Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 124

8

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Tana shiga gida hanyan garden tayi ta wanke fuskanta da kyau dan kar a ce tayi kuka, da sallama ta shigo palon, ba kowa sai Aunty da Aabid a hannunta tana bashi madara, karasawa tayi cikin palon zata hau bene bayan ta cewa Aunty ta dawo taji Aunty tace "Batuul zo nan, mey ya sami idonki ya canja kala, kuka kikayi" da sauri ta ce " a ah Aunty kaina ne yake ciwo tun da naje, nace zan dawo ma Ammah tace in bari sai da yamma a dawo dani, tana gama maganan ta hau stairs da gudu, da ido Aunty ta bita ba wai dan ta yadda da abunda ta fada din ba, tana kaiwa last stair case din taji sallaman mai gadinsu ya shigo da leda wai a bawa Batuul inji mutumin da ya kawota, Aunty ce tace ya ajiye, yana ajiyewa ya tafi abunshi, Batuul kam tsayawa tayi tana kallonshi har saida ya ajiye ya fita tukunna ta tab'e bakinta ta tafi , dan ita ta ma manta gaba daya da batun abunda Ammah ta bata, dakin k'annenta ta bud'e ta lek'a dan a cike take da Ahmad da yaqi picking call dinta kuma bai k'irata ba bare yazo d'aukanta , tana budewa taga dak'in ba kowa, an tattarashi tsaf sai k'anshi da sanyi yake yi kamar ba shine a hargitse ba d'azu, rufewa tayi ranta a b'ace dan taso ta sameshi ya fad'a mata dalilinshi na qin d'aukan wayan, 膹akinta ta k'arasa ta bude, tana shiga ta tarar dashi kamar yadda ta fita ta bari sai d'an gyara da aka sakeyi, kayan jikinta ta cire ta shiga toilet, bath tub ta shiga ta cika shi da ruwan dumi, tana shiga ta dinga kukan da bata san dalilin yinshi ba, sai da tayi mai isanta sannan ta fito daga daga cikin bath tub din ta nufi sink tayi alwala,fitowa tayi daga toilet din, gaban mirror taje ta shafa mai, ta fesa turare masu sanyin k'anshi, da ta gama ta k'arasa gaban closet dinta ta bud'e ta dauko kayan bacci, gown ne na sponge bob iya gwiwa ta saka, ta saka hula blue sannan ta shimfid'a sallaya ta hau ta tada Sallah Isha, tana idarwa ta hau makeken gadonta ta kwanta, remote din AC ta d'auka ta k'ure to the highest volume, duvet dinta ta janyo ta rufe duka jikinta dashi, wayanta taji yana ringing, kamar baza ta d'auka ba ta janyo shi da k'afa ta k'ara a kunnenta , a hankali ta amsa da "Hello" daga d'aya bangaren aka amsa da "sweetheart i was worried about you, inata trying number ki it wasnt going,kun isa gida lafiya", a hankali Batuul tace Farida ina gida, jin muryan Batuul yayi k'asa ya sata tambayanta "Batuul are you okay", a hankali Batuul ta ce " yeah am okay" Ya Ammah, kice mata na gode....", katseta Farida tayi ta ce mata "Yaa Abu ya k'irani wai in fada mishi inda gidanku yake , Baatul tace mata " eh ina ta yi mishi describing ne bai gane ba shine nace ya k'iraki ya tambayeki amma ai tun dazu mukaxo, har ma na kwanta, ce mata ta sakeyi "bari in barki sai da safe tunda har kin kwanta" jikin ta sanyaye ta ajiye wayan dan tasan ba lafiya bestyn ta take ba saboda ko zatayiwa ko shiru bata yiwa Farida, tasan mayb wani abun ya ha膹a ta da Yaa Abu

Tuki yake yana tsaki kwata kwata fitar da yayi niyyan ma fasa ta yayi, wayanshi ne yayi ringing, duba mai kiran yayi sannan ya jona wayan da speaker motan kamin ya d'auka, yana 膹auka yace " said yanxu kika ga daman k'irana kenan" , daga daya bangaren cewa akayi cikin siririyar murya da kanaji kasan an lank'washeta " Bae kaima kasan ba da gangan naqi kiranka ba, kasan muna ta ibada ne kuma muna tare da family so...." bai bari ta k'arashe maganan ba ya katseta da cewa " Yasu Mummy, yaushe ne dawowanku" , "su Mum na lafiya, next week zamudawo ai zakazo d'aukanmu ko, i even have something for you, 膹azu mun fita dasu Mum munje bin Dawood naga wani turare ance shi ne latest of d month,na siyamaka dan har su prince Hamdan ma shi ne nasu for this month, bai bari ta karasa maganan ba ya ce mata " okay yanxu ina driving ne , i will get back to you when i reach home", a sanyaye tace "Aii bae take care" ta katse wayan, kullum sukayi waya sai yayi mata hali, amma babu komai ai Mum dinta tace mata indai ta aureshi komai zaiyi normal, said yadda tayi dashi, shima har yazo ya fita sonshi,ayyanawa tayi a ranta ai tunda tana da kyauzatayi anything possible ya sota fiye da komai, tunanin hakan ne ya sata wani daria mai sauti , y'an dakin hotel din ne suka juyo suna tambayanta mey take yiwa wannan dariyan, murmushi ta sakeyi ta ce musu "Tunanin yadda zanyi da Abutturab nakeyi da yadda zai so ni in munyi aure" ta tab'a matar dake gefenta tace "Yaa zee wlhy ina sonshi, baza ki gane bane, wacce aka k'ira da Yaa zee dince ta ture mata hannu daga jikinta tace "rabu dani dallah, anyi anyi ki rabu da yaron nan kink'i, ni banga ma wani abu da yake dashi ba in banda tsawo da ya 膹ebo kamar isha da girman kai kaman wani basarake, ga manyan mutane nan na sonki amma kin nacewa k'aramin yaro da ya baki y'an shekaru, in banda wulak'antaki babu abinda yakeyi, dubi fa ko yanxu da kika k'irashi ce miki yayi sai yanxu kika ga daman k'iranshi, shi mesa bazai kirakin ba 膹an rainin wayo kawai" taja tsaki ta ci gaba da danna wayarta, yarinyar ta sake cewa "Yaa Zee baza ki gane bane, da kinsan wahalan da nasha kamin ya fara kulani ,ke da kanki zakice inci gaba da hak'uri saboda in inyi fulfilling dream dina in aureshi , kuma ai ina sonshi, tun first day dina a school nake bin shi yana shuning dina har na samu yana kulani yanxu ai bazanyi missing wannan opportunity ba, yanxu kawai jira nake muyi aure komai zaiyi daidai yadda muke so , Yaa Zee tace mata" ke kika sani, Ni ki rabani da labarin wannan sarkin tsawon naki," taci gaba da abinda take, tashi yarinyar tayi ta fita daga 膹akin tana dariya

Aunty ce ta tura Fa'iza ta duba mata ko Batuul idonta biyu, da taje sai da ta lek'a ,hasken da ta ganine ya sata shiga , a hankali tace mata, "Yaa Batuul Aunty tana qiranki, bata tashi ba tacewa Fa'iza "gani nan zuwa" Fa'iza na fita ta tashi tabi bayanta after ta duba fuskanta a mirror taga ya 膹an zama normal , tana sauk'a k'asa taga duka yan gidan a palo kowa ya baje ledoji a gabanshi sai hira sukeyi suna dariya, Baba ne ya fara hangota yayi mata alama da tazo wajenshi, kusa dashi taje ta zauna , Ahmad ne ya kalleta ta doka mata harara, dariya yayi ya 膹auke kanshi yaci gaba da abinda yakeyi, Baba ne yace mata "Da zamuje mu 膹aukeki da muka fita dan Ahmad ya ce min ya bar wayanshi a gida, sai da mukayi waya da Aunty ta ce mana kun dawo , a hankali tace mishi "Ehh Baa, inata kiran shi baya picking shine kawai Ammah tace a dawo dani, tun dazu ma na dawo", tashi tayi ta koma wajen Aunty tace mata "Aunty gani", "kinci abinci ne da kika shiga kika kwanta, kuma da kikace kanki na ciwo wane maganin kikasha", kamar zatayi kuka tacewa Aunty "Naci abinci har na sha panadol, bacci nakeson yi yanxu", da ta tashi tafiya ne Aunty ta nuna mata ledan da mai gadi ya shigo dashi yace nata ne, Faiza tacewa ta hawo mata dashi ta k'arasa sama ta
kwanta, binta kawai Aunty tayi da kallo dan ta san duk bacin ranta baya nunawa amma yau wani abun ya sameta,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.