Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 117 of 124
Cikin gida ta koma kai tsaye ta wuce kitchen tana kokarin mance duk abinda ta gama ji yamzun, Freezer ta bud'e ta ciro wani babban rubber assorted ne soye ciki duk sunyi block, plate ta d'auka ta d'ibi kad'an ta saka ciki snn ta saka a micro wave zatayi warming, kan freezer ta koma ta zauna bayan ta ciro ta d'auki fork tana cin kayan cikin, ta Bawa dake wanke fruits tace "Yaa Batuul naga baki nemi yaji ba kuma akwai su iri iri", Batuul ta d'an yatsina fuska tace "Aunty ta Bawa kinsan a can bamuyi wani aikin nama ba, masallaci kawai mukaje muka dawo, ya dai yi mana yanka", Ta bawa ta riqe baki tace "kai haba, toh ina aka kai ragunan?", Batuul ta tab'e baki tace "Ehhhm, Sadaka akeyi dashi kasashen mabuk'ata", "Ahhh lallai an gaisheku, ai koda za ayi sadaka ba duka ba, nan gaba kice a bar miki naki ko nan kya turo na gyara miki in aikace shi, wa yace duka ake sadakar?", Batuul tayi dariya tace "Toh shikenan", ta dubi Janet dake ta faman goge plates d'in da ta wanke tace "Janet miqo min yajin na tafarnuwa, da sauri ta kawo mata shi ta koma bakin aikinta, tana zaune tana ci Aunty ta dawo kitchen d'in taga Batuul zaune kan freezer tana take
kayan ciki tace "har ya tafi?", kai ta gyad'a tareda amsawa bayan ta cinye wanda yake bakinta, Aunty tace "in kin gama ki sameni sama", Aunty bata gama bama ta sauk'o kan freezer tana ajiye plate d'in ta biyo bayan Aunty, sosai sukayi having mother daughter time d'insu, ta bata addu'o'i da shawarwari masu kyau, tace ta shiga tayi wanka bayan ta had'a mata ruwan da sinadarai masu yawa, bayan ta fito ta taga wata da ganinta y'ar Tchad ce zaune, gyaran jiki Aunty tasa matar nan tayiwa Batuul tayi mata, cikin lokaci kad'an Batuul ta canja sai shek'i takeyi, saida aka gama suka sauk'o dining cin abinci, sai lokacin taga Baba da y'an k'annenta, da murna shima ta rungumeshi, koda zata fara mishi shagwab'a wayo yayi mata yace ai ta girma yanzu sai dai su Yusra suyi, haka suka zauna cin abinci murna fal ranta, har wani emotionally ta rik'a ji a ranta, bayan sun gama cin abinci mai gyaran nan kuma. tayi mata kitso, k'arfe goma daidai ya dawo, tun da ya shigo gidan idonshi ke kanta, babu abinda yake furtawa cikin ranshi sai "Subhanallah, Masha Allah cikin ranshi", har ya k'araso cikin parlour, da murmushinta mai kyau ta juyo ta dubeshi, a nutse suka gaisa da Baba ya sake gaida Aunty, yaran ma dukkansu suka gaisheshi, a nan yake sanar da Baba gobe sha d'aya jirginsu zai tashi, Albarka Baba yayi ta saka musu tareda Nasihohi, Aunty ta cikata da abubuwa dayawa da wasu ma bata san amfaninsu ba, kamar kar ta tafi haka tayi sallama dasu suka wuce, yana barin compound d'in gidan yayi parking gefen titi ya ciro wayarshi yana haskata yace "Glitter kinyi kyau da yawa", murmushi tayi tace "Aunty tasa aka min duka, kaga har kitso anyi min", ta cire d'an kwalinta tareda nuna mishi sabon kitson nata, gaba d'aya motar k'anshinta mai dad'i yakeyi, hannu yakai yana shafa kitson yana lumshe ido a hankali ya dunga furta wasu addu'o'i da shikad'i yakeji snn ya bud'e idon yace "Glitter plss ki tayani addu'a ki haifa min Baby girl mai kama dake", tayi dariya tace "nikam baby boy nakeso, kaga I want to name him after this fav name" hararanta yayi yace "wane sunane favorite d'in naki?", batareda tunanin komai ba tace "I have loved the name tun ina yarinya, I wanted marrying someone with such a name ko kuma in haifi mai sunan, I just have a thing for the name ALIYU", ta fad'a kanta tsaye, ajiyar zuciya ya sauk'e jin sunan da ta ambata, sai da ta ambata ta tuna mey ya fito daga bakinta, ta tun. a shima fa sunanshi kenan, ido ta rintse tana dariya, hannu yasa yana cupping fuskarta yace "Every Aliyu have his own Fatima, it happened you are mine, I can't imagine life without you now, I love you", itama tayi murmushi tace "I love you too", da haka yaja mota sukayi gida, koda suka isa har Ammah tasa an gama shirya musu kaya, d'an hira suka tab'a snn sukayi sama suka kwanta, washe gari tunda suka tashi da asuba basu koma sun kwanta ba har suka gama shirin tafiya, 9 Sadiq ya fita dasu airport, Batuul dai sai kallon ikon Allah takeyi jin babu mai zancen Ajiddeh, Sadiq na dropping d'insu bai jima ba ya juyo, duk motsin da zatayi idonshi yana kanta, candy floss ta hango wani d'an yaro naci, a hankali ta juyo ta dubeshi tace "Yaa Abu inaso", ya kalleta yaga inda take kallo yace "we should go nd get", tayi raurau da fuska tace "Nifa na gaji, ka samomin kai zan jiraka a nan, in na tashi zan gaji dayawa", yayi murmushi tareda lakuce mata hanci yace "okay take care, bara inje duty free nan in duba", har ya juya yaji tace "da spicy French fries plss", murmushi yayi mata kawai ya tafi, baifi five minutes da tafiya ba ya dawo, baisan lokacin da murmushi ya k'wace mishi ba ganinta zaune k'ark'ashin wasu manan rose Petals a wani perfume stall, sosai tayi kyau sbd kayan dake jikinta suma pink ne, abubuwan dake hannunshi ya ajiye ya ciro wayarshi daga aljihu yayi snapping d'inta pictures batareda ta lura ba, har ya isa wajenta yana murmushi, gabanta ya tsuguna tareda mik'a mata floss d'in, da wide smile ta karb'a tayi mishi mouthing "Thank you", kai ya girgiza mata yana nuna mata cheeks d'inshi, wara ido tayi tana blushing tana girgiza mishi kai, baza ta iya ba, kunyan shi duk ya gama cikata, ganin taqi yi ya zumb'uro mishi bakinshi ya miqe zai bar wajen, hannu tasa ta riqoshi, saida yayi murmushi snn ya juyo yana kallonta, a hankali tace "da mutane anan, in munje gida pls", hannunshi zai sake karb'a tace "toh close your eyes", lumshe ido yayi a hankali ta dawo gabanshi, d'age tayi sbd tsawonshi, ji tayi ya d'aura hannu waist d'inta ya d'agata sama, pecking kumatunshi duka biyu snn ta maida kanta ta sinnewa jikinshi, tafi taji duka wajen ya d'auka, tsabar kunya kasa d'agowa tayi, tana jikinshi ya mayar dasu wajensu sukayi zamansu, 11 daidai sukayi boarding jirgi, in banda bacci babu abinda takeyi, lokaci lokaci take tashi, murmushi kawai zai mata ko kuma ya tambayeta in tana da buk'atar wani abin, har suka isa UK
[18:48, 12/22/2017] 鈥�+234 806 969 9042鈥�: 馃挅馃æŒÂBATUUL馃挅馃æŒÂ
96
By Phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Hawayen da kanshi nema take ya zubo ko zataji dad'i ta rasashi, ido ta k'urawa Mummy dake kwance duk jikinta anyi bandaging gwanin tausayi, tunda taga yaqi d'aga k'iranta tasan babu yadda za ayi yazo, tunanin Abutturab yasa ta jin silalowar hawayen da take ta neman zubowarsu ko zata samu y'ar nutsuwa, amma Sam abun ba haka yake ba, saima rad'ad'i da ya k'arama zuciyarta, tun da Dad ya fita bai sake shigowa ba har yau, a hankali taga Mum na k'ok'arin bud'e ido, da kyar ta bud'esu tana k'arewa d'akin kallo, kan Jainaba dake kwance ta d'aya b'arin idonta ya fad'a, hawayene kawai ya dinga silalo mata, a hankali ta maida dubanta ga Ajiddeh dake zaune, rintse ido Ajiddeh tayi ta bud'e snn tace "Mum wani irin fitina ne wannan nake gani a rayuwa?, duk wata masifa ta rayuwa na gama ganinta, Mum kece silar duk wani tashin hankali da nake ciki yanxu, tun ina k'arama tun Dad baiyi arzik'i ba, tun kamin inyi hankali na fahimci duk abinda kike so sai kin sameshi ko da ya kaucewa shari'a, tun bamuda arziki kike cewa mucewa k'awayenmu mufa y'ay'an wane da wanene, tun ban fahimta ba har na gano ma'anar inda kika dosa muka fara biye miki, babu yanda Dad bai nuna k'ok'arisnhi kanmu ba dan mu gyara amma kan ya faskara saboda kullum tare dake muke, zamanmu dake yafi yawa dole mu d'au ak'idarki, Mum kece uwa ta farko da na fara ganin bata tab'a yiwa y'ay'anta fad'a kan abinda babu kyau ba, baki tab'a tsawatar mana akan laifinmu ba, Dad ne kad'ai ke mana fad'a, ana haka Dad yazo ya samu arziki, d'an time d'inshi da muke samu yazo ya zama bama samu, duk wani jin dad'in rayuwa mun samu saboda irin son da yakeyi mana, amma ko shi Dad naga ba time d'inshi kikeda ba sai abinda yake dashi, kin koya mana son abin duniya da muka d'auka muka girma da, nima nasa a raina zanso mutum amma saboda kud'inshi", tayi shiru tana shesheka ta kalli Mummy da ta rintse ido tana kuka, taci gaba, "Allah mai yi yadda yaso da bayinshi ya had'ani da Aliyu da kallo na d'aya naji duk duniyar nan babu wanda nakeso kamar shi, babu possible ways d'in da ban bi dan yasoni amma ko zamana baisan da ba, a haka na tareki da zancen, tashin farko Mum cewa kikayi zamuyi maganinshi, haka mukayi ta bin bokaye, duk basuyi tasiri akanshi ba har saida na samu nayi plan d'in da ya bigeni da mota, ni nasan Aliyu bai tab'a sona ba, amma saboda son da nake mishi yasa bazan iya barinshi ba, ya aureni bawai dan yana so ba, nasan ya rasa abin yine saboda matsa mishi da akayi a gida, na samu fatana ya cika, my dream came true na zama matar Aliyu amma son zuciya da tsoron rasashi suka rinjayeni, babu abinda na tashi saka mishi da sai rabashi da nayi da iyayenshi da danginshi har tsawon shekara, Allah da yake shi ba azzalumin bawanshi bane ya saka mishi, iyayenshi sanin da sukayi ba haka kawai zaiyi haka ba, ba zasu zauna suna gani d'ansu ya halaka ba suka nema mishi aure", dariyan takaici ta saki tana girgiza kai taci gaba tace "Dole ma Allah ma yayi mishi sakayya ta alheri, mey na tab'a yi mishi na zamantakewar aure?, ko tsinke ban tab'a dagawa gidana ba bare inje ga zancen girki, a haka ya dawomin da yarinyar gida, tun had'uwata ta farko hankalina bai kwanta da ita ba, dukda kullum ina admiring duk wani abu nata, nutsuwa, kunya, k'awaici amma hakan baisani ganin gaskiya ba sabida son zuciya, Baiwar Allah jikina dama yana bani da wani abu a tattare da ita mai girma, amma son zuciyata yasa na cutar da ita, da na tab'a sanin akwai ranan da zan bud'i ido inji Aliyu na korata kan yarinyar nan da ko kallon banza ban jifarta dashi bare mugun kaba'iri, gashi a dalilin cutarta da nayi yasa yace ko kallona bai sakeyi, am not putting all the blame on you Mum, I have a commision a ciki, in kinyi abu mara ai nima nasan daidai zan iya gyarawa, shiyasa Allah ya bani hankali amma naqi aiki dashi,è½ gashi we are accounting for all our deeds, we are reaping what we sow, Mum ni bansan mey kikaje yi har illorin ba amma nasan ba alheri bane ya kaiki, gashi nan Allah yana nuna mana ishararsa, Na kirashi yazo mu nemi yafiyarsu Mum yaqi d'agawa, ko yafiyarshi ne yazo in roqa", Sai lokacin Mum ta bud'e idonta da suka kad'a da k'yar tace "Hauwa duk wani abu da nayi dan Ku nayishi, babu wanda nakeso da k'auna duk duniyan nan sai ku da Allah ya mallakamin, banida kowa sai y'ar uwata Jainaba, mun taso cikin k'unci nida Jainaba da nayiwa kaina alk'awarin y'ay'ana bazasu fuskanta ba, ba haka naso rayuwa ta juya mana ba, kuyi hakuri Ajiddeh, nafiku jin ciwon duk abin nan da yake faruwa, tafiyan nan da nayi duk dan nema muku farin ciki na fita yinshi, farin cikinku shine nawa, ku yafemin, ta fashe da wani sabon kukan
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.