Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 42 of 124

Batuul na gama shirin makaranta tazo yiwa Aunty sallama zata wuce, bayan ta gaidata ne tace "Aunty yau in na tashi daga school zanje gidansu Farida", dagowa Anty ta da sauri tana kallonta tace, "mey zakije yi a gidan?", da mamaki Batuul ta dubi Aunty dan bata tab'a hanata zuwa ba, asalima ita ke sata zuwa ko bata son zuwa, cewa tayi "wajen Farida zanje, nace mata zanzo jiya banje ba shine zani yau" a takaice Anty tace "No ki bar zuwan , some other time kya je, ki dawo gida in kin gama lectures kawae", jiki a sanyaye Batuul tace "toh Aunty na tafi", "Allah ya dawo dake lafiya", a hka ta fita dakin, tana fita k'iran Abdallah ya shigo wayanta, sai da ya kusa katsewa tukunna ta 膹auka, a hankali tace "Hello", wani k'ayataccen murmushi ya saki yace "Habibty hope ba tada ki nayi ba, naji voice 膹inki so low", ce mishi tayi "No am okay, yanxu ma school zanshiga, tun 膹azu na tashi", yace "okay okay durlyn, i will meet you there cux nayi missing cute face 膹inki", ce mishi tayi "toh, sai kazo", ta shige mota ta wuce school.
[8/22, 2:04 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
32
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Gaba 膹aya ji yayi kanshi yayi mishi nauyi, idonshi ya canja kala ya zama ja har wani gumi ne ya tsatsafo mishi a goshinshi, ya girgiza kai yana ci shiga gaba da ambaton innalillahi wa inna illaihir raji'un, sai da yaji bugun zuciyanshi ya 膹an daidaita tukunna ka kalli Ammah dake hararansa har lkcn ya marairaice murya yace "Ammah ki min rai ki aura min wata daban amma ba Batuul ba, yarinya ce fa karama, kuma kila ma baxa ta rasa saurayin da take so.....," wani irin kallo Ammah ke mishi, hkn yasa ya sunkuyar da kai ya kasa k'arasa maganar, Ammah tace "ko ma dae jaririya ce, ita din muka yi niyyan hada ka da, don nasan xata fi mana babban macen da ka aura, in kuma nuna mana xaka yi ba mu isa ba bismillah, ae dama ka saba daga sanda kayi aure" Runtse ido yyi a hnkli yace "Wane ni Ammah, in'sha Allah yanda ku ka ce hkn xa ayi." jin ya fa膹i haka yasa Ammah sakin fuska ta juya ta kalli Abui tace "dama nasan 膹ana zaimin biyayya, tashi kaje, Allah shi maka albarka, bbu 6ata lkci xa ayi komae don ka koma bakin aikin ka", shafa kanshi tayi tace " Allah maka albarka" da k'yar ya samu ya mik'e daga tsugunen da yake, yayi musu sallama ya fita daga falon, abubuwa ne suka mishi yawa a kanshi, shi ta ina zai fara sanarda Ajiddeh ma aure iyayensa xa su masa, kuma ma matar ba wata bace illa Batuul, yarinyar da bata wuce sha takwas ba tsabar a ja masa raini, me zaiyi da Batuul yarinyar cikinsa? shi if he can clearly remember ma ai Massa ke sonta tun kamin ya bar gari, tunawa da yayi da Massa ne ya sashi saurin ciro wayarshi daga cikin aljihu ya lalubo number shi Massan, dialing biyu ya 膹aga, "dama ana jinka a gari", abunda Massa ya fara fa膹a kenan, share tambayar da Massa ke mishi yayi yace "Kana inane?, inaso mu ha膹u", ya tsaya jin mey Massan zaice mishi, cewa yayi na fita yanxu bana gida but i will b back in an hour", yace "Aii then, zanje gida yanxu before ka dawo zan shiga in gaida Yaa Mera, sai ka dawo 膹in, i need to discuss some issue with you", da haka suka katse wayan, suna gamawa ya mur膹a k'ofan 膹akinshi ya shiga ya 膹auko key 膹in mota ya fito waje, direct hanyan gidansu Massa ya 膹auka, cikin y'an minutes ya isa gidan yayi parking bayan an bu膹e mishi gate ya shiga, Side 膹in Yaa Mera yayi, tayi mamakin ganinshi, dan rabonshi da gidan tun aurenshi da Ajiddeh da yazo yi mata sallama, mamaki shimfi膹e fuskanta tace "Wata sabon gani Babana kaine a gidan nan yau, ashe ka shigo gari", k'arasowa yayi gabanta ya zauna yace " *Yaa Nda dubdo, aaah u' b猫lan amma tusen g猫i*, "ina wuni Yaa, ehhh na shigo amma banma da膹e ba", ya k'arashe maganan da murmushi a fuskanshi, hira sukayi sosai da Yaa har tana ce mishi matarshi dai ba 'a ganinta, har sun manta kamanninta,suna nan zaune Massa ya shigo da sallama, tun daga can ya tsaya k'are ma Abutturab dake gaban Yaa Mera kallo, ba makawa Abu ne sai dai ya 膹an rame, ko meye dalili oho yaci gaba da shigowa abunshi cikin 膹akin, hannu ya mik'awa Abutturab tareda cewa "Man an dena ganinka, rabona dakai fa tunda naje wajenka kamin kazo gida, that is two months after your wedding, i tot baza ka shigo bama sai aure na ai", Yaa Mera ce tace "Abunda na gama fa膹a mishi kenan, nace gashi matar bata haihu ba bare mu muje can suna tunda su sunqi su zo gunmu", sauk'ar da kanshi yayi k'asa dan shima abin nan da yayi na damunshi, gashi nan har yana son zame mishi matsala, Massa ne yasa dariya yace "Kaji ko, ashe su Yaa zaman jiran jikansu suke, sai kayi k'ok'ari ku samo musu kai da Ajiddeh, kaga sai suji da膹in bin naku can garinku mai da膹i da baku son bari", wani kallo ya sakarwa Massa da ya sashi k'ara yin dariya yace "toh ba gaskiya bane", mik'ewa Yaa Mera tayi ta shige daga ciki su kuma suka wuce chamber 膹in Massa, suna shiga 膹akin ya zauna a 膹aya daga cikin kujerun 膹akin tareda mik'e k'afafuwanshi, Massa ya dubeshi yana bu膹e fridge zai 膹auko ruwa yace "wai gajiya kayi ne haka na ganka so slow, ko kuma duk cikin canjawan da kayi ne", wani irin glare ya wurgawa Massa ya tashi daga kwancen da yake ya zauna, k'arasowa Kujeran Massan yayi shima ya zauna tareda mik'awa Abutturab ruwa, karb'a yayi bayan yasha ya rufe ya ajiye bottle 膹in daga gefenshi ya fara msgana kamar haka "Musty, kwanankin baya lokacin biki na kamar naga you showed interest akan yarinyar nan, har yanxu kuna tare ne?", yayi tambayar yana kallonshi, gaba 膹aya kan Massa ya 膹aure dan shi baisan ma wace yarinyar yake tambaya ba, cewa yayi "wacce yarinyar wai, dan ni ban gane wacce kake nufi ba", ce mishi yayi yarinyar nan k'arama mana, yarinyar Aunty", tsaki Massa yaja yace "kaji ka da wani zance, Aunty 膹aya muke da mai k'aramar yarinya, specify inji", shiru yayi ya kasa furta sunan nata, da k'yar ya iya bu膹e bakinshi yace "Batuul", "ohhh dama wai Batuul kake nufi kake ta wannan abin, wait!, dont tell me bakasan zancen aurena ba", da mamaki Abutturab ya dubeshi yace "kayi aurene?", kai ya girgiza yace "No banyi ba but nan da two weeks za ayi", kan Abutturab ne ya 膹aure, yaushe Massa zaiyi aure har bai sani ba, kuma wa zai aura inba Batuul ba, yes ba Batuul bace tunda har su Ammah sukace ya aureta, da sauri ya juya ya dubi Massan da ya zuba mishi ido ganin yadda yake abu kamar ba shi ba yace "Tell me wacece zaka aura inba Batuul ba, kuma ya akayi haka bayan at that time kace min sonta kakeyi", murmushi Massa yayi yace "Toh kai duk mey ya kawo zancen nan, kai da kace mey zanyi da yarinyar tayi k'arama shiyasa na rabu da ita", kai Abutturab ya girgiza yace "c'mon jokes apart, ba wasa nake ba, mesa ka rabu da ita kuma wa zaka aura?", Massa ne yace "Rahama mana zan aura, y'ar Sultan, Batuul tun lokacin ta nuna bata sona shiyasa ma ban kai abun wajensu Ammah ba, but naso in aureta, she will make a good wi.....", wani tsaki Abutturab yaja yace "hold it, okay?", gaba 膹aya ranshi ya b'ace, sai da ya 膹an nutsu tukunna yace "Mustapha am in a problem, kuma babu mai iya fiddani sai kai, kasan auren nan da nayi shekara kenan, kuma su Ammah suna ganin shine ya hanani zuwa inda suke, and ni inason Ajiddeh, like banima da ra'ayin mata biyu, i cant cope, toh 膹azu su Ammah suka tareni da zancen sai na k'ara aure, da nace suyi hak'uri, amma ganin ransu ya b'aci yasa nace na yadda, toh shine da na tambayesu wa suke so in aura, dan ni i have no one in mind shine sukace min wai Batuul", yadda ya k'ira sunan nata kamar ba daga bakinshi sunan ya fito ba yayi maza ya 膹auke idonshi daga kan Massa , dariya Massa yasa harda kyakyatawa ya kwanta akan kujeran, sai da ya gaji dan kanshi ya gama dariyan tukunna ya mik'e ya zauna, Abutturab ko kallonshi baiyi ba har ya gama dariyanshi, sai da yayi shiru tukunna yace mishi "ka maidani 膹an iska ma ko, inyi maka serious magana shine kake dariya", ya k'ara tamke fuska ya tashi zai bar 膹akin, da sauri Massa ya sha gabanshi yace "No baza muyi haka ba, mu koma ka fa膹amin how am i of help dan ni gaba 膹aya zancen ne yazo min a bazata, kaga kuma tunda bazanyi kuka ba ai sai inyi dariya", ya fa膹a yana k'ara smiling, wani siririn tsaki yaja ya koma ya zauna a kujerar da ya tashi, sai da dukkansu biyu suka zauna Massa yace "ina jinka, mey kakeso inyi maka?", shiru yayi ya kasa magana dan baisan ya Massa zai 膹auki zancen ba barema da yace aurenshi nan da sati biyu, iska ya furzar daga bakinshi sannan yace "Inaso kaje kacewa su Ammah kai ke son Batuul, zaka aureta", a razane ya juyo jin abinda Abun ya fa膹i yace "Are you really okay, duk yadda akayi Ajiddeh har brain 膹inka ta tab'a, toh in naje nace musu inasonta sai inyi yaya da ita bayan inada mata", kai ya girgiza yace mishi "ai dama kana sonta, kuma kasha fa膹amin kai baza ka zauna da mata 膹aya ba, and as crowned prince kaga zaka k'ara wata, kaga tunda sooner or later zakayi, y not do it now", kai ya girgiza yace "No way, thats not happening with me, bazanje inyi abunda ban shirya yinshi ba besides ai Batuul 膹in na fa膹a maka da kanta tace min bata sona, kaga there is no way zan auri yarinyar da bata sona", kai shima 膹in ya girgiza yace "Musty you are not understanding the whole thing, am telling you......", katseshi Massa yayi yace "hold on, kai mesa baza ka auri Batuul 膹in ba, she is perfect, beautiful, simple, religious, mey kuma zaka nema bayan wannan, like menene aibun Batuul, ni wlhy da zata soni zan aureta but ta riga da tace min bata sona, so i will b living with that intuition a cikin kaina shiyasa bazan nemeta ba, kuma tunda har su Ammah ne suka nema maka auren nan i bet its for everyones welfare, they have seen the best in her, kuma ni nasan they have a genuine reason for all this, Batuul is your sister, you can tell others who she is, kafi kowa sanin asalinta", kanshi ya sauk'e k'asa ya rasa ya za ayi ya fahimtar da Massa akan bazai iya auren yarinyar nan ba, yafi minti 膹aya kanshi na dafe kan hannunshi tukunna ya 膹ago a fusace har idonshi ya canja launi yace "Na fa膹a maka bazan iya aurenta ba", sai kuma ya sassauta murya jin ihun da yayi yace "Mustapha i cant marry her, like i cant withstand her for a day, bare kuma har aure da yake for eternity, i just cant, i dont know but there is this effect she have on me anytime nake tareda ita and am never comfortable with what i feel", ya k'arashe maganan yana mai sauk'e idonshi daga kallon Massa, Ajiyar zuciya Massa yayi ya dafa Kafa膹an Abu yace "okay calm down, kasan mey za ayi yanzu, ka kwantar da hankalinka, addu'a kawai zakayi akan lamarin nan, zamuyi magana daga baya, kuma kada ka nunawa su Ammah baka so dan ransu zai b'aci", shima Abun ajiyar zuciya yayi yayi patting hannun Massa dake kafa膹anshi yace "In sha Allah zanyi", da haka suka canja zancen suka shiga na wajen aiki da bayan rabuwa, duk da Abuturrab Sam hankalinsa bae jikinsa.
Bayan Batuul ta dawo daga makaranta gida ta dawo kamar yadda Aunty ta ce mata, da sallama ta shigo taga babu kowa a palo, kitchen ta shiga taga Aunty dasu Esther na aiki, k'arasawa tayi ta gaida Aunty tayiwa sauran sannu da aiki duk suma suka mata sannu da dawowa, jikinta ne yayi sanyi ganin yanayin da Aunty ta amsa mata gaisuwan, hawaye ne ya fara taruwa a idonta don ita a tunaninta tun maganan 膹azu da safen nan ya ke b'atawa Aunty rai, maza tayi ta fita daga kitchen 膹in dan tasan kuka zata fara gashi akwai masu aikinsu a gun, anjima zataje har 膹aki ta sake bata hak'uri akan maganan duk da dai batasan mey ya fara kawo zancen aure ba, sama ta haura bayan ta fito daga kitchen 膹in, hanyan 膹akin k'annenta tabi, bu膹e k'ofan tayi ta shiga , ta ga dukkansu shirin Islamiyya sukeyi, wasu na saka uniform wasu sun gama, shiga tayi ta samu waje ta zauna daga 膹aya daga cikin gadajen 膹akin, ita da kanta batasan mey ya shigo da ita ba, Khalil yace "Yaa Batuul wannan takwarar taki tazo", ya fa膹a yana b'ata rai, Mus'ab ne yayi maza ya karb'e maganan tareda zumb'uro baki yace, "mtsew ni Allah kullum bana son zuwanta", hararanshi Batuul tayi tace "bana son rashin hankali, Mamar Baba cefa kake cewa bakason zuwanta, ita da gidan 膹anta", Ahmad dake fesa turarene yace "ehh mana ai gaskiya suka fa膹a, abu duk randa tazo sai tasa ran Aunty ya b'aci, ni bana ganin amfanin zuwan nata, gara mu mu rik'a zuwa wajen nata mu ka膹ai,ni da tace bata son Abuja ma da膹i naji, kuma fa kamar sunanki naji tana k'ira tana ta fa膹a, ai Aunty ce tace mu hau sama shiyasa banji mey suka fa膹a ba", tsawa Batuul tayi musu tace "bafa na son iskanci, waye yace muku ita take b'atawa Aunty rai, wato dukkanku gulma kuke koya ko", Sa'eed da dama tun can shi bamai magana bane yace musu "ku shirya mu tafi dan Allah, its getting late", ya 膹auki wayanshi kan mirror 膹insu ya saka a aljihu ya fita, Su Yusra ne suka shigo 膹akin su sun gama shiryawa sukace Yaa Ahmad mun gama shiryawa fa, inji Aunty mu k'ira ka mu tafi kar muyi latti, dukkansu fita sukayi daga 膹akin bayan sun gama shiryawa sukayi mata sai sun dawo, jiki a sanyaye tace "okay sai kun dawo, kuyi karatu sosai kunji ko, in kun dawo zan baku chocolate", ta fa膹awa su Mahir da 膹an dariyan yakenta, suna fita ta tashi itama tabi bayansu tayi hanyan 膹akin da tasan zata tarar da kakarta da k'annenta ke cewa tazo, tasan duk gaskiya suke fa膹i, duk yadda akayi ma itace tasa ran Aunty b'aci, batasan meyesa bata sonta ba, tunda tasanta, tasan kakarta bata tab'a son Aunty ba duk da kyautatawan da Aunty keyi mata dan Aunty tasha yiwa Yayya abun kirki tun suna Maiduguri harda suka dawo Abuja ma kuma ba tareda sanin Baba ba, amma bata tab'a appreciating ba, zuwanta bakin k'ofar 膹akin ne yasa ta kawar da tunanin da take ta mur膹a k'ofan 膹akin. 馃挐BATUUL馃挅馃挐
33
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Da sallama ta shiga 膹akin taga bata nan amma akwatinta da jakanta na daga gefe, sai glasses 膹inta dake ajiye kan mirror, zama tayi tana jiranta dan da alama toilet ta shiga, tana nan zaune ta fito tana goge ruwa a hannnunta da 膹an k'aramin napkin, da gudu Batuul ta tashi taje ta rungumeta tana fa膹in, " *Yayya nyi kammo isi min gull猫ma, biya ngaima amme nya sorin*, Yayya ke kullum baki cewa zaki zo sai dai kawai a ganki kin fa膹o", Sai da janyeta daga jikinta tukunna tace " *dai fandoro let猫 chingya nyairo gullukin, k猫rma d猫 fato tadanyi yero kadiko, fanuwa na*?, ku bari ranan da na tashi zuwa gidajenku sai in sanar daku amma yanxu gidan 膹ana nazo, babu izinin wanda zan jira kuna jina", dariya Batuul tasa tace "duk mey yayi zafi haka Yayya, namun ma in kin tashi zaki iya zuwa kai tsaye ba sai ki nemi izinin kowa ba", ta karashe maganan tana kallon Yayya da ta k'ura mata ido tana ta kallon ta, kai ta 膹aga tareda da 膹age girarta 膹aya tace " *Yaaa k猫rma d猫 ai yo do, wa shimmin rumin d猫 nyimai nya n猫m shawan kong猫na ro nonema*, Yanxu kuma menene kika zubamin ido kina kallona haka, kinsan ai ko a yarintarki baki kaini kyau ba, sai ma dai rashin tsayi da kikasa na biyoki da" tsaki taja tace " *ndu nyiro nyiro nyi shawas猫 gullono, u awo wallimin d猫 dai rukkin, rui futu ngam n猫ma d猫, biya dai montindo jarawai ad猫 na kwalluwa*, waye yace miki kina da kyan da har zan tsaya kallo, ja'ira ni wannan rama da kuma bak'in da kikeyi nake gani, wannan jaraba ta makaranta da bata k'arewa, gashi duk ya lalataki", rai Batuul ta ha膹e tace "kin fara ko, ni kinga ma 膹akina zan koma", sanin da Batuul tayi sarai akan maganar da zasu shiga nan ne ya sata cewa zata bar mata wajen, cikin 膹aga murya tace " *len猫miya wande waltim yisimi, fuskam yaame yedai a, aima ba k猫nza g猫i ya, nyai sammaso bannaz猫na, afuno g猫i awo gade mananuwin a ba, kamme nyairo kanuri manaja shiro afunon mananuwin, Baan do d猫 g猫renge yishin ai, shima nyairo s猫k猫lima fayin ai*, in kin tafi karki dawo, da fuskanki kamar na uwarki, babu komai sai hanci da gashi da kika kwaso, duk ta fama b'ataku, inba Hausa ba babu abunda kuka iya, ana yi muku kanuri kuna maidawa mutumin magana da Hausa, ai ina nan ina jiran dawowan Baban naku, in shi ya koya muku duk zanji", ta gama fa膹a harda kalmashe k'afa, dariya abun ya bawa Batuul ta girgiza kai ta fita, D'akinta ta koma taje tayi wanka ta saka gown mara nauyi ta fito kitchen taya su Aunty aiki, k'arfe biyar da rabi suka gama aikin da zasuyi suka jera a dinning, K'arfe shida su Ahmad suka dawo daga Islamiyya, lokacin Baba ma ya dawo a tare suka shigo, sai da kowa yayi sallah tukunna suka sauk'o cin abinci, Aunty ce tacewa Batuul taje ta sauk'o da Yayya suyi dinner, ba b'ata lokaci ta haura sama suka sauk'o a tare, cup 膹in ruwan da Baba ya 膹auka zaisha ya maida ganin Yayya na sauk'owa daga bene, da mamakin ganinta ya mik'e ya isa inda take ya rik'o hannunta suka iso dinning 膹in, sai da ta zauna tukunna ya fara gaidata, yace "Yaa baki cemin kina zuwa ba, kuma ko jiya saida mukayi waya dake fa", yaran ta duba sannan tace "toh garin naku wani nisane dashi, ko sae na nemi ixinin ka kafin in xo gidan ka," da sauri yace "A'a wllh ba hka ba yayya nayi mamaki ne kawae" ta dan kyabe baki tace 'a jiyan bayan mun gama magana da ka sanar dani abinda ke faruwa naga gara kawai inzo ayi ta ta kare, nasa Hamza yayi min booking jirgi na taho yau kawae", duk abin nan Aunty bata 膹ago ta kallesu ba sai da taji Yayya na cewa Baba ya sanar da ita abinda ake ciki tukunna ta 膹ago ta kalli Baba, cigaba da serving abincin tayi ganin yaqi kallo direction 膹inta jikinta a sanyaye.
K'iran Yaa Mera ne ya shigo wayan Ammah, farida dake xaune gefenta ta dauki wayar ta mika mata, Ammah ta daga tare da sallama, gaisawa suka yi snn Yaa Mera tace, "ashe Babana ya shigo gari, 膹azun nan kawai na ganshi ya shigo wllh", Ammah tace "ehh ya kai sati yanxu ashe bae je gaida ki ba" Yaa Mera tace "Wllh kuwa sae daxu ya shigo min" Ammah tace "Ikon Allah, amma bae kyauta ba, nima dae ina nn shigowa Yaa akwae wata magana da xamu tattauna, ko xuwa gobe da safe in'sha Allah xan shigo" Yaa Mera tace "Toh sae kin xo" da hka suka yi sallama Ammah ta ajiye wayar tana kallon farida, hawaye taga idonta tana kkrin gogewa kadda Ammahn ta gani, da mamaki Ammah tace "Ya aka yi farida? Ya haka?" Shiru farida tayi tana share idonta, ganin ynda Ammah ta kafe ta da ido yasa a hnkli tace "Ammah why Batuul?" Ammah tace "Ban gane ba" wasu hawayen suka kuma xubo mata tana girgixa kai tace "Ammah Ya Abuu fa ba shiri suke da Batuul ba, ga kuma matarsa masifaffiya muguwa, Batuul baxa ta iya masu ba cutar ta kawae xa su yi tayi gashi ba kowa gare ta can ba, don Allah ku canxa shawara ko cikin family can Maiduguri ki samu dai dai Ajiddehn a aura masa" tsaki Ammah tayi tare da maka mata harara tace "Toh naki yin hkan, da Batuul kadae xuciyata ta Aminta a hada Aliyu, uwar me Jiddahn xata yi mata wanda Allah bae mata ba, shi kuma Abuturrab din idan aka aura masa ita yyi gunduwa gunduwa da ita ya maido mana," mikewa farida tayi har lkcn tana hawaye ta fita daga dakin. Xaune ta ga Abuturrab dakinta ya rike kai da dukkan alama ita yake jira, yana ganinta kuwa ya mike da sauri ya karasa ya kamo hannunta suka xauna gefen gado yace "In tambaye ki farida, wae wnn kawar taki or wat ever ita tace tana son aurena?" Shi kansa jin tambayar yyi wani banbarakwae a baki don yasan Batuul baxa ta taba cewa tana sonsa ba, he is just confuse, farida ta girgixa kai tace "I don't think Batuul tasan da xancen ma, don daxu ta kirani tana ban hkurin xuwan da bata yi yau ba," ya fuzar da iska yace "Do me a favour little sis, don Allah ki xiga ta a kan kar ta amince nasan dae in har tace bata so baxa a mata dole ba" farida tace "Shknn I will try my best, but ni baxan mata magana kai tsaye ba sae in ita ta kawo xancen don ga dukkan alama bata san abinda ke faruwa ba ma" mikewa yyi rai ba ddi ya fice daga dakin.
Batuul na xaune dakin Anty duk hankalinta ya tashi ganin ynda uwar tata ke hawaye gashi ta ki gaya mata abinda ya faru, ae bata san lkcn da ita ma ta saka kukan ba tana durkushe kusa da Anty, da kyar Anty tayi controlling kanta ta shiga lallashinta sae dae ta k'asa gaya mata dalilin kukan nata don bata san ynda 'yar tata xata dauki xancen aurenta da Abuturrab ba, bude kofar dakin aka yi Ahmad ya shigo da sallama sae dae ganin ynda Batuul ke kuka hankalinsa ya tashi ssae don xuwa lkcn Anty ta daina nata kukan, hankali tashe ya shiga tambayar Anty abinda ya faru, Anty tace "kanta ke ciwo wae shine take kuka, ya aka yi Ahmad?" Ahmad ya durkusa kusa da Batuul yana mata sannu, sae da Anty ta kuma tambayarsa ya aka yi snn yace "Yayya ce tace in kira ta, kuma gashi kanta na ciwo bari kawae inje ince she's not okay" har ya mike Anty ta dakatar da shi tace "A'a bari xata je, ae ta sha magani" tayi hkn ne gudun wani maganan don har ynzu xuciyarta bae yi sanyin abinda yayya tayi mata daxu ba daga tace ita Batuul baxa ta auri mai mata ba in ma aurar da ita ake son yi gwara ta fito da saurayinta kawae, nn fa Yayya ta dinga xaxxaga mata ta inda take shiga ba nn take fita ba, mikewa Anty tayi daga karshe ta bar mata falon, shine tun lkcn take kuka a daki har Batuul ta shigo ta sameta. Kallon Batuul tayi tace "Tashi ki je Batuul" ba musu Batuul ta mike tana share hawayenta ta fita. Yayya na kishingide tana cin Apple, Baba na xaune daga gefenta ya tankwashe kafa suna magana da kanuri, k'arasowa cikin dakin Batuul tayi sae dae bata da walwala don tasan Yayya ce ta bata ma Anty rae ko bata fada mata ba, Xama tayi dan nesa da su tace "Ga ni Yayya" Yayya ta tabe baki ta mike xaune da kanuri tace "Wato har uwar taki ta xuge ki shine xaki wani shigo ma mutane ko sallama bbu, kin wani hade rae koh" Baba dae bae ce komai ba kansa na kasa, Yayya ta ci gaba da cewa "Toh auren Aliyu dae bbu fashi wllh, yaro d'an arxiki mai asali gaba da baya, waye bae san kakansa ba a Maiduguri?" Xumbur Batuul ta mike xuciyarta na wani mugun bugun da bae taba yi ba har wani rawa jikinta ya shiga yi tana kallon Kakar tata tace "Ban gane ba Yayya" da kanuri Yayya tace "Ohh ke da duk baki san abin da ake ciki ba, toh ae shirye shiryen bikin ki ake da Aliyu jikan Kyari, wato d'an wajen Ahmad" Batuul ta xaro ido cikin kidemewa tace "Ni Yayya?" Ae bata jira cewar Yayya ba ta fice da gudu daga dakin ta nufi dakin Anty, Har lkcn Anty na xaune ta xuba tagumi, ta xube jikin uwar tata cikin rawan Murya tace "Anty ban gane abinda Yayya take gaya min ba ynxu," K'asa cewa komae Anty tayi tana kallonta, hkn yasa Batuul ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Wayyo Na shiga uku Anty, wae Ya Abuu ake cewa xan aura, ni ban gane ba" Rungume ta Anty tayi sae dae she's lost of words.
Bayan Magrib Abuturrab na xaune daki abun duniya ya ishesa duk ya rasa tunanin da xae yi farida ta shigo tace "Ya Abuu Ammah na kiranka" mikewa yyi yace "kin yi abinda nace maki farida?" Farida tace "Ya Abuu bata fa ce min komai ba har ynxu, meaning she is still unaware, ni kuma baxa ta soma jin komai a bakina ba ka bari..." ficewa yyi daga dakin ba tare da ya tsaya jin sauran xancen nata ba, dakin Ammah ya shiga ya sameta tana waya, ya xauna har ta gama snn yace "Gani Ammah" Ammah tace "Dama cewa xanyi ka shirya kaje can gidansu Batuul ka gaida Yayya, ta shigo tun da rana" rasa me xae ce da ita yyi don bae son bacin ranta, da kyar yace "Toh Ammah" daga hka ya mike ya fita hankali tashe yasan shknn wani ikon Allah kawae xae hana a manna masa Batuul, wae for God's sake me suke son yyi da 'yar yarinyar nn?? Ya ma xae fara tunkarar Ajiddeh da wnn xancen, da kyar ya iya shiryawa ya dauki makullin motarsa ya fita daga gidan.
[8/22, 2:05 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.