Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 107 of 124

88

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

A guje ta fice daga d'akin tana riqe da bakinta, ko Ammah dake shirin shiga d'akin bata lura da ba tayi wucewarta , hanyar staircase tabi zata yi k'asa taji an rik'ota, Mum ta gani riqeda hannun nata, kuka kawai take tana girgiza kai alaman ta sakar mata hannu, wani uban harara da ta bita dashi ta fincikota tace "Sallamamiya Ce mishin kikayi kinada masaniya kan abinda ya samu tsinanniyar yarinyar?, toh Dan Ubanki duk abinda ya biyo baya ki kuka da kanki tambadadda, In banda lalaci irin naki Dan uwarki har ya isa ya wulakantaki ina gidan nan?, banda sunci darajar gidansu nake daga shi har uwar tasa da na karta musu rashin mutunci, shashashar yarinya, yanzun ma bata baci ba muje in keh baki iya kare kanki ni zan yi, wlhy ban san asarar haihuwa nayi ba da na zubdashi tun kamin kizo kina cusa min kuttu", ganin Ajiddeh na k'ok'arin k'wace hannunta yasa Mum cikeda fusata tace "kinsan Allah in baki kiyayeni ba sai naci mutuncinki, yarinya ana neman k'watar miki y'anci kina neman yi min tijara? Kuma wlhy kika kuskura kika tozartani saidai gidan wata uwar bani ba, tsine miki zanyi ki k'arasa lalacewa kibi duniyar gaba d'aya", ta fizgota sukayi hanyar d'akin, kan kujera Ammah ta tarar da Abu zaune ya dafe kai yana kallon marbles d'in d'akin, hannun Ammah da yaji jikinshine ya sauk'ar mishi da nutsuwa, hannayenta duka biyu tasa ta tallabo kanshi tareda shafa kanshi tace "Are you okay?", ido ya lumshe kamar maijin bacci da k'yar ya bud'esu yana kallonta ya girgiza mata kai alamun "Yeah am fine", kan nashi ta sake ta kamo duka hannayenshi tace "Badai dukan yarinyar nan kayi ba ko Aliyu, naga ta fice a guje tana kuka", ya kalli Ammah for some seconds snn ya bud'e baki da k'yar yace "I just don't want to see her anywhere around, not now not ever", Ammah da taji dad'in maganganun shi taja wata kujerar ta zauna tace "Alhamdulillah, Allah yayi mana tsari da masharranta, tayi maka admitting d'in sunada hannu ciki koh?," ido kawai ya lumshe ya bud'e dan gaba d'aya hankalinshi na wajen Batuul, ganin baison zancen tace "Ba komai ai ka kwantar da hankalinka, zamu jirayi hukuncin Abui, muji ya za ayi dasu, amma albasa batayi halin ruwa ba dan mahaifinta ba halinsa ba kenan, kuma nasan in har yaji wannan ta'asa da sukayi sai ransa ya b'aci, baiwar Allah yarinya k'arama da ita sun sata cikin azaba, mey sukeso mucewa Maryam ya sami y'arta?", ta matso kwallar dake idanunta tace " koma dai menene dukdai nina jawo shi tunda yarinya na gaban iyayenta hankali kwance nasa aka nema maka aurenta, bayin Allah ba tareda second thought ba suka bamu, Allah dai ya mata katangar k'arfe da mugaye", har Ammah ta gama magana bai bud'e bakinshi yace uffan ba, tunanin Batuul dake dad'a yi mishi yawa yasa ya zame hannayenshi cikin na Ammah ya mik'e yayi hanyar k'ofa, hannu yasa zaiyi sliding k'ofar yaji an rigashi ta d'ayan gefen, Mum ce janye da Ajiddeh ta shigo tana sababi, "Har mu za ayiwa sharri, Bilki kinyi kad'an kuma wlhy hukumace zata rabamu daku, wato tun kiyayyar da kikemin muna yarinta shine ya koma har kan y'ay'ana sai kin bisu da sharri ko, mu za ayiwa k'azafin yiwa wata figaggar yarinya can asiri, billahil azim sai kinyi Dana sani", Ajiddeh da damuwa ya cika ta rasa inda zata sa rai taji dad'i zubewa k'asa tayi tana kuka, Mum ta dubeta tace "Sun sallameki kin zama bakida amfani shine suke tunanin muma munyiwa wata can ko, kai kuma d'an mace an tura maka karuwa kanata cin amanar y'ata shine Dan Allah ya kamaku zaka lak'awa y'ata da bata san zance ba", ido Abu ya rintse yana fisting hannayenshi jin ta dangana Batuul da karuwa, kai yasa zai fice daga d'akin Ammah ta rik'oshi ta jawo shi gabanta tace "Abutturab inajin aure ne ya had'aka da y'arsu tun farko, inaso yanzun nan ba anjima ba ya rabaka dasu, mey za ayi da mugun iri irin wannan?, maza sallamar musu y'arsu, Allah ya had'a kowa da rabonshi", a firgice Ajiddeh ta tashi har wani dishi dishi take gani tazo gaban Ammah ta had'a hannayenta duka biyu tana kuka tace "Ammah Dan Allah kimin rai, nasan ban tab'a zame miki sirikar kirki ba, babu abin arziqi da na tab'a yi miki amma Dan Darajar Annabin tsira da aminci kar kisa ya sakeni, nasan ko bai sakeni ba tunda yace bai kuma son ganina nasan mutuwa zanyi, ki yafemin, ki roka min yafiyar Batuul ki rok'a min yafiyarshi in mutu da aurensa akaina, badan halina ba sai dan nasan ke uwace ta gari mai halin dattako, inayiwa d'anki son da bansan adadinshi ba a rayuwata", sanyi jikin Ammah yayi amma ko kallonta batayi ba tace "Babana ina jiranka, ka sallamesu su bar min gida", Jiki a sanyaye itama Ajiddeh ta kalleshi amma ko kallon inda take baiyi ba ya karb'e hannunshi daga rik'on Ammah ya fice daga d'akin, Duka Mum ta d'aka mata tace "Dan uwarki sai ki tashi tunda ke asararriyace, ban taba sanin ke mara hankali bace sai yau, har uwarsa ta bud'i baki tace ya sakeki uwar mey zaki zauna yi gidanta, kike wani cewa keh kinsan uwace ta gari ita, da y'arta ce baza ta tsaya....", ko kallonsu Ammah batayi ba ta fice daga d'akin itama, a guje Ajiddeh ta biyo Ammah tana ci gaba da magiya, Sau d'aya Ammah ta dubeta tace "Ba yafiyata zaki nema ba, wacce kika cutar zaki tambaya ta yafe miki", har ta sauk'o k'asa bata dena binta abaya ba, Abui da Farida tare suka fito jin hayaniyar Ajiddeh da Mum, kallon Mum yayi yace "Bilkisu lafiya?, mey ya sameta?", jin muryar Mum sukayi tana cewa "Ki fita harkar k'ananan mutane kizo mu wuce, kema uban ki nada gidan", Abui ya kalleta jin mey take fad'i snn ya kwalawa Abutturab k'ira, ba b'ata lokaci ya fito d'akin da Batuul ke kwance, yana ganin Ajiddeh ya had'e rai, Abui ya dubi Ammah yace "Mey yayi mata kina wajen baki hanashi ba", Ammah ta had'e rai ta tab'e baki tace "cewa nayi ya saketa", Abui ya dubeta da kyau jin abunda ta fad'i yace "Kan wane dalilli zakisa ya saki matarsa?, kaji shirme, kai Aliyu da hankalinka zaka saki matarka, kuskurene tayi kuma yarinya Allah ya tashi kafad'unta sai dai fatan Allah ya tsare gaba", Ammah ta fashe da kuka tace "Abui ya saketa kawai, dubi fa yadda suka cutar da Fatima amma uwarta ke musun sharri mukayi musu har da cewa k'ara zata kai mu munyi musu sharri", Sai lokacin Farida ta fuskanci kan zancen, Ajiddeh ta duba da wani mugun kallo ta tab'e baki ta matso wajen Ammah, Mum cikeda masifa tace "Yo ba Sharrin kukayi mana ba, wacece Maryam ma bare Fatimar har a wani yi mata asiri, kai kaga", ta nunawa Abu yatsa taci gaba "In ka fasa sakin nata baka cika haifaffen d'an bilki ba", Abui da mamaki yake kallon Mum, Abutturab da tunda yazo ya kasa d'ago kai a hankali cikeda nutsuwa batareda ya kalleta ba yace "I don't need a second thought, get out of my sight before I loose my cool, before you regret ever knowing me", yana fad'in haka ya juya batareda yabi ta kan kowa ba", Ajiddeh na jin haka ya fito daga bakinshi kuma a gaban Abui tasan zamanta gidanshi ya k'are, har wani dishi dishi take gani ta miqe tayi waje cikin hanzari batareda ta kula kowa ba ta fita a guje, Mum ce ta bita a baya tana kwala mata k'ira, girgiza kai Abui yayi yace Allah ya kyauta yayi sama , bayan kamar minti biyu Mum ta sake shigowa ta nuna Ammah da d'an yatsa tace "duk mey zai Samar min 'ya wlhy ki kuka da kanki", ta juya ta fice fuuu kamar wata iska

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.