Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 59 of 124

Daukan Pizzan Ajiddeh tayi ta dawo palon ta zauna tareda ciro wayanta dake aljihun wandon dake jikinta, ranta gaba 膹aya a dagule yake dan tsakaninta da Allah batason Batuul da gaba 膹aya zamanta kusa da mijinta, sai da ta 膹auki slice 膹in pizza 膹aya ta faraci tukunna ta fara neman layin mummy dan a san yadda za ayi, wannan aikin nasu bai ci ba, ringing biyu mummy ta 膹aga, mummy ce ta fara magana da "ya dawon?", cikin b'acin rai Ajiddeh tace "Mummy ya dawo, babu abinda ya faru yadda muka tsara, sai ma wani masifan dake son bibiyata yanxu", cikin hanzari mummy ta katseta da cewa "ban ganeba, kina nufin asirin bai yi tasiri ba kome?, kuma masifar mey naji kina k'irawa kanki", kuka ne ya sub'ucewa Ajiddeh tace "Mummy babu wani aiki da bokan nan na Jainaba ya iya, duk k'arya yayi mana ya karb'e mana ku膹i dan yanxu haka wata matsalar ce kan ta da", Mummy tace "kece dai kikaje kikayi shirme bakibi abinda malamin yace ba, ko ba munyi dake in ya dawo ke da kanki zakije tarbarsa ba dan ki tabbata yabi takan abun", cikin sheshek'a tace "Mummy ni nace miki nasan zai dawo nema, ina kwance ya k'irani wai sun dawo kuma sai na tabbata duk komai dai", Mummy tace "toh naji, yanxu kuma matsalar mey naji kina cewa na bibiyarki, tace "Mummy sun ha膹oshi da wannan y'ar iskar mai kama da refugees 膹in Ethopia, ni tun farko ai sai da nace muku bana sonta, gashi yanxu wai a gidana zata zauna", Mummy tace "ban gane ba, wai wace yarinyace kike surutu haka akanta", tace "Mum ko ba yarinyar nan ba Batuul, dan munafirci irin nasu da baya k'arewa shine suka ha膹oshi da ita wai karatu zatayi, kuma a rasa inda zata zauna sai a gida na", Katseta tayi da cewa "nifa ban gane wa kike magana ba akai har yanxu Ajiddeh, wacece ita", tace "Mum wannan yarinyar da yazo da ita a motar da zamu dinner, bayan nan a wajen dinner ta kusa fa膹i har ya rikota, toh ita fa", mummy tace "ohhh jaraba, toh wannan duk ba matsala bane, su suka sani, mu yanxu tashi muke, indai muka samu mukayi tasiri akanshi ai mun gama da kowa da kowa, wulak'anci ka膹ai ya isheta har sai ta nemi hostel ko kuma ta koma gidan ubanta karatun, kuma ai suma da nasu gidan a can da sun sata zama ai", Ajiddeh tace "Toh mummy ni yanxu ya zanyi dashi, ni bazan iya da bak'in halin nan nashi ba, ko 膹azu inace abu yayi na kama mishi hauka ashe babu abinda yayi toh da naga a hankalinshi yake shine fa na sauk'o, wlhy bakin rai nashi daban yake, i cant take it", Mummy tayi ajiyar zuciya tace "zai bari kizo Nigeria?", kai ta girgiza kamar Mum 膹in na gabanta tace "Mummy wlhy ko giyar wake yake sha bazai barni ba, dan ni da kaina nasha fa膹a mishi ban son zuwa, ko wancan bikin da mukazo nasan da abinda na shuka shiyasa, amma da cikin nutsuwarshi yake da babu inda zamu tunda da bakina na nuna mishi bana son zuwa", Mum tace toh shikenan yanzu zamuyi magana da Jainaba sai muji yadda za ayi, duk yadda akayi zakiji a waya", tace "toh Mummy ki gaida Dad", da haka suka katse k'iran

D'aya saura ya bu膹e idonshi, ganin Ajiddeh bata nan yasan tana 膹akinta, tashi yayi ya dafa kanshi tare da sauke ajiyar xuciya at last dae ya shawo kanta ya kuma san ta hakura, mikewa yyi ya fa膹a toilet ya sakarwa kanshi shower yayi wanka yayi alwala, sai da ya fito ya canja kaya zuwa English wears, k'arfe 1:15 ya gani lokacin, yasan by now ya fara jin yunwa, 膹an tsaki yaja tunawa da yayi Ajiddeh ba iya abinci tayi ba, yanxu dole yadawo gidan da xae riqa fita yana nemawa kanshi abinci, tunawa ya sakeyi Batuul na gidan, wani xuciyar yace mishi ai sai ta riqa dafa muku, wani kuma yace mishi yarinyar nan ce zatayi maka girki, baka shirya cin abinci ba knn, 膹an tsaki yaja dan itama yanxu wata liability ce, fitowa yayi ya bu膹e 膹akin Ajiddeh don sata tayi sallah dan in ba fa膹a mata akayi ba toh ba yi zatayi ba akan kari, ganin bata nan ya fito yayi hanyan 膹akin da ya ajiye Batuul, kan gado ya sameta kwance tana bacci ta k'udundune waje 膹aya a cikin bargo. 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

45

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

K'arasawa yayi bakin gadon yasa hannu zai yaye bargon yaga small figure 膹inta na bacci peacefully a 膹an takure, kitson da aka yi mata ya rufe rabin fuskanta, d'an tabe baki yyi ya bugi gefen gadon da nufin t'ada ta amma ko motsi bata yi ba, cire bargon yyi lkci daya ta mike xaune da sauri ta shiga komawa baya ganinsa, tsaki yyi yace "Kin ma yi breakfast din kusa?" Kai ta gyada ba tare da ta kallesa ba, yace "Gud, sae ki tashi kiyi sllh ki kara komawa kitchen ki sama ma kanki lunch, don matata bata girki!" Jin bata ce komae ba ya duka kusa da ita har tana iya jiyo numfashin sa da kamshin turarensa da ya cika ta, cikin kaushin murya yace "Hope am clear?" Kai ta gyada masa tana kkrin mayar da hawayen idonta, ya juya ya fice daga dakin.

Kwance ya tadda Ajiddeh parlour, kwalin pizza duka uku a bu膹e an 膹an tab'a kowanne, sai apple a hannunta yana kallon Tv, daga gefenta ya zauna ya kamo hannunta yana kallonta yace "shine kika gudo kika barni koh babe", ba tareda ta kalleshi ba don ita kam Batuul ta tsaya mata a rai tace "ai bacci ka keyi shi yasa na dawo nn" murmushi yyi ganin ynda ta basa amsan ya mik'e yace "tashi kiyi sallah toh", dauke kai tayi kawae, kwalin da tayi littering yabi da ido ya ka膹a kai ya koma sama, yana idar da sallah ya koma gaban desktop 膹in dake 膹akinshi, bu膹ewa yayi yana dudduba sak'onnin da aka turo mishi, yawanci daga office ne sai na k'arshen ne ya gani daga Sadiq, sai da ya gama bu膹e na office 膹in tukunna ya bu膹e wanda Sadiq 膹in ya turo mishi, tsayawa yayi ya gama karanta abinda yake ciki tukunna yayiwa sauran reply sannan ya kashe ya 膹auki wayanshi ya shiga neman layin Sadiq, Sadiq na 膹auka yace "Yo bro, kun isa lafiya", Abu yace "Sallama kenan", kai Sadiq ya sosa kamar yana gabanshi yayi sallama, Abu ya amsa yace "Yeah naga ka turomin abu ta email, Sadiq yace "Ehh Abui ne yace in turo maka, acceptance letter Batuul into London University of Economics ba?", Abu yace "tun yaushe aka nema mata admission 膹in, like everything is so fast kuma tana da wannan k'ok'arin ne na karatu a can ne ma?", dariya Sadiq yasa yace "Yaa Abu dont estimate Batuul, yarinyar nada kok'ari sosai, ai sai da akayi issuing transcript 膹inta suka bata admission toh kaga they are satisfied with her perfomance", yace "Fine naji, sai anjima ka gaida gida", Sadiq yace "Okay bro, a gaidamin Batuul da sis Ajiddeh", yace "zasuji", daga nan ya katse k'iran, duk da yana son jin muryar Ammah bae kirata ba don bae son ta d'aga masa hankali da xancen Batuul.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.