Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 48 of 124

11 o'clock bayan doctor ya dubata yayi discharging 膹insu akan zai na zuwa har gida yayi mata alluranta da suka rage sannan yace a guji duk wani abu da zai rik'a b'ata mata rai kuma kar a rik'a fa膹a mata maganan da bata expecting har ya rik'a shocking 膹inta tana zama unconscious, Baba ne yayi magana yace zasu kiyaye, da haka suka yiwa doctor sallama, suna komawa gida tace ita baza taje 膹akinta ba a 膹akin Aunty zata zauna, wanka tayi bayan ta shiga 膹akin sannan ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai k'arfe biyu, tayi alwala ta tada Sallah, tana idarwa Aunty ta shigo rik'e da tray a hannunta, ajiyewa tayi ta zubawa Batuul abinci sannan tace mata ta sauk'o taci, da kyar taci ka膹an tace ta koshi,

Da yamma wajen k'arfe biyar tana zaune tana kallon E.tv Aunty na ha膹a kayan Aabid Baba ya shigo 膹akin, kan gadon da Batuul ke zaune ya zauna, tashi tayi zata sauk'a ta gaisheshi yace mata "Yaanyi" (Mamata), 膹agowa tayi ta kalleshi da idonta da ya fara kawo ruwa, hannu yasa ya goge mata hawayen ya matso da ita jikinshi ya fara mata magana kamar haka "Ya jikin ki Batuul", jiki a sanyaye ta amsa mishi da "Alhamdulillah Baa, yayi sauk'i, na warke yanxu", yace "Masha Allah, har yanzu kinason zuwa Uk kiyi karatun?, ya tambayeta yana kallonta, 膹agowa tayi ta dubeshi dan ta tabbatar da abinda taji yana fa膹a mata, ganin dagaske yake da sauri ta shiga gya膹a kai ta da膹a rungume shi, tasan dama babu wani aure da za ayi mata kawai Yayyace ta fa膹a, ce mishi tayi "ehh Baa inaso" murmushi 膹auke fuskanta, murmushin yayi shima yana shafa kanta yace "toh zan samo miki admission sai kije kiyi karatunki kinji ko, ai zakiyi karatu sosai ko?", kanta ta gya膹a har lkcn murmushi shimfi膹e fuskanta har yafi nada, cewa tayi "Baba toh yaushe ne za ayi, ko sai na gama semester 膹innan sai inyi transfer", ta tambayeshi tana jiran jin mey zaice, Aunty dake aikinta tana jinsu ta saki dariyan takaici dan tasan so kawai Baba yake ya shawo kan Batuul dan yasan tana son karatu sosai, zata iya hak'ura da komai dan tayi achieving dream 膹inta, Babane yace "very soon Mamata, amma kinsan mey nakeso dake", kai ta girgiza mishi yace "yawwa, kinga dama bana son zaman hostel, ko", nanma kai ta gya膹a, yace "toh kinga sai kiyi zamanki tareda Yayanki, nasan sosai zai kula dake", kanta ne ya膹aure ta fara tunanin wane Yayan kuma, ce mata yayi "nasan tunanin wane yayen kike, Abutturab nake nufi", wara ido tayi ta kalli Baba tana girgiza kai tace "Baa toh zan zauna inyi a gida na fasa wllh, bana son zuwa," hawaye cike idonta ta kare maganar "k'ara janyo ta yayi jikinshi ya goge mata hawayen dake zuba a idonta yace "ki kwantar da hankalinki kinji Batuul, nasan anytime you will be proud of whatever decision i made, nasan Aliyu tun yana k'arami, nasan abunda zai iya da wanda bazai iya ba, ki kwantar da hankalinki kinji, kuma auren da Yayya ta fa膹a miki gaskiya ne", sosai ta shiga kuka harda sheshshek'a" muryarta na rawa tace "Baba nifa yarinya ce, just last month na cika 18, kayi hak'uri in na girma sai kayi min ko da waye ma kaji Baa", dariya maganan nata ya bashi yace "Batuul akwai Babba ne da k'arami a bautar ubangiji, babu, toh kinga ina laifin tun kina k'arama ki fara bautawa ubangijinki, kinga ladanki nema zai k'aru, ga kuma ladan da zaki samu na yi mana biyayya, ko ba kya so", ya tambayeta yana kallon fuskanta dake ta ambaliyan hawaye, kasa cewa komai tayi, ci gaba yayi da mata magana yace "toh mamata y dont you start it early and be rewarded abundantly, tunda at any point zakiyishi its better you do it now, and am assuring you Abu will b d best husband we will ever recommend for you, Nida Babanshi have been good friends for over 30yrs, har gida yazo ya sameni ya nemawa Aliyu aurenki, duk mutumin da yaso jininka har yaso ha膹a zuriya dakai yafi k'arfin wulak'anci, kinga ba da膹i ince musu a'a, sosai yake ganina da mutunci, friendship 膹inmu da muka gina based on trust yafi k'arfin ya nemi abu a wajena in hanashi", jikinta ne yayi sanyi sosai, 膹agota yayi yana kallon fuskanta yace "Ko in koma ince musu kince bakya so", a hankali ta girgiza kanta alamar a'a, yace "yawwa Mamana Allah ya miki albarka, yanxu ki share hawayenki ki rok'i Allah ya tabbatar miki da duk alherin dake cikin bikin nan", haka ya dinga bata baki yana kwantar mata da hankali har yasa Batuul ta hak'ura, sai da aka k'ira magrib tukunna ya fita daga 膹akin ya tafi yin Sallah.

Washegari misalin goma na safe Abuturrab na kwance falo kan 3sitter abun duniya ya taru yyi masa yawa ganin ynda Ammah ta dage sae Shirye shiryen aurensa take ba ji ba gani, Ammah ce ta shigo falon ya mike xaune ganinta, da fada ta fara magana tace "anya kuwa Abuturrab kana son gamawa da mu lfya, tun jiya ina bin ka ka je gida ka duba yarinya an sallamesu ka ki xuwa?" Sakkowa k'asa yyi da sauri yace "Don Allah kiyi hkuri Ammah, ynxu nake son shiryawa in tafi wllh" bae jira cewarta ba ya mike ya nufi stairs, cikin mintunan da basu wuce goma ba ya sakko sanye da kananun kaya yana rike da makullin mota, cikin falon ya karasa yana kallon Ammah yace "Xan tafi Ammah" ta d'an sake fuska tace "Toh Allah ya tsare, kuma saura ka je masu empty handed, don nasan ba kai ya isheka ba" murmushin karfin hali yyi ya fita daga falon, parkin space ya nufa ya dauki motar da xae dauka ya bar gidan rae ba ddi. A waje ya bar motarsa ya fito ya shiga gidan, har xae danna bell ya fasa ya murda kofar a hnkli ya ji sa a bude, turawa yyi ya shiga falon da sallama, bbu kowa falon sae kamshi me ddi dake tashi da sanyin Ac, da alama duk yaran gidan sun tafi makaranta, ya karasa cikin falon ya xauna kan kujera, motsin da yake ji a kitchen ya sa shi sanin da mutum, ba a dau lkci ba ta fito rike da bowl din fruit salad da alamar lkcn ta hada ganin ynda taje jujjuya shi, sanye take da d'an mini skirt da top, ta bar gashinta in a messy bun s, cak ta tsaya tana kallonsa gabanta yyi mugun faduwa, shima kallonta yake daga sama xuwa k'asa, mikewa ta ga yyi, bata tsaya wani tunani ba ta nufi sama da gudu, yyi kwafa ya koma ya xauna, ya kusa awa daya xaune falon masu aikin gidan sae kai komansu sake bae ce su kira masa kowa ba, Anty ce ta sakko don shiga kitchen ta daura girkin rana da masu aiki ganin sha biyu ya kusa, da mamaki take kallonsa tace "A'a Abuturrab, yaushe ka xo" ya sunkuyar da kai yace "Ban jima ba Anty, ina yini" tace "Lfya lau, maimakon ka aika su fa'ixa su kira mu" murmushi kawae yyi bae ce komae ba, Anty ta nufi kitchen fa'ixa na biye da ita a baya, sae da suka shiga kitchen din snn tace "Tafi ki kira Batuul" juyawa tayi ta fita daga kitchen din. Batuul na kwance dakin Anty sae dae ban da faduwa bbu abinda xuciyarta ke yi, da ta tuna maganganun baba sae ta ji hawaye ya sakko mata, ynxu shknn hka tana ji tana gani xa a aura mata Ya Abuu, fa'ixa ce tayi knocking, ta share hawayen fuskarta tayi mata ixinin shigowa, fa'ixa ta ba ta sakon Anty snn ta fita, mikewa xaune tayi jiki a sanyaye.
[8/22, 2:07 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.