Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 103 of 124
Sadiq ne ya d'auko Zamzam d'in da ake buk'ata a side d'in Abui, a cup Asheikh ya d'an tsiyaya snn ya samu waje ya zauna ya fara tofi cikin ruwa, Abu dai har lokacin ya kasa cewa komai sai ido da ya zuba mata idonshi duk ya kad'a, motsin kirki ya kasa yi, he is so freaked, gani yakeyi duk wanda ya tab'ata ce mishi za ai ta bar rayuwa, Asheikh da ya gama tofin shi ya miqe ya dawo gaban kujerar da Abu ke riqe da ita, Abui yace "Aliyu ko zaka samu a gyarata tasha maganin", kamar badashi akayi maganan ba, saida Asheikh ya sake maimatawa snn ya d'ago rinannun idanunshi dake cike taf da hawaye kamar wani yaro, kai Abui ya kad'a mishi alamun he should be strong tare da zuwa kusa dashi ya zauna ya dafa mishi kafad'a yace "Abutturab you have to be strong okay?, zata samu lafiya In sha Allah kaci gaba da yi mata addu'a, ido ya lumshe snn yace "Abui bata mutu bako, baza ta mutu ba In San Allah", sosai Abui ya tausaya mishi yace "ciwo ai ba mutuwa bane Aliyu, zataji sauki da yardar Allah, kayi yadda yace d'in ka kwantar da ita a nema mata lafiya", gani yakeyi kamar in ya sauketa daga jikinshi wani abun zai sameta, kallonta yayi for some seconds snn jiki a sanyaye ya shimfid'eta kan doguwar kujerar amma har lokacin hannunta na cikin nashi, Asheikh ya karaso gaban kujeran ya tsuguna daidai kan Batuul snn ya mik'awa Abu ruwan yace "amshi ka shafa mata a fuskarta", hannu Abu ya mik'o ya tsiyaya mishi ruwan snn ya shafa mata shi a fuska, bayan ya gama ya sa a mik'o k'aramin spoon yace Abu yana sa mata droplet a baki, jiki a sanyaye ya anshi cup d'in ya d'ebi kad'an ya d'iga mata shi a baki, wani irin dogon numfashi taja da ya sa Abu saurin kamota yace "Batuul am glad you are alive, don't leave me again kinji, don't plsss", sai ga hawaye nan idonshi, bata bud'e ido ba haka nan batasan abinda akeyi ba, kamar ba ita tayi wannan numfashin ba ta koma yadda take d'azu, Asheikh yayi gyaran muryan yace "Alhamdulillah, wannan ruwa da ta sha ya dad'a tabbatar mana da lallai asiri akayi mata kuma yana nan cikin jikinta, yawo yakeyi gaba d'aya jikin nata dan a ruwa aka jefa sihirin da akayi mata, yadda yake yawo cikin ruwa haka itama yake yawo cikin jikin nata snn gaba d'aya rayuwar aka so ta bari da ita da abinda ke cikinta amma da yake Allah yayi tana da saurin numfashi bata mutu ba sai dai za a ci gaba da magunguna snn anayi mata sauk'ar Qur'ani da kuma tofi kullum, In sha Allah da yardar Allah zata samu sauk'i", Abui yace "Subhanallahi, La hawla wala quwata illa billahil aliyyil Azim", Sadiq dake tsaye shi ma tun d'azu ya rasa ma abin fad'a, yanzu har Batuul abar ayi ma asirice, duniyan nan is so cruel, Allah ya bata lafiya su kuma Allah ya toni asirinsu koma su waye sukayi mata", kamar wanda aka tsikara haka Abu ya mik'e ya isa gaban Asheikh yace "Asheikh inaso in san su waye sukeson cutar da ita da dalilinsu na cutarta, yanzun nan bama sai anjima ba, Ko su waye su sai nasa sun gane kuaransu na cutar min mata da sukayi", Asheikh yayi murmushi yace "Toh mu dai baza muce ga wadanda sukayi mata ba har sai ta samu sauk'i, in akwai likita sai a samoshi ya riqa dubata da abinda ke jikinta, snn tunda ba abinci zata ci ba, su sai su duba suga yadda za ayi tana samu, mu kuma a namu b'angaren zamuyi kok'arin ganin mun taimaka da addu'a", Jinshi kawai Abu yayi amma ba wai ya aminta da zancen ba, Abui yace "Toh Asheikh mun gode sosai", yace a k'ira mishi Aunty Amna ko Ammah yayi musu bayanin sauran magungunan nata da yadda za ayi amfani dasu, Aunty Amna ce tazo amma Abu sam ya kasa ya tsare sai shi aka bawa magungunan yace "Zaitun d'in za a riqa shafa mata shi a dukkan jikinta, Ma'ul ward d'in kuma ana d'iga mata shi a baki, kad'an kuma a saka a wool a kai mata hanci ta shak'a, Habbatus saudanma jikinta za a riqa shafewa dashi kamin ta kwanta, Abu ne ya anshi komai.
Tuk'i sukeyi hanyar Jere, Driver sai dariya lbr raha yake yi yana kyakyatawa, yana son fita irin wannan da Dad keyi ba tareda entourage d'inshi ba, kamar daga sama sai ganin mata sukayi sanye da Hijab d'inta ta shigo titin a guje, ji kake k'iiii ammma ina saida suka buge ta, daga nan sukayi losing control d'in tasu motar, Babu abinda Daddy yake fad'i sai "Innalillahi wa inna illaihi rajiun", abinda ya dinga nanatawa kenan har motar taje ta bugi wata bishiya snn motar ta tsaya, kan kace meye mutane har sun cika wajen wasu suna wajen matar da aka buge wasu kuma sunyi wajen motar, jin surutun mutane yasa Dad sanin lallai da sauran ransu, a hankali ya d'aga hannunshi da yakeji kamar ba nashi ba ya tura k'ofar motar, Driver dake gaba sai faman kokuwa yakeyi da airbag da ya rufe mishi fuska, mutanen dake wajen ne suka taimaka musu suka fito daga cikin motar, daga can Side d'in sukaji ana ihun "ta mutu", wasu suna "ba mutuwa tayi ba ayi saurin kaita asibiti", da sauri Daddy ya karasa gurinsu, ganin matar taji ciwo sosai yasa cikin hanzari yace "Dan Allah bayin Allah akwai wani wanda ya santa cikinku sai muje dashi asibiti dake cikin gari", duk mutanen dake gurin kowa yace su gaskiya basu tab'a ganinta ba, haka duk suka riqa zuwa suna kallonta suna basu santa ba, ganin ana b'ata lokaci yasa Dad yace musu "Toh koh zaku had'a mu da wani da kuka yarda dashi mu tafi asibitin dashi, sai yaje ya gano inda muke ko daga bayane in Allah yasa an samu y'an uwanta sai mu dawo da ita", duk yawan mutanen dake gurin nan kowa mak'e kafad'a yayi yace shi baxa shi ba, Mutumin birni ba abun yadda bane", d'an k'aramin tsaki Dad yaja yace "Ado zo mu taimaka mu sata mota, mutanen nan ba lafiya ne dasu ba", Ba b'ata lokaci Ado yazo suka kamata suka sata mota, mutanen ganin dagaske suke tafiya zasuyi da ita yasa suka kama surutu, kota Kansu Daddy baibi ba yacewa Ado yaja motar su tafi, Abuja suka karaso direct suka wuce asibiti lokacin ana kiraye kirayen Sallar Magrib, suna zuwa aka karb'eta aka fara bata taimakon gaggawa
Bayan Asheikh ya koma guest side ne Abu ya d'auki Batuul yayi d'akin Ammah da ita ya kwantar da ita kan gado, ya jima yana yi mata addu'a da fatan samun lafiya kamin Ammah tace yaje ya watsa ruwa yayi Sallah dan ko azahar da la'asar d'inma duk a gida yayisu, sam yaqi barin wajenta, abinci kam har lokacin ba a samu ya shiga cikinshi ba, tunda ya dawo sai yanzu ya shiga d'akinshi, gaba d'aya ya manta da zancen wata Ajiddeh a gidan, ajiyar zuciya ya sauke ganinta zaune bakin gadon kamar mai jiran ace cas ta sa gudu, K'araswa yayi cikin d'akin ya zauna kan gadon tareda riqe kan da duka hannayenshi, a hankali ta dawo gefenshi ta zauna ta d'an dafashi tace "Sannu, how is she feeling now?", bai bata amsa ba sai rungumeta da yayi tsam a jikinshi, har saida ta tsorata jin irin force d'in da yasa a hug d'in, kok'arin kwace kanta takeyi amma sam bai saketa ba, maganganun Asheikh kawai yake tunawa da yace da abinda akayiwa Batuul ta fara wannan ciwon, a hankali ya d'aura fuskarshi kan wuyanta ya fara magana a hankali "I can't risk losing her for anyone, they were trying to hurt her, so suke su rabata da rayuwarta, Mey tayi musu zasu maka haka?", kyarma jikin Ajiddeh ya fara bugun zuciyarta ya tsananta har wani danshi takeji yana bin jikinta, saketa yayi ya rik'o kafad'unta yace "Hauwa do you know they wanted killing her?, an encounter with them will have to b their worst nightmare, I will make them pay for each pain they caused her", da sauri Ajiddeh ta d'ago itama idonta duk ya cicciko da kyar tace "Its okay babe, they will surely pay for it, amma kasan su waye?", kai ya girgiza mata alamun No, ta saka hannayenta cikin gashinshi tace "Everything will b fine kaji, kaje kayi wanka, you need rest", mikewa yayi ya shirya ya shige toilet, baki Ajiddeh ta toshe ta saki wani irin kuka, tausayin rayuwarta ta fara, in dai Abu ya gano she is behind komai tasan zamansu ya xo karshe, har ya fito daga wanka tana nan inda ya bar ta, cikin few minutes ya shirya cikin kananun kaya ya dawo kusa da ita ya xauna yace " You also need some rest, ki tafi kiyi wanka, farida will get you something to eat sai ki kwanta" mikewa yayi ya fiddo mata da towel ya mika mata ta karba a sanyaye ta mike ta shiga bathroom din, kwanciya yayi ya lumshe ido ya dafe kansa da yayi masa nauyi, ji yake kamar ciwon Batuul ya dawo jikinsa kawai, da yake a gajiye yake gashi tun jiya rabonsa da bacci, lokaci daya baccin ya daukesa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.