Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 36 of 124
Ranta b'ace ta shigo cikin gida, ignoring kowa tayi zata haura sama Aunty tace "zo nan Batuul" , dawowa tayi ta zauna daga gefe kanta a k'asa, "kikace baki sanshi ba, ya akayi yasan sunanki, har parlour ya shigo ya sameni yace min Batuul yake nema " , "Aunty nima ban san ya akayi yasan sunana ba , ni ban sanshi ba " ido Aunty ta k'ura mata da taga taqi magana tace mata "tashi kije" ranta gaba 膹aya a dagule, ta rasa mey ya hanata cewa mutumin bata sonshi, ko dan ta ganshi matured ne not like the other guys da suke binta, alwala sallah Isha tayi ta tada Sallah, tana idarwa ta kwanta, tunanin abubuwan da suka faru a yau ta rik'a yi, abinda ke damun Ammah ne ya dawo mata, mesa Yaa Abu zaiyi haka, shi ko tsoron hakkinsu baya ji gashi har yasa Ammah a damuwa matar da take very jovial and authoritative ta zama very silent just because of Abu, tsaki taja tareda juyawa 膹ayan gefenta, dama can mugu ne shi ita ta dade da sanin haka, haka taci gaba da tunane tunanenta har bacci ya 膹auketa, cikin bacci taji kamar wayarta na ringing , tashi tayi ta zauna ta duba screen 膹in wayar, sai sabuwar number ta gani, har ya katse bata 膹auka ba sai da aka sake k'iranta , 膹agawa tayi bayan tare da tace komai ba, daga 膹aya b'angaren taji ance " salamu alaiki Noor " cire wayan tayi daga kunnenta ta sakr duba number, cikin muryan bacci tace "ba Noor bace, it's a wrong number " zata ajiye wayan taji ya sake cewa "toh ai ke 膹in Haske ce shiyasa na saka miki suna Noor " , cikin kosawa da surutun da yake mata tace "who are you " , murmushi yayi daga cikin wayan har tana jiyowa yace "It's Abdallah, tunda kin kasa ganewa let me tell you, well as it is, nakasa bacci because of tunanin ki na kasa bacci " ita dai bata ce komai ba sai shiru da tayi tana sauraronshi, "baza kiyi min magana inji muryan ki mai dadi ba Noor " a hankali tace "bacci nakeji yanxu bazan iya doguwar magana ba, am sorry you should call me tomorrow " , murmushi ya sakeyi yace "Alright Noor, it's okay kiyi bacci but gobe zan kiraki kuma zakiyi min magana but for now you should go to bed , okay? " a hankali ta amsa mishi da "toh" , yace mata "good night sleep tight" ya katse wayan, mamaki ta rik'a yi mesa shi wannan mutumin baya bata haushi kamar sauran mazan dake cewa suna sonta, ganin babu mai bata amsa yasa ta kwanta ta koma bacci
B.A flight ne ya iso Nigeria K'arfe 6 na yamma, cikin mutanen dake fito fitowa daga ciki harda Abutturab da matarsa Ajiddeh, tafiya suke cike da nutsuwa, sunyi kyau sosai, kanta kwance yake kafa膹anshi gashin nan da yasha gyara an barshi iska sai ka膹awa yake , wani mutum ne yazo cikin hanzari ya karb'i Jakar dake hannun Abutturab yace "Sir this way please, the car is parked down there" bayan mutumin nan suka bi har wajen motar da zata kaisu, bayan ya bu膹e musu sun shiga sun zauna ne Ajiddeh tace "Babe, bana so muje gidanmu saboda y'an sa ido, kar aje ana cewa mun shigo gari, we should lodge in a hotel, kuma ma tunda babu wanda yasan muna hanya sai y'an gidanmu Mum da Yaa Zee kaga it will take time before a gyaggyara kuma ma ai ba da膹ewa zamuyi ba ana gama bikin nan zamu koma, so we should stay in the Hotel " gefen fuskanta ya shafa yace " alright then, hakan ma zaifi" Hotel 膹in dai suke so su sauk'a suka fa膹awa mai tukin motar, ba b'ata lokaci ya juya yayi hanyan Hotel 膹in da aka fa膹a mishi , suna isa bayan sun kama 膹aki tayi ordering abinci taci tayi wanka tasa aka turo mata driver daga gidansu, Ce mishi tayi ya tashi su tafi yace mata "No he is exhausted, bazai iya zuwa ba , amma zaije dinner " ganin kaman ranta ya fara b'aci yayi maza ya taso ya rungumeta tare da mata peck yace "baby na gaji ne yanxu; I can't come but anjima zanzo dinner da za ayi I promise, kuma zan baki what you asked for " sai a sannan ta sake fuska tace "toh zaka K'aramin akan na da" yace "yeah , everything for you " juyawa tayi ta fita daga 膹akin, da ido ya bita a ranshi yasan something is not right but ya kasa ganewa ko menene, ya rasa gane mesa baya iya yiwa Ajiddeh fa膹a akan abubuwan da takeyi , yanxu ko kayan jikinta ma bai kamata tana matar aure ta rik'a fita babu 膹an kwali ba amma bazai iya ce mata komai ba, kan gadon ya koma ya zauna tareda da dare kanshi Dan mugun Sara mishi ya fara.
[8/22, 2:01 PM] .: 馃挅馃æŒBATUUL 馃挅馃æŒ
28
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Tana fita ta wuce gidansu daga hotel din, cike gidan yake da mutane da suka zo biki, wucewa takeyi tana ta daga kai ita a dole matar mai ku膹i, matan dake zaune sai gaidata suke wasu kuma suyi gulmarta, 膹akin da tasan zata samu Mum straight ta wuce, ba ko sallama ta saka kai cikin 膹akin, Mummy na ganinta ta taso cike da murna ta rungumeta tana fa膹in "Yar albarka baki min waya kince kun iso ba " ta fadi tana K'arewa Ajiddeh kallo ganin yadda ta canja lokaci ka膹an, ga wani kyau da ta k'ara dama can Masha Allah, Hannunta ta jawo bayan ta saketa daga rungumar da tayi mata taja hannunta suka shiga bedroom, Junaiba dake zaune ce ta bisu cikin 膹akin, a tsakiya suka sa Ajiddeh, Mummy ce ta fara ce mata "Ajiddeh kinga yadda kika canja , lalalala Masha Allah, kin zama matar manya, duk komai yana tafiya yadda muka shirya ko? , Jainaba ce tayi maza ta karb'e maganan da cewa " Mummy ai ko baki tambaya ba gashi kin gani, yarinya zata cuci kanta, ana so a ayi miki abin kirki a taimakeki kina ke mijinki, kefa kina sonshi, toh da mun barki haka da yanxu duk ba haka bane, yanxu fa膹a mana muji inda matsala mu san yadda zamu b'ullowa matsalar mu magance ta" , tunda suke surutun su bata ce komai ba sai danna waya da take tayi , sai da ta gama ta 膹ago tana ka膹a hannu tace "Mummy ai Aliyu sai abinda nace, tun farkon aurenmu da ya fara min masifa kullum ni k'azama ce, na faye son jiki, bbu abinda na iya, gashi da bak'in halin jaraba sam ba a zama ayi hira dashi , amma tun bayan nayi muku complain 膹innnan da kukace in turo ku膹i , everything have been fine since then, kuma sam baya tambayan mutum mey zakayi da ku膹i komi yawansu bayarwa yakeyi shiyasa bamu samu matsala ba, maganan da nakeyi muku yanxu haka Mummy tunda mukayi aure sau 膹aya yaje gida, waya kam dama babu magana, ai na gaya muku wannan watan sun turo k'anwarshi tazo, itama 膹in dai bata da膹e ba Nasa ya maidata , wannan zuwan ma da zamuyi ban yadda mun zauna a gidanmu ba saboda Kar ma susan da zuwanmu " "Jainaba ce tace "ai hakan ma yayi daidai da kikayi, toh ya akayi da wancan abinda nace miki na abincin shi ne, wannan na naman, tunda cewa kikayi ba kya girki, ko kinyi bayaci" , dariya tasa tace "Jainaba kenan, ai in yasan wata baisan wata ba, shi yake dafawa kanshi abinci ko kuma ya siyo, toh watarana yakan ajiye na dare da safe yayi warming yaci, ni dama bana bi ta kanshi, kuma dama ba iya dafawa nayi ba, sai dai kullum in rik'a ordering don of recent ya sallami cook din gidan" , Mik'e wa tayi tana dariya tace "Mummy ,Jainaba, ku bari mu dawo daga dinner in mun nutsu zan fa膹a muku duk yadda ake ciki, ni sam ban maje naga Amarya ba, tunda aka saka ranan nan ya 膹aga mun hankali wai sai nayiwa Ufa magana ayi bikin aurenta a gidannan saboda bata sn y'an uwan mijinta su rainata " , Mummy ce tace "ai da gaskiyarta, Ina zata yadda da raini, gara da ta bar gidansu tazo nan 膹in ayi komai a gama, ko ba komai itama tana da y'an uwanta masu akwai " Da haka suka fita daga 膹akin, Mummy da Jainaba suka tsaya daga falo Ajiddeh taje side 膹in da Amarya da k'awayenta suke.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.