inda ta bar shi, ba tare da ya kalleta ba yayi wucewar shi garage 膹in gidan, tana nan tsaye ya fito da wata dank'areriyar Benz, a hankali take k'arasowa inda motar take ta bu膹e gidan gaba ta shiga, k'anshin turarenshi ne ya cikata, juyar da kanta tayi tana kallon wajen glass, bai ce mata komai ba yaja motar ya 膹au hanyar makarantan, tafiyan minti goma suka isa k'ofar makaranta sae a snn ya juya ya kalleta yace "yhu look for wat to take for breakfast a sch din," ko kallonsa bata yi ba wani irin farin ciki ya ziyarceta ganinta a k'ofar university da kullum take mafarkin zuwa tayi karatu, batasan lokacin da murmushi ya sub'uce mata ba tana kallon yadda students kowa na aikin gabanshi, jin sautin murmushinta da yasa gefen kumatunta lotsawa ya bayyana dimple 膹inta ya sashi juyowa yana kallon yadda take murna, yau ne rana ta farko da ya fara kallonta tana dariya haka, driving yake amma gaba 膹aya hankalinshi na wajenta har ya iso gaban wani building yayi parking motarshi, sai a lokacin ta juyo da murmushinta ta kalleshi taga shima ita yake kallo, hararanta yayi ya bu膹e motar ya fito, ita dai bata fito ba dan baice mata ba, har ya fara tafiya yaga bata fito ba tana cikin motar a zaune, rai b'ace zagayo ya bu膹e mata k'ofan yana mata mugun kallo yace "zaman mey kikeyi da baki fito ba", baki ta zumb'uro ta sa k'afanta a waje, ita batada lokacinshi dan ji tayi duk bak'in cikinta ya yaye, k'wafa yayi ya juya yaci gaba da tafiya, biyoshi tayi a baya har lokacin da murmushi fuskanta, har sukazo k'ofan shiga wani office sannan ya juyo yana kallonta rai a ha膹e, ha膹e dariyanta tayi ganin yadda yayi kicin kicin da fuska sannan ya tura k'ofan ya shige, a sanyaye itama ta shiga a ranta tace masifaffe kawai, nidai yau is my happy day banida time 膹in kowa ta shige cikin office 膹in itama, Office 膹in ta k'arewa kallo, an manna hotunansu su Adam smith, Alfred Marshal, David Ricardo, J.S mills da sauran manyan economists 膹in duniya, wani bature ne zaune kan kujera a office 膹in, da gani shekarunshi zasu kai 60, dogo sannan yana da jiki, hannu ya mik'awa Abu yace "Mr Kyaree you are welcome", baki ta kyab'e jin har sunanshi ya sani, juyowa yayi yana kallon Batuul yace "You can sit down madam", yayi mata nuni da kujeran gefen Abu, kallon Abu tayi taga shima kallonta yake da lumsassun idanuwanshi, kujeran ta jawo ta zauna, tana zaune suka gama maganganun da zasuyi, mutumin ya 膹ago yana kallonta yace "Mrs Fatima are you single?", question 膹inne ya zo mata bazata, ta 膹ago tana kallon Abu dake danna wayarsa, a hankali ta 膹auke kanta ta kalli mutumin da taga sunanshi Stephen xata yi magana ta ji Abuturrab yace "No! She's nt, she's married" kallonsa tayi sae kuma ta sunkuyar da kai, mutumin yyi murmushi yace "Dat's Gud, yhu are welcome to London University of Economics Mrs Fatima kashim Goni" murmushi Batuul tayi jin ynda yyi pronouncing sunan nata, nan Mr Stephen ya shiga yi mata bayanin abubuwan da ya kamata, shi dae Abuturrab danna wayarsa kawae yake, sun kusa minti ashirin office din bayan ta cike wasu forms din da ya bata ta kuma yi signing kafin ya dauko ID dinta na makarantar ya bata, ya kuma yi mata maraba snn ya mika mata timetable da wasu textbuks har uku yyi directing dinta zuwa dept dinta, godiya tayi masa tana murmushi, Abuturrab ya mike ya kuma yi masa godiya mutumin ya basa hannu snn suka fita office din, bin bayansa kawae take farin ciki shimfide fuskarta, da alama ya san kan makarantar sosae ganin ynda yake tafiya with courage abunsa kuma short cut yake bi, xaro ido tayi da ta tuna ae shi ma makarantar yyi if she remembered rightly, ko kadan bata damu da ynda ya hade rae ba farin cikin da take ji a lkcn baxae ma bari ta damu da hkn ba, jefi jefi tana ganin bakaken fata kmr su suna wucewa, har gaban dept din ya kai ta, wata baturiya ce ke tafiya rungume da litattafenta, ya karasa inda take yace "Excuse me Ma'am!" D'an kallonsa tayi tace "Pardon?" Yace "Just a minute or two" Tambayarta ya shiga yi da harshen turanci ko a Dept din nn take, ta masa nodding tace "Yea!" Murmushi yyi yace "Dat's gud Ma'am, am handing my sister over to yhu, assist her for today, yhu know! she's new in here" Baturiyar da baxata wuce shekaru 18 ba tayi murmushi tana kallon Batuul tace "She's welcome, she will really like it in here, from Africa I guess!" Yace "Yea! Exactly Africa! Africa Nigeria." Karasawa gun Batuul dake kallonsu tayi ta kamo hannunta tare da shaking dinta tace "Welcm frnd, yhu will really enjoy it in here, I am Samantha Brown, yhu" Batuul tayi murmushi tace "Am Fateema kashim" k'asa pronouncing din sunan yarinyar tayi Batuul tayi dariya, yarinyar ta bude deep green eyez dinta tace "your looks are more like dat of Britney Smears a pop artiste, just dat yhu are a dark, I will cal yhu Britney! Nyc meeting yhu Britney" kallon Batuul dake dariya bakin rai Abuturrab yyi, sae ta basa dariya don bae taba ganinta cikin farin ciki haka ba, murmushi yyi yana kallon Samantha yace "Dat's a gud start! I will take my leave now Miss Samantha, it's nyc meeting yhu for the first time" hannu tayi masa stretching ya karba tace "Nyc meeting yhu too Mr..." Yana murmushi yace "Aliyu Ahmad" murmushin ita ma tayi tana nodding ta sake hannunsa, karban timetable din hannun Batuul yyi yana dubawa, snn ya mika mata, ya ciro 20 pound sterling hade da wayarsa d'aya ya mika mata yace "Driver xae kira ki anjima" risinawa tayi ta karba kanta a kasa tace "Nagode" bae tanka ta ba, ya ma Samantha waving ya juya ya bar su wajen.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.