Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 61 of 124

46

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

A hargitse ta tura k'ofan 膹akin, yana kwance kan gado ya lumshe ido kamar ba shine ya shigo yanxun ba, dai dai kanshi tazo ta tsaya tana huci, ranta b'ace har wani gumi takeyi ta shiga yi masa magana, "Aliyu nifa bazan yadda da wannan abinda kuka tsira ba, wlhy ni bazan yadda da zamanta ba a cikin gidan nan, inma kai baza ka iya fa膹awa iyayenta baka son zamanta gidanka ba sai ka kama mata hostel 膹in da kanka kawae, amma ba dai tayi ta zama min a gida ba dan dama nasan munafirci ya kawota", sai da yaji tayi shiru tukunna ya bu膹e lumsassun idanunshi dake rikitata yace "tunda gidanki ne sai ki koreta", ido ta wara tana kallonshi hawaye na bin kuncinta, cikin rashin damuwa da hawayen nata yaci gaba da cewa "tsabar rashin hankali da rashin sanin ciwon kai shine ki kaje kika tsareta a kitchen kina gaya mata maganganu koh, toh duk kika yrda ta raina ki baxa ki ji da dadi ba kuma bbu ruwana baxan kuma ce mata don me ba ", hankalinta ne ya k'ara tashi wai yau ita Abu ke k'ira mara hankali akan wata can y'ar iskar, wlhy Allah sai tasan yadda tayi da Batuul, sai ta wulak'anta ta fiyeda tunaninta, k'wafa tayi ta juya a fusace ta banko mishi k'ofar 膹akin a xuciyarta tana cewa xaka rashin hankali kuwa, tabe baki yyi ya sake lumshe idanunshi ya gyara kwanciya yana shak'ar k'amshin Batuul da ya mannne mishi a kaya da yayi hugging 膹inta.

Tana fita 膹akin tayi hanyan 膹akin Batuul a fusace kamar wacce zata tashi sama, kai tsaye ta tura k'ofar 膹akin da Batuul ke ciki, tana zaune kan gadon a takure ta ha膹e kanta da guiwa, bata 膹ago kanta taga ko waye ba dan tasan shine ya dawo, ji tayi ance "tashi ki fita dan ubanki tunda ba ubanki ya gina min gidan ba", a tsorace Batuul ta 膹ago tana kallonta da mamaki shimfi膹e a fuskanta, gani tayi tana k'ara shigowa 膹akin, da sauri Batuul ta mik'e tana kallonta, inda akwatinan ta ke ajiye Ajiddeh ta nufa ta 膹auka tana watsarwa, a tsorace Batuul ta tsaya tana kallonta, hawaye ya taru a idonta, ita wane irin masifa ne wannan yake tunkarota ko kwana daya bata yi ba, hawayen dake k'ok'arin zubo mata ta maida ta sauk'o daga kan gadon tana ganin yadda Ajiddeh ke watsar da kayan tayi hanyan waje, wai wannan ma fa dan bata san matarsa bace ita, hanyan waje tayi zata fita daga 膹akin, hannu Ajiddeh tasa ta rik'ota tana cewa "ga y'ar iska na miki magana koh, toh dan ubanki kisan inda dare yayi miki dan gidana ba gidan ajiye y'an iska karuwai bane", ido Batuul ta rintse jin abunda Ajiddeh ta kirata dashi, zata iya rantsewa gaba 膹aya rayuwanta bata tab'a jin an ambaci wannan word 膹in a gidansu ba wai sai yau gashi ita ake k'ira da word 膹in, hawayen dake idontane ya shiga gangarowa, hannunta tasa ta goge fuskanta, tasa hannu ta mur膹a k'ofan zata fita, wani irin force taji Ajiddeh ta tunku膹ata dashi , ido ta rintse tana k'iran sunan Allah lkci daya ta fasa ihu tana jiran jinta a k'asa, amma ta ji akasin hka don jikin mutum ta fa膹a baya tayi zata fa膹i yayi hanzarin rikota ya rungumeta, shigewa jikinshi tayi tana boye fuskanta a kirjinsa, sai a lkcn ta fashe da kuka jikinta na rawa tsabar tsorata da tayi, kuka sosai ta shigayi tana cewa "Yaa Abu dan Allah ka maidani gida, dan Allah inaso inga Aunty, hannu yasa ya da膹a ha膹e jikinsu dan yasan tsorata tayi ba da wasa ba, neman kukan da takeyi tayi ta rasa jin kanta faffa膹an k'irjinshi, sai da yaga ta fara nutsuwa sannan ya saketa yana kallon fuskanta da hawaye ya gama wankewa, saketa yayi ya matsar da ita gefe ya zaunar da ita kan kujeran dake tsakanin 膹akunan biyu, mutuwar tsaye Ajiddeh tayi ganin Aliyu ya kare Batuul, sam ba haka taso ba, taso koda Batuul bata mutu ba ta nakasa ta in yaso iyayenta suzo su 膹auketa amma wannan jarababben ya taimakota, juyowa yayi ya shigo 膹akin yanayinshi da ta gani ne ya sata tsorata, baice mata komai ba yasa hannu ya rik'o hannayenta tana binshi a baya kamar wata doluwa yayi 膹akinshi da ita, kallonsu Batuul tayi hawaye cike idonta, ita dama tasan abin tausayi zata zama a gidan nan, duk abin nan da matarsa tayi baice mata komai ba sai ma rikota da yayi su tafi abunsu, kuka sosai ta kifa kanta kan cinyarta tanayi, sai sunan Aunty take k'ira da Baba, yana shiga 膹akinshi da ita ya sake mata hannu, magana ta fara mishi cike da masifa "wllh Aliyu yarinyar nan ta barmin gidana dan....." bai bari ta k'arasa maganan ba ya wanka mata mari lafiyayyu guda biyu, a gigice ta 膹ago kanta da idonta da ya rine yayi ja tana kallonshi, wani shegen murmushi ta saki tana hawaye tace "koh baka dakeni ba nasan karuwarka ce ko daga yadda ka rik'eta a jikinka, ni za a yiwa bariki a wani ce karatu tazo yi, munafiki kawai azzalumi, Kuma wlhy kaji na rantse sai na illatata, mugu kawai.....", wani irin fixga da yayi mata yasa ta kasa k'arasa maganan da takeyi, idonshi ya sake yin jaa, yana kallonta yace "ai ke gidan na ubankine koh, dan bakida hankali kashe y'ar mutane zakiyi xa ki hanka膹ata hka, kinsan zaki iya barin gidan nan ita ta zauna, jahila kawai wacce bata aiki da hankalinta, kika sake min shirmen nan a gidana sai na b'ata miki yadda baki zato ba, mahaukaciya jahila", yana kai wa nn ya jefar da ita ya fice daga 膹akin, inda ya barta kan kujeran nan ya dawo ya sameta sai kuka takeyi, ce mata yayi "kukan mey kike ma mutane ke kuma har ynxu", bata 膹ago ta dubeshi sai kukan da ta ci gaba dayi, cikin tsawa ranshi b'ace yace "ba magana nake yi miki ba", rinannun idanunta ta 膹ago ta kalleshi cikin sanyi hawaye nata zuba tace "Yaa Abu dan girman Allah da Annabinshi ka mayar dani wajen Aunty", hararanta yayi ya kamo hannunta, komawa tayi baya da sauri ta janye hannunta, tsayawa yayi yana kallonta yace "you thought all i was telling is lie huh, gashi nan kin fara gani tun ba aje ko ina ba, its just your first day and you have already faced soo much, sai da na fa膹a miki babu ruwanki da ita, mesa kika nemi magananta", haushi ne ya cikata ta tsananta kukanta tabi ta gefenshi zata shige 膹akin yayi saurin rik'ota, wayantane taji yana ringing, fixge hannunta tayi tayi 膹akin, bayanta yabi a hanzarce, hannu yasa ya rigata 膹aukan wayan yana kallon mai k'iran, Affan ya gani rubuce in bold da hrt emoji daga gaban, kin bata yayi har sai da wayan ta katse, batare da ya kalleta ba ya jefa wayan kan gado, tsayawa tayi tana kallonshi , Juyawa yayi yana k'arewa 膹akin kallo yadda kayanta ke zube a k'asa, ce mata yayi "da kika zauna kina yiwa mutane kuka waye zai tattare miki kayan da aka zubar garin neman fa膹anki, kinsan baki da k'arfi kika nemi tsokananta", bata ce mishi komai ba ta nemi waje ta zauna daga bakin gadon tare da janyo wayarta, dubawa tayi taga wa ya k'irata, ganin Affan ne ya sata ajiyan Zuciya, cikin kakkausar murya yace mata "ba magana nake yi miki ba, waye zai tattara miki kayan", zumb'uro bakinta tayi ta juya tana gyara zamanta kan gadon tace "Ai ba ni na zubar ba, suna zamansu ta shigo ta watsar, a k'irata ta gyara mana", da mamaki ya ke kallon yadda take mishi magana, matsowa yayi gaban gadon, da sauri ta shige cikin bargon tana cewa "nikam in ka tab'ani zan fa膹awa Ammah", ce mata yayi "tashi ki tattare kayanki", ba musu ta yaye bargon ta taso ta shiga kwashe kayan, juyawa yayi zai fita daga 膹akin, har yaje bakin k'ofa ya juyo yace "kin nemi abinda zaki cin ko kuma baki gama jan maganan ba", ganin batace mishi komai ba ya fita daga 膹akin ya barta anan

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.