Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 41 of 124
31
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Washe gari da asuba Batuul na xaune kan darduma ta idar da sllh Anty ta shigo dakin tace mata in gari ya gama waye ta sameta a bedroom dinta, hakan kuwa akayi wajen takwas 膹in safe taje tayi knocking k'ofan Aunty, sai da taji an bata izini tukunna ta shiga, Aunty na kwance kan gado ganin Batuul ya sata mik'ewa dan dama ba bacci takeyi ba, tun daren jiya bayan sun gama magana da baba ta kasa samun nutsuwa, daga gaban dressing mirror Batuul ta tsaya ta kasa k'arasawa ganin yanayin Aunty kamar wani abun na damunta, alama tayi mata da ta zauna tukunna ta samu waje daga k'asa ta zauna tareda gaisheta, magana Aunty ta fara yi mata kamar haka "Batuul ke kika cewa Baba kina son aure" da sauri Batuul ta 膹ago kanta jin abunda Aunty ta fa膹a gabanta na faduwa, lkci daya idonta ya cicciko da hawaye ta ma rasa mey zata cewa Aunty, sai da Aunty ta sake magana tace tambayanki nake Batuul kika min shiru", hawayen dake idonta har ya fara gangarowa ta shiga girgiza kai cikin sheshek'a tace "Aunty wlhy Allah ban tab'a irin maganan da Baba ba, ni bansan wa ya fa膹a mishi ba, ni da nake son inyi karatu", taci gaba da goge hawayen dake kwaranya a idonta, da tausayi Aunty ta dubeta dan dama tasan babu yadda za ayi Batuul tace tana son aure, dama so take ta ga ko Batuul 膹in na da ra'ayin aure sai ayi mata amma ba da mai mata ba, ae kam sam baza ta yadda da wannan batun ba, baxata yrda a cutar mata 'ya ba, Aunty ta sauke ajiyar xuciya tace "rantsuwan kuma na meye,ni bance kimin kuka ba, tambayanki kawai nayi, tashi kije kici gaba da abinda kike yi Allah shi miki albarka," kasa mik'ewa Batuul tayi daga zaunen da take sai da Aunty ta sake ce mata "Tashi kije shikenan", hak'uri ta shiga bawa Aunty tana kwalla tace "dan Allah kiyi hkuri Anty amma ni bn ce ina son aure ba" tausayinta Aunty taji tace ta tashi ba komai, in ta shirya tafiya school ta sameta tukunna, da kyar ta samu ta tashi ta fita daga 膹akin dan har kanta ya fara sarawa.
Zaune yake a garden din gidan da yamma misalin biyar da wani abu yana kallon tsuntsayen dake ta shawagi abunsu a sama, dan yanxu bashida aiki sai na xama da tunani, wayarsa ne ya soma ringing, ya dauki wayar ganin mai k'iransa yasashi recieving da sauri cike da Mamakin kiran, daga daya bangaren Ammah tace "Ina neman ka ynxu" d'aga hka ta katse wayar, mikewa yyi da sauri ya nufi cikin gidan duk da bae san kiran da take masa ba amma ya ji ddin kiran Mahaifiyar tasa, har ya manta rabon da su yi magana ta waya da ita, bedroom dinta ya nufa da sallama ya tura kofar yaga bata ciki, dai dai nn farida ta fito daga dakinta ya juya yana kallonta yace "Ammah fa?" Tace "Tana bangaren Abui ae," a hnkli ya rufo kofar ya nufi bangaren Abui, sae dae duk jikinsa yyi sanyi ya rasa dalili, da sallama ya shiga falon kansa a k'asa ya xauna kan lallausan carpet din dake malale tsakiyar falon ya gaida iyayen nasa, Abui ne ya amsa, daga hka ya sunkuyar da kai yana jiran jin kiran da iyayen nasa suka masa, Ammah ce ta fara magana kamar hka "Aliyu kana jina koh" d'ago kai yyi yana kallonta sanin a serious issues take kiran sunansa kan tsaye, yace "Ina ji Ammah" in a serious tone tace "Aliyu a gskya mu kam bamu ga amfanin auren nn naka da kayi ba, Sam bashi da amfani, mun tilasta ka kayi aure ne don mu samu kwanciyar hankali kai ma hka, sae dae we were mistaken don tun da kayi auren nn hankalinmu ke tashe, baka yi sa'ar mata ba Abuu, da mun san abinda xae je ya dawo knn da bamu yi Na'am da yarinyar ba, kwata kwata bata san darajan iyayenka ba sae nata, don hka ni da mahaifinka mun yanke shawarar kara maka aure" d'ago kai yyi cikin rikicewa yace "Aure kuma Ammah?" Ta hade rae tace "Kwarae kuwa aure" marairaice wa yyi yace "Ammah ko shekara guda knn fa....." Tsawa ta daka masa tace "Ko ka wata guda ne, meye amfanin yarinyar da take neman rabaka da iyayenka da 'yan uwanka, kai har kana da bakin yi mana musu Aliyu, toh wllh ka guji bacin raina, 'yar mutunci da tasan darajanmu da xa kuma ta dinga nuna maka muhimmancin 'yan uwanka xa mu aura maka," ya share xufar da ke keto masa kmr xae yi kuka yace "Ammah wllh ina son Ajiddeh kuma ni bni da ra'ayin hada mata biyu, ku tausaya...." Wani tsawan da ya fi na da Ammah ta daka masa cikin fushi tace "Shknn Abuu, ni xan hakura in bar ma Ajiddeh kai sae ka maida ta uwarka, d'a na Aliyu da na sani a da baya min musu, jikinsa na rawa yake daukar duk abinda nace, ni kam wnn ba Aliyu na bne nasani...." Hawaye ne ke sakko mata sosae, jikinsa yyi sanyi ya dawo kusa da ita ya rike kafafuwanta cikin rawar murya yace "Haba Ammah, ni din bnxa xa ki xubar ma hawayenki, bani da amfani in har xa ki dinga xubar min da hawaye, kiyi hkuri ki rufa min asiri amma, hawayen ki masifa ne a gare ni, wllh na amince da kome kika ce, Aliyun ki ne ni ba a canxa maki ba wllh" duk ya rikice ba kadan ba yana rike da kafarta, kallonsu kawae Abui yake bae ce komae ba, Ammah taji ddin hkn ta shafa kansa cikin sanyin murya tace "Allah maka albarka" dagowa yyi da sauri ya daura hannunsa kan cinyarta yace "Nagode Ammah na" bata kuma cewa komae ba ya koma ya xauna ya langwabar da kai yana kallonta yace "To wace matar kika xaba min Ammah" kallonsa tayi bbu yabo bbu fallasa tace "Ba wata bace facce 'yar uwarka Bitti" xaro ido yyi ya koma baya da sauri yace "Batuul???" Ta hade rae tace "ita fa" innalillahi wa inna ilaihi raji'un, abinda ya dinga maimaitawa knn yana kallon Ammah da ke ta hararansa tana karkada kafa.
A bangaren Ajiddeh kuwa tun ranan da sukayi waya bata sake k'iranshi ba saima 膹agawa su Mummy hankali da tayi akan abinda ke shirin faruwa tsakaninta da Abutturab, su Mummy ganin abin na nema zama matsala ne dan ta dena kula kowa ita fa sai ansan yadda za ayi mijinta ya zama kamar yadda yake a da, Jainaba ce ta kawo shawaran su ziyarci sabon bokan da taji ance yana aiki kamar da bakin wuk'a amma fa ba a k'asar nan yake ba, yana can Tchad, a ranan sukayi shiri akan gobe zasu tafi, da daddare Mummy da kanta take sanarwa Daddy akan zasuyi tafiya gobe, da ya tambayeta inda zasu tace mishi ai kakar su Ajiddeh zasuje gaidawa sabida tun kamin aure rabonta da ita kuma ba lafiya bane da ita, da mamaki yake tambayan Mum akan dama Ajiddeh bata koma ba tun bayan bikin dan shi sam baisan ma tana gida ba, Mummy ce tace mishi "ehhh wai mijinta take jira akwai abinda yakeyi a nan 膹in", cewa yayi "kuna dawowa ta koma wajenshi, in ta zauna a nan 膹in amfanin mey take mana, taje can gidan nashi su zauna idan kun dawo", toh kawai Mummy tace ,cheque yayi musu signing yace su rubuta amount 膹in da zasu buk'ata tunda ziyara zasu, basu sanar dashi ma cewa da mota za a yi tafiyar ba, washegari k'arfe shida suka 膹au hanyan Maiduguri daga nan zasu shiga Tchad ta can, tafiya sosai sukayi bayan sun isa Tchad kamin su isa k'auyen da bokan yake, da k'yar suka samu sukaje inda yake, wata bukka ce da gani ta da膹e ko ina duhu sai wani 膽an haske dake fitowa daga windon bukkar, da zuwansu yace musu yasan abinda ke tafe dasu duk ya sai dai akwai abinda har yanxu ya kasa ganowa, shima baisan meye bane amma abin babba ne, kuma nan gaba yake shirin faruwa, har saida yace musu duk laifinsu ne da tun farko kamin bikin sun nemeshi da duk matsalan babu, hankalinsu ne ya k'ara tashi gaba 膹ayansu babu ma irin Ajiddeh suka shiga bashi hak'uri kamar sun mishi laifi, zata iya yin komai in dai akan Abutturab ne, gaban bokan ta sake matsawa tace "naji ranka shi da膹e, amma tunda al'amarin bai faruba yanxu, ni ayi min abinda zai manta da kowa kuma bazai sake waiwayen gida ba, sannan daga baya sai mu san yadda zamu b'ullowa abun dake shirin faruwan", kai ya ka膹a bayan ya gama jin batunta yace " hakan ma yayi", tashi yayi ya shiga wani 膹aki daga cikin bukkar ya fito rik'e da wani k'warya, sai da ya zauna ya zauna ya mik'o mata wani kuttu yace "ga wannan nan zaki samu tsohuwar bak'ar tsamiya, da hannunki zaki jik'ata, sai ki ajiyeshi a waje mai danshi da sanyi, kada ki bari rana ya tab'ashi, shi kuma wannan", ya mik'o mata wata bushashiyar fata yace "garin maganine a ciki, tunda dama yace kiyi tafiyarki toh aikin zai zo ma da sauk'i, wannan garin a k'ofar gidanki zaki barba膹a, sai kuma wajen kwanciyanshi nanma zaki barba膹a, Kinga yadda wannan tsamiyar keda tsami da duhu, haka zai rik'a ji duk lokacin da ya tuna gida, sanyin nan kuma da kika ajiye a wajan, duk lokacin da ya ganki ko ya tuna dake haka zai rik'a ji, g'arin nan kuma da zaki barba膹a, yadda iska zai kwasa ya tafi dashi wajen ya shafu haka zai shafe babin gidansu a k'wak'walwarshi", duk maganan har suka gama da yarensu sukeyi, wani irin murna Ajiddeh takeji har cikin ranta shikenan zata samu yadda takeso, ku膹i masu yawa suka zube mishi tareda mishi alk'awarin dawowa bayan kwana biyu, suna fita Ajiddeh ta dubi su Mummy ta ce "Mum, gobe zan koma, inada Visa ticket kawai zan siya shima online zanyi dan bansan lokacin da zai koma 膹in ba, gara inje tun wuri in gama abunda zanyi", Mummy ce tace "toh shikenan, duk yadda akayi sai ki fa膹a mana a waya, Allah dai ya taimakemu ya bamu sa'a, a daren suka 膹au hanyan birnin Tchad, murna fal cikin Ajiddeh.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.