Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 75 of 124

Batuul ta d'auko flask d'in fresh milk d'in kenan zata fito daga kitchen taga Ajiddeh na sauk'owa hankali tashe, duk gashin nan an baje shi, ae fa nan gabanta ya shiga faduwa ta k'asa karasawa dinning,
a tsorace take kallonta ganin yanayin da take, wani irin mugun kallo tabi Batuul dashi ganin irin kayan dake jikinta, har sai da tazo zata wuce ta dinning d'in a hankali Batuul tace "INA kwana", wani kallo ta watso mata tareda hararanta, tab'e baki Batuul tayi ta d'auke kanta, dama ita kirkin da Ajiddeh ke mata ba yadda tayi dashi ba, gara tana masifan da ta Saba kawae, tana dire flask d'in hannunta ta haura sama abinta da sauri.

Da wani irin kuka ta fad'a jikin Abutturab dake kwance kan sofa da remote hannunshi yana kallon TV, don yi yayi kamar bae san ta sakko falon ba da farko, a rikice ya d'agota ya shiga tambayanta lafiya, tana kuka kamar zata had'iyi rai tace "Mummy", tashi yayi yana kallonta yace "What happened to her", cikin sheshek'a kamar dagaske ta kasa ce mishi komai, a d'an tsawace ya d'ago fuskarta yace "talk to me Ajiddeh, what happened to Mum", a sanyaye tace mishi "Yanzu Yaa Zee ta k'irani, wai Mummy ba lafiya kuma tana son ganina", ajiyar zuciya ya sauk'e ya jawota jikinshi ya rungume yace "shhhhh, its okay , she will be alright, okay?, gobe zamuje gida", da hanzari ta d'ago tana kallonshi tace "baby bazan iya ba, inason inje inganta yau, bazan Iya ba", ta k'arashe maganar da kuka sosai, tashi yayi ya kamata suka haura sama, sai da ya shiga d'akin ya zaunar da ita kan gado yace mata tashi ki shirya kayan da zakiyi amfani dashi, yanzu zamuje muyi booking flight ko na evening ne sai mu bi", rinannun idanuwanta ta d'ago tana tana kallonshi tace "Baby ai kana da aiki, ba komai ba sai kaje ba, you should stay back ka kula da abubuwan da kakeyi, In sha Allah she will b fine", haka tayi ta insisting har sai da ta samu tayi convincing d'inshi ya fasa bin ta, bakwai da arba'in da biyar daidai suka sauk'o shida Ajiddeh tana riqe da trolley d'inta a hannu, Batuul na palo suka sauk'o tare, mik'ewa tayi tsaye har suka k'araso inda take, Ajiddeh sai hararta takeyi ta gefen ido, sai lokacin ma ya tuna da ita, kud'i ya ciro daga aljihunshi ya mik'a mata sannan yace "David ya kaiki school", da haka suka fita suka barta nan tsaye ko wayanma bai samu ya bata ba yau. Haka kawae taji ranta ya baci ta bi bayan Ajiddeh da harara, suna fita ta ja tsaki ta haura sama don xuwa dauko jakarta ta bar gidan ita ma.[8/30, 7:35 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

60

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

A bakin mota ta tarar da David tsaye yana jiranta, hannu tasa ta bud'e motan ta fad'a sannan shima ya shiga, sau biyu David na maimaita gaisuwarshi, sai a na ukun ta amsa mishi, zuciyanta ne taji yana mata xafi ta rasa dalili, ta ja tsaki yafi sau biyar zamanta cikin motan, hawaye ne mai d'umi ya shiga sirarowa daga idonta, hannu tasa ta shafo hawayen ta tsaya tana kallo da mamaki, kifa kanta tayi tsakanin cinyoyinta ta fara kukan da batasan dalilinshi ba, daga sama taji David na fad'in "We ve arrived", a hankali ta d'ago kanta ta k'arewa wajen kallo, batace mishi komai ba ta d'auki jakanta ta fita daga motan, department d'insu ta nufa taga Su Samantha da Aisha da wasu students d'in na tsaye hall way d'in, agogonta ta duba taga saura 15mins su fara lecture, tana juyawa zata bar wajen suka had'a ido da Aisha, d'auke kai Batuul tayi kamar bata ganta ba, can bayan faculty d'insu ta nufa ta zauna taci gaba da kukanta, k'anshin turare mai dad'i ne ya bugi hancinta amma bata d'ago taga daga ina k'anshin yake ba, cikin wani irin masculine voice mai dad'i da nutsuwa taji ance "Here, take this", ta d'ago rinannun idanuwanta ta sauk'e kanshi, da sauri ta d'auke idonta ta juyar da kai gefe ta hade rae, har lokacin bai bar wajen da yake tsayen ba, juyowa ta kuma yi ta ga har lokacin hannunshi na mik'a mata farin handkerchief d'inshi, a sanyaye tasa hannu ta karb'a, wani k'anshi mai dad'i ne ya bugi hancinta da takai fuskanta, ido ta lumshe ta shiga goge hawayen dake fuskanta, daga d'an nesa da ita ya zauna, bai ce mata komai ba har sai da ta juyo ta dubeshi sannan yayi mata murmushin shi mai kyau, kau da kai tayi ta fara wasa da biron da ta ciro cikin Jakarta, a hankali ya fara magana "if you don't mind, may I know d reason behind those tears, I might help", sai lokacin ta sake tunowa da yadda taga Abu ya riqe Ajiddeh, wani siririn tsaki ne yayi escaping lips d'inta ta fara k'ok'arin maida hawayen dake shirin dawowa, jin tayi shiru batace komai ba yasa ya sake kallonta, suna had'a ido ya d'aga mata girarshi d'aya yana jiran jin mey zatace, agogon hannunta ta duba taga lokacin lecture yayi, da hanzari ta mik'e ba tareda ta bari sun had'a ido ba ta miqa mishi handki d'inshi, ganin bai amsa ba ta ajiye mishi tace "Thank you, I need to go right away", bata jira jin cewarshi ba ta tafi cikin sauri ta bar wajen", murmushi yayi yabi bayanta da kallo tare da lumshe ido, tana isa taga har an fara shiga class itama taje ta zauna, waje d'aya suka zauna itada Aisha, bayan sun zauna ne Aisha tace "Fatima wai meye problem d'inki, ko yau you look pale, in bakida lafiya dolene sai kinzo school", had'e rai Batuul tayi tace "wa yace miki banida lafiya", dan bata jin yin magana da kowa, murmushi Aisha tayi tace "ai ba sai an fad'i ba, you look sick, red eyes, plump lips, pale face, nasan inda zan tab'a temperature d'inki nasan yayi sama", yak'e Batuul tayi tace "Am totally fine, bacci ne kawai ban samu nayi ba jiya", ta d'auke kanta tana sauraron maganan da lecturer d'insu ya fara, baki Aisha ta tab'e bawai dan ta yadda da abinda Batuul ta fad'a mata ba itama tayi concentrating da jin lecturer d'insu, Batuul dai na zaune ajin ne amma gaba d'aya mind d'inta is off, batasan ma dalilin da yake sata damuwa ba, har suka gama lecture l batayi grabbing komai ba, jiki a sanyaye ta mik'e suka fito daga lecture hall d'in, Samantha ce tace "Let's go and get some food, am hungry just as the glutton I'm, then we go home after then, no any other class, done for d day",ta fad'a tareda d'an tsalle, dariya sauran suka sa amma Batuul was absent minded bata ma san mey suke cewa ba, sai da Samantha ta sa hannu fuskanta ta fara waving sannan tace "Hello, you there", sannan ta dawo daga tunanin da take tace musu, "You carry on, I will b there right away, I need to clear somethings over here", Aisha dai batace komai ba tayi gaba abinta haka ma Samantha tare suka tafi, suna tafiya itama ta juya ba tare da tasan inda zata ba, wani guri ta hango duk bishiyoyi ne, wajen very serene, ba tareda wani tunani ba taje ta zauna abinta ta fiddo littafi kamar me shirin karatu sae dae ita kanta tasan ba karatun xata yi ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.