Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 109 of 124

聽 聽 聽聽
聽 聽 聽 聽聽 Tana fita Allah yasa taci karo da cab, lokacin da Mum ta fito bata ganta ba drivern ta dake zaune yana jiran ta tambaya ko yaga Ajiddeh yace yaga fitanta a guje, komawa tayi ciki tayiwa Ammah gargad'in wani abin in ya samu Ajiddeh she wont take it lightly, snn ta fito suka tafi da driver, sai kalle kalle takeyi ko zataga Ajiddeh, saida sukaje gida taga cab d'in parke k'ofar gida, ta tambayeshi ko shi ya kawo Ajiddeh by description yace ehhh amma bata bashi kud'i ba kuma ta fita ba tareda bayani ba, Mum ta ciro kud'i cikin jakarta ta mik'a mishi ta koma mota driver ya k'arasa da ita cikin gida, sak'e sak'e kawai takeyi a ranta, abubuwan sun mata yawa as of this time, batasan da wanne zata fara bama, komai ya dagule mata lokaci d'aya, masu aikinta ta kwalawa kira sukazo su biyu a tare, ta tambayesu ko sunga shigowar Ajiddeh, "Ehhh ta shigo amma tayi side d'in can na gefen na Sir", Mum ta wara ido duk da tasan nan ne wajen zuwan Ajiddeh duk lokacin da ranta ya b'aci tace "Ba nan aka ajiye matar nan ba da Daddy ya mask?", sukace "Nan ne Hajiya", tace "Kuje, Keh Sadiya ki tabbata kin kai mata abinci da duk abinda zata buk'ata snn ku zauna kuna lura da ita da duk motsinta", suka amsa kai da baki suka fita, suna fita ta janyo waya ta shiga neman layin mutum d'aya da tasan lallai zai samar mata mafita

聽 聽 聽 聽聽 K'arfe hud'u Abu ya farka, har lokacin yana jin Zuciyarshi bata mishi dad'i, idonshine ya fad'a kan Batuul da yasashi jin wani sanyi cikin ranshi, ya lumshe ido ya bud'e snn ya gyara mata kwanciyarta kamin ya sauk'o da k'afafunshi a hankali dan bayason yayi motsin da zata farka ya mik'e ya shiga toilet, wanka yayi tareda yin alwala ya fito ya zira farar rigarsa ya shimfid'e abin Sallah ya hau, raka'a biyu yayi snn ya d'auko Qur'an kan shelf ya fara karantawa a nutse yadda bazai tasheta ba, saida ya karanta Rabin Suratul Tauba cikin kira'arsa mai dad'i snn ya dakata yayi addu'o'insa, jin ana k'iran Sallah ya tashi ya gabatar da raka'atanil fajr kamin ya koma kan gadon, bayason fita ya barta ita kad'ai a d'akin, shi zai jasu suyi Sallah tare , hannu yasa ya shafi gefen fuskarta a hankali ya shiga k'iran sunanta, "Fatima wake up, lokacin Sallah yayi", a hankali ta bud'e idon da ya cika da bacci snn ta mayar ta lumshesu, murmushi yayi yace "You sleep too much, Sleepy head", tashi kiyi Sallah, its time", sai a lokacin taji mey yake fad'i, zuciyantane ya fara pounding tunawa da jiya da tayi, words d'innan na ringing cikin kanta, sake rintse ido tayi ta kasa bud'ewa, tsoron bud'e ido takeyi kar daren jiya ya zame mata mafarki, She have longed to hear someone say he love her, duk da ba sani tayi tana son nashi ba bataso wannan karon da ta samu taji ya zama mafarki, "Fatima", sulalewa tayi daga jikinshi tace "Toh kayi nima zanyi nawa anjima", mamakinta ne ya cikashi ganin taqi bud'e ido amma tana magana yace " Fatima Open your eyes", kamar baza ta bud'e ba a hankali ta bud'esu ta sauk'esu kanshi, cak ya d'auketa yayi toilet da ita, ya zaunar bakin bathtub d'in, brush d'inshi ya samata toothpaste ya mik'o mata, turo baki tayi ta ansa ta shiga wanke bakinta, tana gamawa ya jawo kan shower ya shiga tsiyaya mata ruwan, saida ta gama alwalan snn ya sake d'aukarta cak ya fito da ita ya saka mata dogon Hijab d'inta dake ninke gefe, saida suka idar yace "Tashi kiyi rak'atainil fajr", mik'ewa rayi ta jero raka'a biyu snn ta bishi suka ci gaba da addu'a, Hannu yasa jikinta yaji temperature d'inta yace "Good morning", kallonshi tayi taga murmushi shimfid'e fuskarshi, bata tab'a ji ya gaidata ba sai yau, kuma from his look its sincere, a hankali cikin jin kunya tace "ina kwana", ya rik'o hannunta yace "Baki amsa min ba", sunkuyar da kai tayi batace komai ba, "How you feeling right now?, kinajin wani ciwo?", kai ta girgiza mishi tace "Am fine", ya sauk'e ajiyar zuciya yace "Mai idon bacci, go back and sleep", mik'ewa tayi ta cire Hijabin ta ninke zata koma gadon taji ya rik'o mata hannu, yace "Hey, My princess, I couldn't say Hi to her", juyar da kai tayi tayi murmushi snn ta dake ta kalleshi tace "Its not like I care" ta k'wace hannunta ta koma kan gado, yayi dariya yace "Really?, well her Papa cares, Say Hi to her for me pls and tell her that Papa Loves her so much ", murmushi tayi ta shige cikin bargo tanajin kamar moment d'innan yayi ta zama haka, kada komai ya canja mata, cikin baccinta taji an rungumeta ta baya, gyara kwanciyarta tayi suka koma bacci, k'arfe goma ya farka itama ya tasheta, wanka ta farayi snn ya k'ira Farida a waya ta kawo mata kaya ta saka, bacci ma takeyi kasancewar yau weekend, idonta cikeda bacci ta taso ta kawo mata kayan, sai wani irin kallo take bin Batuul dashi tana dariya k'asa k'asa, Hararta Batuul tayi ta anshi kayanta tace "Kyaji dashi dai", bakin gadon ta zauna tace "Keh ni mey nace miki toh, kawai dan nayi dariya", Abu ya fito daga toilet, ya kalleta yace "kayan fa?", nuni tayi mishi dasu tace "gasu nan", yace "zaman na meye toh?", ta zumb'uro baki ta mik'e zata fita tace "Ammah tace ince muku breakfast is ready" kallonta kawai yayi ta fice Batuul na murmurshi, suna gama shirayawa ya rik'ota hannunta suka fito, tun tana qi har ta hakura, suna sauk'a downstairs ta fakaici idonshi ta warce hannunta tayi gaba abinta, kowa na kan dinning su biyune basa nan, Ammah da Abui da Sadiq ta gaida sukayi mata ya k'arfin jiki, a kunyace ta amsa da Alhamdulillah snn ya ja mata kujera ta zauna sukayi breakfast tare

Da yamma suna zaune itada Farida a main parlour, kamar daga sama ta jiyo muryar su Ahmad, rabonta da jin muryarsu watanni kenan in ba a waya ba, da wani irin murna ta tashi t isa inda take jiyo muryar, da gudu ta isa ta rungumeshi hawaye na k'ok'arin zubowa idonta ganin duka kannenta a gabanta, d'aya bayan y'ata ta dinga rungumarsu snn ta karb'i Aabid dake hannun Sayyid tayi pecking d'inshi, sam ya manta da ita sai kallonta yake kamar yaga sabon mutum, jiki a sanyaye ta kallesu tace "Aunty fa?, batace zata zo bako?", Ahmad ya dubeta yace "ita tace muxo, zasu zo tareda Baba su dubaki wai", kai kawai ta gyad'a tana k'ok'arin maida hawayenta da bataso su gani tace "Ku shiga ku zauna, duk kunyi wani tsayi, Sayyid gashin meye haka ka tara kanka kamr wani black cotton?", dariya kawai ya mata ya sunkuyar da kanshi suka karaso ciki, Farida ta d'auki Hafiz tace "muje ka rakani sweet boy", basu jima ba ta sauk'o tareda Ammah, Ammah tace "Ashe manya bak'i ke tafe bamu sani ba, ya kuka baro gida, Ya Auntyn Ku?", Duk suka gaisheta snn suka amsa mata da tana lafiya, nan tasa aka cika musu gabansu da kayan abinci iri iri, suna nan zaune Abu da Sadiq suka shigo a tare, tausayinta yaji ganin yanda take farin ciki ganin yaran, bama yadda take yiwa Aabid wasa ba, ya k'araso wajenta batareda tasan ya shigo ba ya sunkuya daidai kunnenta yace "Hey am happy to see you happy", a d'an tsorace ta juyo ta dubeshi tayi mirmushi tace "Thank you", ya girgiza mata kai yace "You look cute holding the baby, can't wait to see you babysitting my princess", wara ido tayi tana kallon koda wanda yaji, ganin babu mai kallonsu ta sauk'e ajiyar Zuciya ta d'an bugeshi cikin wasa, dariya yayi ya mik'e ya anshi Aabid hannunta yana cakud'a mishi gashi yace "Hey Champ", dariya Aabid yayi mishi cute dimples d'inshi na appearing, da maamki ta bishi da kallo, gaba d'aya ba shine Abutturab d'in da ta sani ba months back, murmushi kawai tayi tana jin wani farin ciki a ranta da takeson ya d'ore a haka,d'aya bayan yaran suka gaisheshi yana amsawa, ya kalllesu yace "Maybe we should go out for ice cream ko, Movie or anything? am offering the treat, who wants to join?", Yusra da kamar jira take tace "Ni zanje, muje Blue cabana, they got the best ice cream and Chapman, yafi na ko ina and their Kebab, omg its so yummy, kasan ko Aunty sai ince mata akaini weekends wai saitace saidai a siyomin, am happy you are taking me.....", bata k'arsa ba Khalil ya sakar mata da wani harara, shiru tayi zata koma ta zauna ganin an harareta Abutturab da tunda ta fara magana yake murmushi ya kamo hannunta yace "Then you will get us all in munje ko" kai ta kad'a mishi, Batuul da mamaki take kallonta ganin yanda yarinyar ta k'ara tsayi, Abu yayi dariya yace ku fad'awa Ammah we are going tunda yamma tayi, Farida ta mik'e tareda Batuul zasuje su shirya, Abu yace "Farida ki sauk'o mata da Hijab in kinje sama", kallonshi tayi idonta yayi rau rau har hawaye ya ciko jin yace a kawo mata Hijab ta dawo kusa dashi a hankali tace "Hijab kuma?, dashi zanje?", ya kad'a kai yana wasa da Aabid ba tareda ya kalleta ba yace "Yeah, anything?", matsawa tayi daga kusa dashi ta zumb'uro baki ta zauna kan sofa, Farida ta sauk'o tareda Amamh riqeda Hijab d'in Batuul ita kuma ta d'aura veil kan cape top da skirt d'in dake jikinta, ta mik'awa Batuul hijab din, duk suka mik'e Ammah tayi musu Allah ya kiyaye sai sun dawo, Batuul ce kad'ai bata tashi ba tana fushin da babu wanda ya lura da ita, Ammah ce tace "Bitti tashi ki bisu kema ki warware jikinki kinji, zaman gidan ai babu dad'i, tashi kije", batason yiwa Ammah musu, mike we a tayi ta zura Hijab d'inta ta fita, koda taje k'in shiga motar Abu tayi dukda taga ya bud'e mata front seat, zagayawa tayi ta shiga ta Sadiq tayi zamanta batareda ta kalleshi ba, baima lura da Fishin da takeyi ba, bayan kowa ya shiga yaja mota suka fita tasu Sadiq ta biyosu a baya.
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.