Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 53 of 124
Sai wajen k'arfe goma ya shigo cikin gidan, kai tsaye 膹akin Ammah ya nufa, sallama yyi can kasa ya tura kofar dakin ya shiga kansa a kasa, Ammah na waya daga xaune gefen gado, Batuul kuma na xaune kasan lallausan rug din dakin ita da farida da ta sata gaba ta ci abinci, gabanta ya fadi ba kadan ba ganinsa tayi saurin d'aga mayafin dake kan kafadarta ta mayar kanta ta rufe har fuskarta da shi, shi kam Karasowa cikin dakin yyi ya ja stool din gaban mirror ya xauna, Farida ta gaishesa ya amsa ba tare da ya kalli inda suke ba, Batuul ta shiga jujjuya spoon din hannunta cikin shinkafa da miyan gabanta, a hnkli Farida tace " Ki ci mana besty, ko in dibar maki sinasir din ne?" Batuul ta girgixa mata kai kawae, Ammah ta juya tana kallon Abuturrab bayan ta gama wayar da take, ya sauka kasa ya gaisheta, tace "Sae ynxu Abuu" dan shafa kansa yyi yace "Muna tare da Massa ne Ammah" Ammah tace "ina massan?" Yace "Bae dde da tafiya ba" Ammah tace "Toh ka ci abinci kuwa?" Bata jira cewarsa ba ta juya tana kallon Batuul tace "Bitti kin gama cin abincin?" Farida tace "Taki ci Ammah" dawowa kusa da su Ammah tayi tace "sbda me Bitti? Nan fa ba bakon waje bne ki ci abinci" sunkuyar da kai Batuul tayi, Ammah tace "Maxa ki ci Kinji" mikewa Ammah tayi tace "Bari in je gun su Amnah ina xuwa" d'aga hka ta nufi kofa Abuturrab ya bi ta da kallo ganin ko ta kansa ba ta kuma bi ba, girgixa kai yyi cike da takaici, Farida xata mike Batuul ta riko ta da sauri murya can kasa kmr xata yi kuka tace "Plss kar ki tafi farida" tausayin ta ne ya cika ta, ta juya tana kallon Abu ta ga hararanta yake yi, a hnkli tace "ynxu xan dawo Batuul waya ta xan dauko" a sanyaye Batuul tace "Promise?" Farida ta gyada mata kai snn ta mike ta fice daga dakin. Mikewa yyi ya dawo gefen gado ya xauna kusa da inda take xaune a kasa, girgixa kai yyi yana wani irin murmushi yace "Happy for yhu an makala min ke, ba dae kince kin ji kin gani xa ki iya ba koh?" Banxa tayi masa gabanta na faduwa hawaye na bin kuncinta, yace "Toh wae ma wa kike rufe ma fuska ma tukun?" Nan ma dae bata tanka sa ba, ransa ne ya fara baci yace "Kehh!" Still taki cewa komae, sakkowa kasa yyi ya dawo gabanta yana facing dinta a fusace yace "How dare yhu ina maki magana kike kyaleni?" Kmr jira take ta fashe da kuka ssae ta shiga rerawa, bude baki yyi yana kallonta cike da mamaki, can ya runtse ido yace "Na maki wani abun ne?" Kukanta kawae take bata ce komae ba ya bude idanuwansa yace "Ohhk Allah ya baki hkuri" mikewa yyi ya koma inda yake ya xauna, ya kusa minti goma xaune bata bar kukan da take ba shi kam sae kallonta yake sae dae fa xuciyarsa tafasa yake, gashi yana shakkar kuma ce mata komae don yasan sae kwanan gidan ya gagaresa daren, don kanta tayi shiru daga karshe, abincin gabanta ya kalla xae yi magana Ammah ta shigo, karasowa gun Batuul tayi tace "Kin cinye abincin Bitti" a hnkli Batuul tace "Na koshi" Abuturrab yace "Ammah ban fa ci abinci ba duk yau" daukan plate din gaban Batuul tayi ta mika masa tace "gashi ka kara a nn kar a xubar bata wani ci ba" kallonta yake da mamaki, kafin ya sa hannu a hnkli ya karba, ya mike yace "Sae da safe Ammah" Ammah tace "da wuri hka," yace "Na gaji ne da yawa" Ammah tace "Toh Allah ya tashe mu lfya" tana fadin hka ne tana kallonsa ta ga ko xae yi ma Batuul sae da safe, ae ko tuni ya fahimci hkn, kusa da Batuul ya tafi ya dan duka yace "Sae da safe" ba karamin mamaki Batuul tayi ba, ta dago kanta dake cikin mayafi tana kallonsa, murya can kasa tace "Allah ya tashe mu lfya" ita ma tayi hkn ne sanin Ammah na jiran jin abinda xata ce ne, ssae Ammah taji ddin hkn a xuciyarta tace "Alhmdllh, tunda sun fara fahimtar juna" Abuturrab ya kuma yi ma Ammah sae da safe snn ya fice daga dakin rike da plate din abincin da Batuul ta rage.
Tun k'arfe biyar Batuul ta tashi dan dama ba isasshen bacci tayi ba, sai kuka da tayi ta yi cikin dare, tana jin k'iran Sallah ta sauk'o daga kan gadon, kayan baccin dake jikinta ta cire ta 膹aura towel, sai da tayi brush, tayi wanka tukunna tukunna ta tayi alwala, tana fitowa tasaka bak'ar abayar da ta gani cikin akwatin da Ammah tace nata ne da zatayi sallah jiya, ta saka Hijab tayi raka'atainil fajr sannan ta tada Farida tukunna tayi Sallahn asuba, bata koma ta kwanta ba har k'arfe bakwai, akwatin ta jawo ta shiga dubawa ko da kayan shafa a ciki, ganin akwai yasa ta shafa mai ta saka ta 膹an fesa turare, kwalli kawaita saka a idonta sannan ta 膹auko wani lace purple daga cikin kayan akwatin dan duk ya fisu simple, duk a sanyaye take bata da wani kuxari, 膹inkine mai kyau riga da skirt amma yayi kyau sosai, daidai yayi mata kamar dama can a jikinta aka 膹inka kayan, ta saka silver jewellery, komawa tayi kan gadon ta zauna tana tunanin y'an gidansu, wayanta ta shiga nema, tunawa tayi bata ma zo dashi ba can ta baroshi gida, idonta har ya cicciko da hawaye, zama tayi kan gadon tana ta tunane tunane, daga yau shikenan zata bar gaban iyayenta ta koma zama da wani mutum daban da ba sabawa ma tayi dashi ba, ba shiri ta shiga kuka sosai, sai da tayi mai isanta dan kanta tayi shiru dan bata ma bari Farida taji ba, haka tayi ta zama shiru ita ka膹ai, k'arfe tara Ammah ta turo k'ofan 膹akin itama har tayi wanka ta saka atamfanta mai kyau, ganin Ammah ce ta shiga gyara 膹ankwalinta kanta, a hankali ta gaida Ammah, da fara'a Ammah ta amsa mata tace "Bitti har kin tashi", kai kawai ta gya膹a ta kasa 膹agowa, Farida ce ta fito toilet 膹aure da towel, Ammah ta tace "Bitti sauk'o kiyi breakfast kinji, Farida in ta gama tazo daga baya", kasa motsawa tayi a inda take, Farida ce ta dubeta tayi murmushi tacewa Ammah "Ammah yanxu zan gama shiryawa zamu sauk'o tare", Ammah tace "Toh karki b'ata mata lokaci", daga haka ta fita, a tare suka sakko falon da Farida bayan ta gama shiryawa sae dae ta dan rufe fuskarta da mayafin jikinta, har dinning farida ta kai ta tana rike da hannunta, Ammah da Anty Amnah na xaune sae Sadeeq da Abuturrab dake rike da cup din tea yana sha a hnkli, tun da suke saukowa daga stairs yake kallonsu har suka karaso dinning din, Sadeeq yyi murmushi yace " Ina kwana Anty Amarya" dariya duk suka yi bnda Abuturrab dake ta shan tean sa, Anty Amnah tace "Toh ku xauna mana kin bar ta a tsaye Farida" kujerar dake gefen Abuturrab Farida ta ja mata tace "Xauna Batuul" Batuul bata so hka ba sae dae bbu ynda ta iya don idansu Ammah na kansu ta xauna a hnkli kan kujeran, kamshin turarensa me ddi duk ya cika ta, farida kuma ta xauna daga gefen Sadeeq. 馃挅馃æŒBATUUL馃挅馃æŒ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.