Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 37 of 124
Babu abinda ke tashi a wajen nan sai sautin ki膹a, Hall ne mai girma da aka yiwa ado sosai na gani na fa膹a dan da gani kasan yaci Naira, Tun daga mota Abutturab yake k'iran number Ajiddeh amma bata receiving, fitowa yayi daga cikin motan yayi heading cikin hall, mata ne tare da maza kowa yana displaying talent 膹inshi na rawa, Ajiddeh ya hango daga cikin y'an rawa sai ka膹a waist takeyi, ranshi ba K'aramin b'aci yayi ba ganinta cikin maza tana rawa ga wasu shegun kaya da ta saka duk bayan ta a bu膹e, ji yakeyi kamar yaje ya fincikota amma babu hali, waje yaje ya samu ya zauna daga gefe yana jiran lokacin da zata gama, sai da suka gama tik'a rawansu tukunna bayan Dj ya k'are suka bar filin rawar, tana juyowa idonta ya sauk'a kan Abutturab, ha膹e rai tayi kamar ba ita ke dariya ba yanxu, k'arasowa tayi inda yake zaune ta tsaya mishi a ka k'erere tana 膹an karka膹a k'afa, 膹agowa yayi ya dubeta tare da cewa mata "Babe har kun gama rawan ne? " wani Harara ta sakar mishi tace "Kai fa ka cika wulak'anci, tun 膹azu muyi da kai zaka zo shine sai yanxu ka wani 膹ebo k'afa kazo, y'an uwana sai tambaya sukeyi ina kake, kowa yazo da mijin shi sai ni ka膹ai ce babu mijina, ni tun farkon nasan wulakantani kaso yi dama bada son ranka muka zo ba....." katse mata maganan yayi tareda kamo hannunta ya zauna da ita kan kujeran dake kallon nashi, magana ya fara yace "Babe c'mon, tun 膹azu fa nake wajen nan ina k'iran wayanki baki 膹auka, da na shigo kuma na ganki you guys were busy dancing" , a ranshi yana son yi mata maganan cewa ita matar aurece, bai kamata tana irin wannan shigar ba har tana Cu膹anya da maza, amma bazai iya ba, kawar da zancen yayi yaci gaba da cewa "so bana so in dameki shiyasa na bari sai kin gama tukunna sai ki ......" bai k'arasa ba yaga ta warce hannunta daga rik'on da yayi mata ta bishi da harara ta juya daga wajen ta nufi tsakiyar hall 膹in Jin an ambaci cewa y'an uwan Amarya suzo ayi hoto da ita, wani irin bak'in ciki yaji a ranshi wai shi Ajiddeh ke yiwa abubuwan nan da takeyi haka "toh meye ke damuna ne? " ya tambayi kanshi, inda tabi shima yabi da ido ya ganta ita da sauran y'an uwanta maza sun sata a tsakiya cameras nata haskasu sai washe baki takeyi yana cikin tunani yaji an da dafashi daga baya, a 膹an firgice ya juya yaga ko waye, kanshi ne yaji yayi dammm tare da zaro ido ganin mutumin da yake expecting gani least a wajen, zagayowa yayi ya zauna daga 膹ayan kujeran murmushi 膹auke a fuskanshi yace "Ashe kana gari, Well i can see you are surprised to see me here ko bro? , bai bashi ansan tambayan da yayi mishi ba sai ma jifanshi da yayi da nashi tambayan shima "What brought you here Sadiq? Mey kazo yi?" Shima bai bashi amsa ba sai ce mishi da yayi "Answer me first bro, ni na fara tambayanka kuma your question is irrelevant, yaushe ka shigo Nigeria, ko da shike dama ance mana kana shigowa mune dai bama ganin ka " 膹agowa yayi da sauri ya dubi Sadiq Jin abinda Sadiq 膹in yake fa膹i , cikin rashin Jin da膹in abinda Sadiq ya fa膹a mishi yace "ance muku ina zuwa Nigeria? Su waye ke fa膹a muku cewar ina zuwa" murmushin takaici Sadiq ya saki yace "Allah sarki these doesn't matter now, Ni auren Abokina Muhsin nazo, shine angon, so banma jima da shigowa ba, but tunda na shigo na ganka wani xuciyar ke cemin ba kai bane, I thought ma gizo kake yimin ba kai bane cus I wasn't expecting you " , sai da yayi shiru tukunna Abutturab yace mishi "Ai Amaryar k'anwar Ajiddeh ce, so shine muka zo Dan kusan Ajiddeh ce tayi sponsoring biki saboda mamar yarinyar ai ta rasu" kai Sadiq ya ka膹a yace "Ohhh , that's nice then, toh yau 膹in zakaje gidane ko kuwa zaka koma ba tare da kaje ka gaida Ammah ba " jikinshi ne yaji ya da膹a sanyi Jin an ambaci sunan Ammah, ba tare da ya yadda sun ha膹a ido da Sadiq ba yace "toh shikenan bari in fa膹awa Ajiddeh zamuje yanxu, k'ar inje kuma bata sani ba hankalinta ya tashi " , da tausayin 膹an uwan shi a ranshi yace "gaskiya hakan ma yayi kyau, kaga kar tazo tana ta nema ai babu da膹i" , yace "Ehhh shine yanxu zan k'irata, naga ma she is so busy yau 膹innan" , yaci gaba da dialling 膹in number ta, da k'yar aka samu ta 膹auki wayan bayan ya k'ira kamar sau bakwai , tana 膹auka tace mishi "baby wai meye haka, baka ganin am busy ne ? Kasan fa ni nayi komai na auren nan kuma na da膹e ban ha膹u da y'an uwana ba ai sai ka barni in huta, da ka k'ira kaji ban 膹auka ba ae sai ka hak'ura, amma ka ta wani k'irana sai kace ladan a masallachi" , sai da ta gama ya kwantar da murya yace "sorry Babe, something came , zanje wajen su Ammah ne in duba su, ya da膹e da na gansu, I will go briefly and come back " , batasan lokacin da ta mik'e daga zaunen da take ba, gumi ne taji gaba 膹aya ya fara tsatsaffo mata, Ce mishi "Aliyu ba muyi haka dakai ba, mu da zamu koma gobe mey zakaje yi, toh ni dai bana son zuwanka, kuma baxa kaje ba " , samun kanshi yayi da katse wayarta, har sai da yayi mamakin kanshi shima, mik'e wa yayi ya cewa Sadiq "muje ko? " kallon mamaki yabi Abutturab dashi wai wannan shine yayanshi da yake takawa maza ma birki amma yau shine da kanshi mace ke mishi tsawa har yana ji a waya, ji yayi hawaye na son zubo mishi yayi maza ya maidasu yace "Yaa Abu muje" , ya shige gaba Abutturab na binshi daga baya,
Wani ihu ta saka tare da fashewa da kuka, hankalin su Mummy yayi kanta a tashe, tambayanta suka shiga yi lafiya take ta ihu haka amma tak'i magana, Yaa Zee ce tace mata " a k'ira miki mijin nakine ko wani abin ne ya sami mijinki", wani irin kallo ta Watso mata tace "Da wani abun ne ya same shi ai duk mai sauk'ine akan abinda yake shirin faruwa" taci gaba da kurma ihunta, su Mummy ganin tana Janyo hankalin mutane kansu tayi maza tasa su tafi da ita gida, har suka isa gida tana kuka suko sun sata gaba suna kallonta suna jiran Jin meye ke damunta, sai da tayi shiru tukunna tace " Mummy Aliyu ya tafi gidansu, duk k'ok'arina na kar yaje sai da yaje kuma gashi malamin nan sai da yace indai nayi mishi toh ko kar in yadda ya ha膹u da 膹an gidansu ko 膹aya in ba haka ba Babban Al'amarine zai biyo baya, Mummy ni ban san meye Al'amarin ba amma duk yadda akayi ba mai kyau bane, gashi kuma ya tafi, Mummy ya tafi na shiga uku, bige mata baki Mummy tayi tace "akan wannan abin kika 膹agawa kanki hankali, mu inane bamu shiga, ai in yasan wata baisan wata ba, ki kwantar da hankalin ki ba gobe zaku koma ba, toh babu abunda zai sameku daga ke har shi 膹in " a haka dai suka ci gaba da bata hak'uri da baki har suka samu tayi shiru amma ba Dan hankalinta ya kwanta ba, Dan gaba 膹ayansu basu san waye Aliyu ba, ita tasan yadda ta wahala a hannunshi farkon aurensu , tasan idan asirin nan ya karye toh nata ya k'are
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.