Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 49 of 124

38

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Jiki a sanyaye ta mik'e ta fito daga 膹akin ta sakko downstairs, ganinshi zaune a palo yasa ta jin da膹in kimonon da ta 膹aura kan kayan dake jikinta, 膹auke kanta tayi kamar bata ganshi ba tayi hanyan kitchen, da ido ya bita har ta shige tukunna ya 膹auke idonshi daga wajen, tana shiga tace "Na'am Aunty, gani", tray da aka cika da snacks iri iri sai drinks da ruwa Aunty ta nuna mata tace mata "膹auki ki kaiwa Abuu", da sauri ta 膹ago zuciyanta sai fa膹uwa yake tana kallon Aunty dake ta aikinta tace "Aunty ni kuma", ba tareda da ta juyo ta kalleta ba tace "ehhh 膹auki ki kai mishi tun 膹azu yake zaune ban sani ba kuma babu wanda ya fa膹a min", zuciyanta duk babu da膹i har idonta ya fara hawaye ta matsa gaban Island 膹in ta kinkimi trayn tayi waje, tunda ta fito yake kallonta har ta iso palon, 膹an nesa dashi ta ajiye mishi trayn fuskarta daure ta juya tayi tafiyarta, murmushi yyi ya ci gaba da kallon tv da yake, kitchen 膹in ta koma ta tsaya bata cewa kowa komai ba ta hau kan deep freezer ta zauna, juyowa Aunty tayi zata cewa Janet ta mik'o mata abu a Fridge taga Batuul zaune kan Fridge, kallonta Aunty ta tsaya yi da mamaki tace "Batuul meye hakan, mey kika dawo yi kika barshi shi ka膹ai a palon", kanta ta girgiza tana kallon Aunty tace "Aunty toh ai abinci zai ci kuma ma nifa.....", bata k'arasa ba ganin kallon da Aunty keyi mata ta sauko tace "kiyi hak'uri zanje", ta juya jiki a sanyaye ta fita daga kitchen din, da k'yar take 膹aga k'afanta har ta isa palon, yana nan inda ta barshi yana kallonn Discovery channel, sau 膹aya ya 膹aga kai ya kalleta ta sadda kai k'asa tana ta fidgeting yatsunta, ya 膹auke kai yaci gaba da kallonshi har ta k'araso ta zauna can nesa dashi, lokaci lokaci yake satan kallonta ita ma hka, sai da programm 膹in ya k'are tukunna ya dubeta, ta sadda kai k'asa tana wasa da yatsunta, sauk'a yayi daga kujeran ya janyo trayn yana kallonta murya can kasa yace "Baki fa膹a musu sak'ona ba knn har ynxu koh?" Kin cewa komae tayi kuma bata d'ago kanta ba, kallonta ya tsaya yi, ta dan sata kallonsa jin shirun yyi yawa, suka hada ido ta dauke kai da sauri, kallon hanyar kitchen yyi kafin yyi kwafa ya dauki glass cup ya bude lemon kwalin dake kan trayn da ta ajiye masa ya tsiyaya ya mayar ya rufe, ba tare da ya kalleta ba yana girgixa kai cikin sanyayyan muryarsa yace "Ni tausayin rayuwar ki da nake yasa ki ka ga ina maki kashedin kar ki yrda su makala min ke, yhu are too young to start facing challenges or rather I shud put it as problem, ni ina da matata kuma muna son junan mu like! har kika kuskura aka yi auren nn u will only end up shattering ur life, it's still not late for yhu...." Bata Bari ya kai karshe ba ta xamo kasa da sauri hawaye na bin kuncinta xuciyarta na tafasa tace "Kai wae me xae hanaka yin magana sae ni? Naga kai ma xaka iya gaya masu baka son auren ae koh?" Yyi wani murmushin da ta kasa fassara nufin shi yace "Ni baxan iya yi ma iyayena musu ba, ina ganin darajan su shi yasa kika ga har ynxu ban musa masu ba" wani mugun kallo ta shiga yi masa har lkcn tana hawaye ssae tace "Kai ne kasan darajar iyaye ni ban sani ba koh, toh kmr ynda baxa ka iya masu musu ba nima baxan iya ba, sae dae idan an makala maka ni ku kashe ni kai da matarka" tana kai wa nn ta mike tana kuka ssae ta haura sama da gudu, bin ta da kallo yyi yana murmushi, kafin ya fara shan drink din hannunsa, cake kawae ya dan ci ya mike yace ma Janet da ta fito daga kitchen ta ce ma Anty xae koma, fitowa Anty tayi bayan Janet ta bata sakon shi, tayi Mamakin rashin ganin Batuul a falon sae dae bata nuna ba tace "Har xaka tafi Abuturrab" Yace "Eh Anty, it's almost time for sallat ne" tace "Toh shknn, Allah ya tsare" fita yyi daga falon, ita kuma ta nufi sama don xuwa jin dalilin kin jin maganarta da Batuul tayi rai a bace, dakinta ta sameta kwance tana kuka har da sheshsheka, Anty ta tsaya daga bakin kofa tana kallonta tace "Meye hkn Batuul?" Mikewa xaune tayi da sauri ta kuma fashewa da kuka tace "Don Allah Anty ku rufa min asiri a fasa auren nn wllh bana son ya Abuu shi ma baya sona ..." Harara Anty ta galla mata tace "Wnn kuma sae ki jira idan babanku ya dawo ki sanar da shi" tana kai wa nn ga juya ta fice daga dakin.

Aunty na shigowa daki taji wayanta na ringing, kamin tayi picking taga har ya katse, 膹auka tayi ta duba taga wa ya k'ira, missed calls biyu ta gani duk Ammah ce ta k'ira, zama tayi daga bakin gado zata k'ira kenan wayan ya fara ringing, Ammah 膹ince ke k'ira, 膹agawa tayi tare da yi mata sallama, bayan sun gaisa Ammah ke tambayan Aunty "Maryam ya shirye shirye", murmushi Aunty tace "Alhamdulillah Ammah", ita har yanxu mamaki take na zata aurar da Batuul nan da y'an kwanaki, Ammah ce ta katse mata tunani da cewa "dama kayan Batuul ne nakeso a tambayar min ita inda akwai abunda take buk'ata dan Aliyu ya tambayeta tace ita bata son komai, toh ni ba yarda nayi dashi ba shine nakeso a bincika min sannan gyaran jiki zan turo a kawota gida sai ayi mata duk abinda ya kamata", shiru Aunty tayi har sai da Ammah ta kai aya tukunna tayi ajiyan zuciya tace "Toh Ammah zan tambaya miki ita, sai dai gyaran kamar zai fi tayi a gida nake gani ba sai taje can 膹inba ai hidima zaiyi yawa, har nayi magana mai gyara gobe zata zo daga Ndjamena", cewa Amma tayi "toh shikenan hakanma yayi", da haka suka gama wayan, zaman tunani Aunty ta yi dan ita bata da wani shiri ma da zatayi na bikin, ko y'an uwanta ma bata fa膹a musu, waya ta sake 膹auka tana k'iransu 膹aya bayan 膹aya duk ta sanar dasu auren Batuul, sai mamaki sukeyi ganin abun yazo da wuri.

Bayan Abuturrab ya koma gida da daddare Abui ya k'irashi har si膹e 膹inshi, daga palo ya tarar dashi kishigi膹e yana kallon News, da sallama ya shiga ya zauna k'asa sannan ya gaidashi, gyaran murya yayi sannan ya k'ira sunanshi, "Aliyu", a hankali ya 膹ago dan gaba daya jinshi yayi wani iri dan Abui baya k'iran shi da sunanshi, yace "Aliyu na nema maka auren Batuul bawai dan na isa inyi maka abinda nakeso ba, bawai kuma dan bana sonka ba sai dan inason ci gabanka, yarinyar nan amana zan baka, ba iyayenta ka膹ai bane suka baka amanarta, har ni amananta zan baka, ka rik'eta kamar yadda zata zauna a gun iyayenta, in ka cuceta toh ka cuci amanar mu, yarinyace ita sannan mace, she is so naive and weak sai kayi hak'uri da ita, sannan bawai dan an ha膹aka da ita ka fifita matarka da kakeso kanta ba, kayi k'ok'arin adalci tsakaninsu sai kaga Allah yasa komai yazo maka da sauk'i, Aliyu ban yadda da saki ko yaji a tsarin zaman aurenka inba maishi ya sab'awa shari'a ba da bama fatan faruwanshi, ka kula da ita kamar yadda zaka kula da Farida, bana son ka zama silar rugujewar abotan da yake kulle tun kamin zuwanka duniya, kaji tsoron Allah a duk inda ka tsinci kanka, In sha Allah aurenka da Batuul alheri ne", k'asa 膹agowa yayi dan wani nauyi kanshi yayi mishi, ji yayi kamar abu aka 膹aura mishi a kan, Abui ne ya sake k'iran sunanshi, da k'yar ya 膹ago ya iya cewa "Na'am Abui", wani chest box ya 膹auko daga gefenshi ya mik'o mishi yace "ga wannan shine Sadakin Fatima, shi za a mik'awa Waliyyin Batuul as Sadaki, sannan a can zataci gaba da karatunta, kayi supporting 膹inta in every way to the best of your ability tunda tana karatunta muka nema maka aurenta, Allah yayi muku albarka", wasu makullai guda biyu ya mika masa yace "wannan na motane bayan an 膹aura muku aure sai ka bata, wannan kuma gidana na farko dake Mississipi street na bata shi halal", da sauri ya 膹ago ya kalli Abui da mamaki, shi ya rasa gane wane irin so suke yiwa Batuul dashi da Ammah, ko aurenshi na fari basuyi wannan abin haka ba, da k'yar ya iya bu膹e baki yace "In sha Allah Abui, zanyi yanda kace,", yace "yawwa, ka gama arranging gidan da zata zauna na nan da can ko kuma ha膹asu zakayi waje 膹aya", kai ya gya膹a tareda cewa "Yeah a can dai tare zasu zauna amma a nan Asokoro nacewa Mum zata zauna", Abui yace hakan ma yayi kyau, Nasa Mustapha da Sadiq suyi duk necessary arrangement 膹in 膹aurin auren, Allah ya tabbatar muku da alheri ya taya ka riko, Allah yayi muku albarka", jiki a sanyaye ya mik'e yayi wa Abui sallama ya fita.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.