Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 10 of 124

Bayan ya koma 膹akinshi ne yaji komai baya mishi da膹i, key 膹in mota ya 膹auka ya fita shehuri ba tare da ya cewa komai ba, kai tsaye dogarai suke bu膹e mishi k'ofa dan sanin matsayinshi da sukayi a fada, chamber Massa ya wuce kai tsaye ya shiga, Massa ya tadda kwance a makeken gadonshi na sarauta yana waya kuma da alama yana jin da膹in wayan da yake, waje Abutturab ya nema ya zauna akan 膹aya daga cikin royal chairs 膹in 膹akin, ganin wayan da Massa keyi bazai k'are bane ya sashi tashi ya fizge wayan ya katse, "dan wulak'anci na kai minti goma ina 膹akin nan, amma kakeyi kamar ba kasan ina nan ba ka zauna kana ta waya kana k'yalkyala dariya, ni banga ma abin yiwa dariya ba a waya da budurwa,mtsewww", tsayawa Massa yayi yana kallonshi har sai da ya gama yace mishi "mik'o min wayata in ka gama" mik'a mishi wayan yayi ya nemi waje akan gadon ya zauna ya dafe kanshi, ganin da Massa yayi abokinshi ba wasa yakeyi ba yasa shi zama kusa da shi dan ya san ba komai ke sashi damuwa ba, komai girman abu yana danne zuciyanshi, dafashi yayi yace "Man whats wrong, you dont look yourself, you seem to be upset, hope dai lafiya, tell me whats wrong am dead worried right now", ajiyar zuciya yayi yace "Su Abui ne suka ce that sun bani two weeks i should introduce to them the girl i would marry , ko kuma su nema min da kansu, wai bazan tafi project 膹ina ba mata ba" kuma you know i have no one at hand da zance musu gata am ready to marry, cikin jimamin abinda ke shirin faruwa da abokinshi yace "Man toh baga Ajiddeh ba, you guys go along well dan naga babu wacce ke samun attention 膹inka kamar ita kuma ma she is beautiful and everything" wani kallo Abutturab ya watsa wa Massa, "wa yace maka dan kyanta nake kulata, yeah i know there is this ounce of affection i have towards her but bai kai har ince zan aureta ba, su Abui should understand su k'aramin lokaci, i need time, bana son yin mata biyu, so kaga i should be given time dan in samu right choice 膹ina" k'arashe maganan yayi tare da nannauyan ajiyan zuciya" Massa ne yace mishi kawai kayi introducing Ajiddeh tunda tana sonka you can make her all you like, zatayi duk abinda kake so, Ko Shehu bazaiyi siding damu ba saboda shima damuwanshi kenan a kanmu, sai dai ma ya ce a k'ara dani, Man kawai muyi addu'an abinda yafi alheri", cigaba sukayi da hirar neman mafita daga k'arshe kawai suka yanke shawaran ya auri Ajiddeh tunda ita ka膹ai ce option 膹in dan basu san wacce su Abui 膹in zasu zab'a mishin ba, k'arfe goman dare ya mik'e yace da Massa zai koma dan yana da flight gobe by 11:00, sun fito waje Massa na rakashi inda yayi parking mota Massa ke tambayanshi, "Man ya akayi ne baka zo ba jiya inata jiranka", tambayan ne ya sashi tunawa da duk abinda ya faru tsakaninshi da Batuul, 膹an k'aramin tsaki yayi daga ciki yacewa Massa "gajiya nayi", dariya Massa yayi yana 膹an tab'a kafadarshi yace "ango tun bakayi auren ba har ka fara gajiya, toh in kayi auren kuma bazamu na ganinka ba kenan", Abutturab bai ce mishi komai ba ya bu膹e motarshi ya shige tare da ce mishi "sai munyi waya, ni zan wuce", Allah ya tsare hanya Massa yaayiwa Abutturab sannan sukayi sallama

Bayan sallah asuba babu wanda ya koma bacci, kowa shirin tafiya ya farayi, sai hayaniya akeyi a gidan, kowa ya tashi a gidan banda k'ananan k'arshe, Janet ce tayi knocking k'ofan, bayan an mata izinin shigowa ta shigo 膹akin, tarar da Aunty da Batuul a 膹akin tayi,Batuul na shiryawa Aunty kayanta da zata tafi dasu a cikin jaka, Aunty ce tace mata yarannan fa har yanxu basu tashi ba Janet, maza je ki k'irawo Fa'iza kuzo kuyi musu wanka dan 8 ya wuce, da toh ta amsawa Aunty sannan ta fita k'irawo Fa'iza dan suyi aikin da aka sasu, 膹aya nayin wankan 膹aya kuma na shafa musu mai da sa musu kaya, Batuul na gamawa tacewa Aunty "zanje in shirya sannan ta fita daga 膹akin Aunty ta isa d'akinta, wanka tayi sannan ta fito ta shirya cikin atampa exclusive green da pattern 膹in yellow da bak'i, 膹inkin yayi mata kyau sosai, skirt ne with peplum blouse mai three quarter hannu, ba a sa komai a jikin rigar ba sai patterns 膹in atamfar aka yi mata aiki dashi, 膹an kunne kawai ta saka bata sa sark'a ba, agogon gucci ta 膹auka ta mak'ala a hannunta, babu wani kwalliya da tayi sai kwalli kawai da ta saka a idonta, duk da ba tsayine da ita ba, bata saka takalmi mai tudu sai slippers din versace baqi da ta saka, luggage 膹in kayanta ta jawo ta ajiye bakin k'ofa sannan ta 膹auko k'aramin bak'in gyale ta ajiye a kafa膹arta, fitowa tayi ta sauko k'asa taga kowa ya shirya cikin kayan alfarma suna breakfast, shiyasa ma bata fara saka abaya ba dan tasan Baba sai yayi mata maganan abayar, k'arasawa tayi itama ta janyo kujera ta zauna , Aunty da Baba ta gaida a tare suka amsa mata sannan duka k'annenta suka gaisheta suma, Bismillah tayi ta fara cin abincin itama, a nutse suka gama breakfast ,tara da rabi dai dai aka fara fita da kayansu, manyan mazan kowa da hand luggage 膹inshi a hannu, na Aunty, Batuul dasu Hafix kuma yana hannun su Janet, Baba ne shima ya sauk'o daga bene rik'e da nashi, Batuul na hango shi da sauri taje ta karb'a ta k'arasa dashi k'asa ta bawa driver su fita dashi, Kanta ya shafa Yace ya gode , Baba na k'arasowa duk suka tashi suka fita suka nufi inda motocin gidan ke pake, Baa Liman ne da Sunday driver zasu kaisu airport, Batuul da Ahmad, Sa'eed, Khalil, Mus'ab mota 膹aya suka shiga while Baba, Aunty, Yusra, Mahir, Hafix da Aabid na mota 膹aya, sai da sukayi addu'an fita daga gida da ayatul kursiyu kamin drivers 膹in su fita daga gidan

Hanyan Maiduguri international airport suka bi, goma da rabi suka isa, ana shiga cikin airport 膹in heartbeat 膹in Batuul ya k'aru idonta ya fara tara hawaye, addu'a ta soma har taji ya 膹an ragu, bayan sun shiga har ciki sun sauk'a ta isa wajen Aunty ta ce mata, "Aunty tunda muka zo Maiduguri heartbeat 膹ina baya running at a normal pace, yanxu ma muna shigowa airport naji ya k'aru sosai", Aunty ce ta dube ta tuna da ranan da ta dawo idanunta sunyi ja, ce mata tayi "baki da gaskiya shi yasa yak'e karuwa, dariya sosai Batuul tayi sannan tace "kai Aunty, wane rashin gaskiya zanyi har heartbeat 膹ina ya rik'a karuwa, ni dai babu abinda nayi", ta juya ta tafi, binta Aunty tayi da ido dan itama ta tab'a shiga yanayi irin na Batuul na k'aruwan bugun zuciya, murmushi tayi ta girgiza kai sannan ta tattara kan yaran sukayi departures waiting room suna jira a k'ira su in jirgi ya shirya 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

11

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.