Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 33 of 124
Convoy 膹in motoci sukayi shida abokanshi bayan sallar azahar har gidansu Ajiddeh, daga waje suka tsaya ya k'ira wayanta, shi yama manta da 膹azu ya b'ata mata rai, a dak'ile ta amsa wayan har yanxu ranta a b'ace, ce mata yayi "ki fa膹awa su Mum gamu nan mun iso, zamu shigo yanxu", tsaki taja tace "meye toh sai ka k'irani ne, ko gidan bak'onka ne", cire wayar yayi daga kunnenshi ya duba ya tabbatar da wacce yake magana, mayarwa yayi ya k'ara wayar a kunnenshi yace "Ajiddeh kinsan da wanda kike waya kuwa", "na sani mana , wanda ya daka min tsawa ya katse min waya akan wata Batuul....", ji tayi an warce wayan daga bayanta anyi sallama cikin natsuwa, Janaiba ce ta anshe wayan tace mishi "Aliyu har kun iso ne", bai nuna mata kamar sunyi komai da Ajiddeh ba yace "ehh muna bakin gate", tace "toh bari a zo a shigo daku", k'wafa yayi bayan sun gama wayan a ranshi yana zanyi maganin ki, bakinki bazai sake min tsaki ba, shi ba dan Ammah ma tasa shi zuwa ba wlhy da bazai zo ba, dan ya gaji da bikinma gaba 膹aya, bayan y'an mintuna aka zo aka yi musu jagora, a guest room aka sauk'esu , duk matan suna parlourn lokacin, cikin girmamawa suka gama gaishesu sannan suka sa aka shigo musu da akwatuna dozen , suka ajiye musu bandir 膹in dubu d'ai d'ai sabbi guda biyar, sannan suka yi musu sallama suka tafi akan anjima zasu zo 膹aukan amarya, daga nan sukayi hanyan gidansu Abutturab 膹in zasu gaida su Ammah, kai tsaye side 膹in Ammah yayi dasu har sama, Batuul na kwance a palon sama tana kallon e tv, bata zata ba taji sallama, gashinta a bu膹e, da hanzari tamik'e daga kan kujerar, kamin ta tashi ta rufe kanta har sun shigo, idonshi ne ya fa膹a akanta , ido hu膹u sukayi, lumshesu yayi kamar mai jin bacci tare da galla mats hararara, juyawa tayi zata bar falon Massa ya tareta "haba cutie, sai kiyi ta wani b'uya, inata nemanki ina kika shiga ne", a tak'aice tace mishi "ina nan mana, kaine baka ganni ba", taci gaba da tafiya Massa na biye da ita, waje Abutturab ya bawa sauran abokan nashi suka zauna shi kuma yaje ya cewa su Ammah sun iso, a bakin k'ofar 膹akin ya tarar da Massa ya juya zai dawo, bai kulashi ba ya bu膹e 膹akin ya shiga, a gaban madubi ya tarar da ita, cikin dakewa yace "ki dena zamawa mutane a gida kai a bu膹e kina k'ira musu aljanu, kullum za a ganki kai babu 膹an kwali", idanunta ta juya dan tasan masiface kawai yakeji da ita tak'i kulashi, ai ko juya idanun da tayi yasashi fixgota har ta kusa fa膹awa jikinshi tukunna tayi maintaining balance 膹inta ta tsaya, duk da haka tana jiyo numfashinshi a fuskanta, "did you just roll your eyes, I mean ni kika harara?", yana tambayanta fuskarsa daure, tsoro ne ya sa ta kasa ansa mishi, kiciniyar k'wace kanta ta farayi daga rik'on da yayi mata idonta taf da hawaye, janyota yayi jikinshi ta fa膹a k'irjinshi, shiru tayi a jikinshi tana jiyo bugun zuciyanshi, sun kai kusan minti biyu a haka babu wanda ya motsa daga k'arshe ta samu ta k'wace kanta ta gudu ta shige toilet ta rufe, binta yayi da ido ya kai minti uku tsaye daga baya ya juya yyi kwafa ya fice daga 膹akin, a palo ya tarar da su Yaa Mera, Aunty, Ammah, Aunty Amna da sauran Aunties 膹insu a zaune suna gaggaisawa, bayan sun gama gaisawa sukayi musu sallama suka tafi, su Ammah sukayi musu fatan komawa gidajensu lafiya, suka ha膹a musu guzuri dayawa.
Da daddare akaje 膹auko amarya, kuka sosai tayi kamin su fito kamar ba ita ke 膹aukin ayi auren ba, sosai babanta ya zaunar da ita yayi mata fa膹a, wa'azi da Nasiha sannan suka tafi, a side 膹in Ammah aka sauk'eta ita da y'an uwanta bayan su Ammah sun gama masu fatan alheri sukace akaita side 膹in Abutturab, can dare wajen k'arfe goma ya raka abokanshi ya shigo ya tarar da Batuul da Affan zaune sun rakoshi yazo yi musu sallama dan yaje gida wajen Aunty tace mishi ai tana gidansu Farida, shima fa膹a Aunty tayi mishi kan in yaje school yayi abinda ya kaishi ya maida hankali ya kula da ibadunshi don gobe zai wuce, sunsha kuka sosai, bear hug tayi mishi tace zata koma ciki dan baza ta iya ganin tafiyanshi ba, Farida taje 膹auko mishi wani abu, Abutturab ne ya shigo ganin su tare ya bisu da harara, komawa tayi daga ciki zata wuce ta corridor taji an fixgota, baki ta bu膹e zata saka ihu ya toshe mata baki da 膹ayan hannunshi, jikinta a sake yake dan bata da k'arfin yin kokawa dashi, dab da ita yake numfashinshi na bugun fuskarta, idonta da ya cika da hawaye yayi ja yake gani, lumshe idon tayi ba tare da ta bu膹e ba hawayen dake tare suka zubo, jikinshine yaji yayi sanyi , baya son ganin hawayen mace, sassauta rik'on da yayi mata yayi yace "wane moron 膹inne ya biyoki har cikin gida kike hugging 膹inshi, kasa yi mishi magana tayi dan tasan in ta bu膹e bakinta to kukane, janyota ya sakeyi yace "ba tambayanki nake ba, waye shi nace",a hankali ta bu膹e baki zata yi mishi magana ta kasa, sulalewa tayi a k'asa ta shiga rusa kuka, binta yayi ya kamota jikinshi, "mey aka miki kike kuka kuma yanxu, salon ki kuma hada ni da Ammah koh", ya fa膹a tareda 膹agota yana hararanta, cikin sark'ewar murya tace "Affan , he is going", kallonta yayi sannan yace "who is he nace?", a hankali tace "my bestfriend, cousin, everything", dubanta ya sakeyi sannan ya saketa daga rik'on, jin ya sake ta ta ruga ciki a guje tana share hawaye, kusan kwana sukayi itada Farida suna jin tafiyar Affan, kamar ance musu bazai dawo ba.
Ana gobe Abutturab da matarshi zasu tafi Batuul ta koma gida dan Ammah tace sai ta warke zata tafi, ko sau 膹aya basu tab'a magana da Batuul ba, in ta shigo wajen Ammah iyakanta tabi Batuul da harara, itakam Batuul 膹auke idonta takeyi tace kya ji dashi, ranan da ta koma gida Aunty take fa膹a mata Baba ya samo mata admission a Nile, tayi hak'uri da London university of economics 膹in, bata fa膹a mata dalili ba, ranta baiso ba amma tayi addu'an Allah yasa hakan ne yafi alkhairi, a ranan da daddare yazo yiwa su Aunty sallama shida matarshi, sai da suka fara zuwa gidansu Ajiddeh tukunna sukayi gidan su Massa, haka sukayi ta yawo, wajen sha 膹aya sukaje gidansu Batuul, tana kwance a parlour ita ka膹ai tana kallo taji bell na ringing, da mamakin waye mai buga k'ofa war haka ta tashi taje ta bu膹e, manyan idanunshi na masu kama da mai bacci ya watso mata, da sauri ta 膹auke nata idon dan wani iri takeji ganin idonshi, matsawa tayi ta basu hanya suka shiga ciki, Ajiddeh bata sanma nan bane gidansu Batuul sai da taga Abutturab 膹in ya matsa ta hango Batuul, tsaki taja itama ta shigo, hanyan sama tayi zata hau taji ya biyota a baya, sai da ta hau sama yana biye da ita tukunna ta tsaya, a dake ya ce mata "Aunty fa, i want to meet her", bata ce komai ba tayi hanyan 膹akin Aunty, tafiyan a hankali yake kallo daga baya har ta shige 膹akin, ya sauk'o k'asa, 膹akinta ta wuce bayan Aunty ta sauk'a, samun kanta tayi da tsayuwa a bakin window tana jiran taga tafiyansu, ta da膹e sosai tukunna taga sun fito, sai da taga tafiyan nasu tukunna ta fa膹a kan gadonta, bata murna kuma bata farin ciki, ta rasa gane meke damunta, washegari karfe tara jirginsu ya 膹aga suka tafi UK.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.