Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 38 of 124
Tafiya sukeyi babu wanda yace da wani komai, Abutturab ne ya 膹ago ya dubi Sadiq yace "Farida ma last month taje wajena ai, amma kai ko sau 膹aya baka nemana ko? " wani siririn dariya Sadiq yayi, yasan yayanshi is feeling guilty of himself shiyasa baisanma mey zaice ba, Sadiq yace "No Yaa Abu, abubuwa ne sukayi min yawa, ga hidiman Ammah, Abui da kuma na wasu shiyasa, amma in kuka koma har can zanzo , In shaa Allah" , jikin Abu ne ya kuma yin sanyi yace "Allah ya yadda " a ranshi yana tunanin mey zai fara cewa su Ammah, sai yanxu yake sake ganin rashin kyautuwar abinda yayi, a haka suka isa gida suna hira jefi jefi, a k'ofar gida Sadiq ya tsai da motar tare da yiwa masu gadin horn, da sauri saurinsu suka taso suka bu膹e, ba K'aramin mamaki sukayi ba ganin Abutturab, da sauri suka fa膹a膹a fara'arsu suna "Alhaji K'arami sannu da zuwa , an sha hanya to ya iyali , fitowa yayi daga motan ya mik'a musu hannu suka gaisa , sai murnan dawowanshi suke dan yana da kyauta sosai duk rashin dariyarsa, wucewa Sadiq yayi tukunna Abutturab yabi bayanshi, a hankali yasa kai cikin falon har wani fa膹uwa gabanshi yakeyi, Farida ce ta fito daga kitchen da tray a hannun ta, to abin ka da jini batasan lokacin data ajiye trayn ba tazo da gudu ta rungume shi ba, har da hawaye a idonta bayan ta sassauta rik'on da tayi mishi ta kalleshi tace "Yaa Abu ashe za kazo, Dan Allah kana zuwa gun mu kaji" Janyota ya sakeyi jikinshi yace zan rik'a zuwa kullum kinji Autan Abui" Dariya tasa ta goge guntun hawayen dake idonta tace "yawwa Yaa Abu, gidanmu babu da膹i da baka nan, gaba 膹aya abinda yayi mata da taje wajenshi last month ya rik'a tunawa, sae yaji bai kyauta ba, duk rashin shirin su da Farida amma cikin k'annenshi yafi sonta, haka itama tafi sonshi, masifanshi ne kawai bataso, juyawa tayi tace "bari in kira Ammah ya Abuu tana daki" k'asa cewa komae yyi sae bin ta da kallo da yyi, dai dai nn Ammah ta shiga sakkowa daga stairs. 馃挅馃æŒBATUUL 馃挅馃æŒ
29
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Dawowa yayi yabi stairs 膹in da kallo, da sauri ya 膹auke idonshi daga wajen dan bazai iya kallon Ammah ba , falon k'asa tazo ta zauna ba tare da ta kalli inda Abutturab yake ba, jikinshi ne ya k'ara yin sanyi har sai da Sadiq ya lura dafa kafa膹anshi yace mishi "it will be okay, just pray and be optimistic, a hankali ya 膹aga k'afanshi kamar k'afan na mishi ciwo, har cikin falon shima ya k'arasa, ya samu waje a k'asa ya zauna 膹an nesa da Ammah, cikin sanyin murya yace mata "Ammah ina wuni " ba tareda ta kalleshi ba a tak'aice tace "lafiya" daga hka yyi shiru don ya rasa abun cewa, Abui ne ya shigo daga waje, da sauri Abutturab ya mike ya isa wajen Abui, cikeda girmamawa yace "Abui barka da gajiya, sannu da dawowa gida " , kallon mamaki Abui ya shiga yi masa daga sama xuwa k'asa snn a takaice yace "sannu na gode , ashe ka shigo gari " inji Abui yana me dubansa har lkcn, Kai Abutturab ya gya膹a tareda cewa "Ehhh Abui, 膹azu na shigo " , yace "madallah toh yayi kyau " , bai sake bi ta kanshi ba yayi hanyan stairs, Ammah ce ta tashi tabi bayanshi suka haura tare tana mishi sannu da dawowa gida, Juayawa yayi ya dubi Sadiq a sanyaye , kai Sadiq ya girgiza mishi alamar assuringly, kamar yasa ihu haka ya rik'a ji a wajen, idonshi ne yaji yana kawo hawaye, tambayan kanshi ya fara "mesa na zama haka ne? , akwae randa su Ammah xa su ki murnan ganina bayan tsawon watanni, yana cikin tunanin yaji wayanshi na ringing, hawayen dake idonshi yayi maza ya goge ya ciro wayar daga aljihu, sunan da yayiwa Ajiddeh saving ya gani a screen 膹in, sai da ya kusa katsewa tukunna yayi receiving yasa a kunne, Sadiq kam juyawa yayi ya bar wajen, jiki a sanyaye yace "Hello" , "Aliyu wai meye haka ne, har yanxu baka fito ba wai , tun 膹azu fa nake zaman jiranka, daga cewa kaje gidanku yanxu zaka dawo shine zaka zauna ka shanya ni, ni da ina nan ma Wllh bazan bari ka tafi ba, kuma Hotel 膹in kake son naje ni ka膹ai?" wani irin tsawa da ya daka mata ne ya sata yin shiru ba shiri, gaba 膹aya jikinta sai da ya 膹au rawa har gumi sai da ya tsatsaffo mata a goshinta , "bana son rashin hankali kina Jina ko, kin manta inda nace miki zanje ne, gidan iyayena naje kuma da kike cewa ke ka膹ai zaki kwana a hotel yau kika fara kwana a hotel ke ka膹ai ne , kuma ba dawowa zanyi ba so kar ki koma hotel 膹innan ki wuce gidanku ki kwana a can" gaba 膹aya ta tsorata dashi, a hankali ta bu膹i baki tace "toh sai da safe" , wani iska mai zafi ya furzar daga bakinshi ya maida wayar aljihu, 膹akin shi ya nufa, tsaf 膹akin yake kamar yadda ya tafi ya barshi , babu abunda aka canja sai 膹an k'uran da yayi, sai da yayi karka膹e k'uran tukunna yayi wanka ya kwanta, gaba 膹aya bacci ya k'aurace mishi, sai yanxu abubuwan da yayi suka fara tariyo mishi, sai yanxu yake sake ganin rashin kyautuwar abinda yayi wa iyayensa, kusan kwana yayi yana tunani, ganin babu abunda tunani zai mishi ne yasa ya mik'e yaje ya 膹auro alwala ya fara Nafila, haka ya kwana yana addu'a yana rok'on Allah ya huci zuciyar su Ammah, yana zaune kan sallaya har aka k'ira sallah asuba, Tashi yayi ya tafi masallaci, a nan ya ha膹u da Sadiq da Abui, tunda Abui ya amsa gaisuwan shi bai sake ce mishi komai ba, ba K'aramin tashi hankalinshi ya da膹a yi ba, babu abunda yak'i irin ganin b'acin ran iyayenshi, Sadiq ne yaci gaba da kwantar mishi da hankali har suka shiga gida kowa yayi 膹akinshi, zaman jiran gari ya waye yayi yaje ya samu Ammah, yasan in Ammah ta hak'ura toh Abui bashi da matsala, bakwai saura ya kasa hak'ura ya tashi yayi 膹akin Ammah, yasan bata bacci war haka, yafi minti uku tsaye bakin k'ofar 膹aki ya kasa shiga, a hankali yayi knocking k'ofar 膹akin, muryan Ammah yaji tace bismillah, a hankali ya tura k'ofar 膹akin ya shigo, Ammah na zaune daga bakin gado casbah a hannunta, da sallama ya shigo kanshi a k'asa ya zauna dab da k'afanta , cikin sanyin murya yace "Ammah Nda wattu" sai da ta 膹auki seconds ba tare da kallon inda yake ba ta amsa mishi da "Lafiya" hankalinshi ne ya sake tashi yasan Ammah ba K'aramin fushi tayi ba , ko da wasa bata so tayiwa mutum kanuri yayi mata hausa, amma gashi yau ita da kanta tayi mishi hausa, shiru yayi ya rasa mey zaice can da yaga shirun baya zuwa ko ina yace "Ammah Dan Allah kuyi hakuri, wlhy ban san meye ya yazo kaina ba , Ina sha Allah bazan sakeyi ba, ku yafe min pls " cikin kanuri yyi mata maganar, duk maganan da yakeyi ko sau 膹aya bata juyo ta dubeshi, jiki a sanyaye ya sake matsawa kusa da k'afanta yace "Ammah fishinki na 膹aga mun hankali fiyeda komai, nayi alk'awarin hakan bazai sake faruwa, kuyi hakuri ku yafe min, fishinku a kaina na Janyo min fishin ubangijina, Am so sorry Ammah " , Hannunta yaje ya rik'a cikin nashi cikin sark'e war murya yace "Ammah kiyi min aikin gafara ko zan samu kwanciyar hankali, Ammah nasan na b'ata muku ......" , bata bari ya k'arasa ba ta Janye hannunta daga rik'on da yayiwa hannunta tace mishi " hakurin mey kake bani wai, ni nace maka kayi min laifi ne, I thought you did what you think is right ko, then you should let me be ka dena damuna da hakuri, bance kayi min komai ba", kanshi ya kifa a cin y'anta ya fashe da kuka yana girgiza kai, ya kai 1min kwance kai bata 膹aga shi ba, tausayin dan nata ya cikata don tasan of course ba yin kansa bne, ta sa hannu a hankali ta 膹auke kanshi daga cinyarta tace "you can go, am okay bakayi min komai ba , rasa mey ya ke mishi da膹i yayi ya dubeta da idonshi da suka rine sukayi ja yace 'Ammah pls forgive me, am promising you it won't happen again, Ni gaba 膹aya garin ma bazan sake bari ba, I will resign daga aiki a can, you should forgive me Ammah " ce mishi tayi "Aliyu tashi kaje, bana so kazo kana damuna kaji , you should leave " , kallonta yayi zai sake magana tace " I said leave", jiki ba k'wari ya mik'e ya fita, da ido tabi bayanshi cike da tausayin 膹an nata, waje ya fita daga 膹akin kanshi na Sara mishi, 膹akinshi ya koma ya kwanta ya runtse ido hawaye na bin kun cin shi, wayar ya Janyo yayi receiving saboda K'aran da take, a kunnenshi ya saka tareda yin shiru, Ajiddeh ce tayi magana daga 膹aya b'angaren tace "Aliyu har yanxu baza ka dawo ba , yaufa zamu wuce, kuma ma....." katseta yayi yace "Look here free me, in baza ki iya zama ba toh ni kinga rabu dani, you should just go back am busy over here, xa ki iya tafiyar ki" ya katse wayan, hankalinta yafi na kullum tashi, shikenan ta shiga uku ta dinga nanatawa ta fa膹a kan kujera, baya fitowa daga 膹akin sai in zai zo bawa Ammah da Abui hakuri amma duk da haka babu progress, hka yyi ta neman fuskar iyayen nasa amma bae samu ba, Farida da Sadiq ne ke shigowa wajenshi suna tausanshi tareda bashi baki, ranan kwana uku da yaje ya samu Abui, a ranan Abba ya nuna masa komae ya wuce ya hak'ura, murna fal cikin ransa ya fita tareda yiwa Abui alk'awarin hakan bazai sake faruwa ba, Ammah kam har yanxu tak'i hakuri tana nan kan bakanta
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.