Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 101 of 124

Aunty Amna dake tsaye tana magana ta hango Abu rik'e da Batuul suna sauk'owa downstairs, juyawa tayi ta dubi Ammah snn ta juya tayi stairs d'in, tana zuwa ta rungumo Batuul jikinta tace "Ayyyyy Batuul Habibty, bakiji dad'i ba ashe, Allahumma yashfiki, Allah yasa Kaffara ne Allah ya k'ara miki lafiya, baiwar Allah kina zamanki mutane na binki da sharri, kiyita Addu'a kinji, In sha Allahu duk wani mugun nufinsu akanki bazai tabbata ba da izini Allah", murmushi Batuul tayi tana tunanin maganganun da Aunty Amna ta gama fad'a mata yanzu, ita bata gane ma zancen mey takeyi ba", lumshe ido tayi ta bud'e snn tace "Namafa ji sauki Alhamdulillah Anty", Aunty Amna tace "Zaki warke kinji, Allah ya rabaki da sharrin masharranta", daidai nan Ajiddeh ta fito d'akin Abu zata sauk'o down stairs itama, jin maganan da Aunty Amna keyi yasa ta kasa d'aga k'afarta kuma, ta tsaya tana kallonsu, Aunty Amna ta dubi Abutturab da ya had'e rai tace "kai kuma yarinya batada lafiya kaje ka ajiyeta baka fadawa mutane ba", hannun Batuul ya janye ya dawo da ita gabanshi yace "Bata fa jin dad'i, she is weak", wara ido Aunty Amna tayi tace "Iyye, kaji mara kunya, da kasan she is weak ka barta tana shan wuya a can, kai a dole mai mata ko, ai sai ka kinkimeta tunda she is weak" sunkuyar da kai Batuul tayi dan kunya, kamar jira yakeyi ko sai gani sukayi yasa hannayenshi duka biyu zai d'auketa, wara ido Batuul tayi tareda matsawa baya tana girgiza mishi kai alamun kar ya mata haka, kamar bai gane mey take nufi ba ya sa hannu ya kamota zai d'agata taji kamar ana kulle mata ciki ta fasa wani razanannen k'ara da yafi na ko yaushe had'e ta rike cikin tana kiran Anty da kyar, lkci daya ta sulale yayi maza ya bita ya kamata a rikice yace "Ya salam, Not again baby, you will get well soon", Aunty Amna da ta tsaya kallon tsiyar Abutturab a tsorace da jin karan ta tsuguna itama ta kamo Batuul duk ta rud'e tace "Abu ciwon nata ne", kasa bata amsa yayi sai d'aukarta da yayi cak yayi k'asa da ita yana k'iran sunan Ammah, Ajiddeh da ke tsaye har lokacin tana kallonsu idonta ciccike da hawaye ta kasa d'aga k'afarta, ta rasa me ke mata dadi a duniylar, ganin yayi k'asa da Batuul ta fashe da kuka ta koma d'akin da take da sauri, a rikice Ammah ta fito tana tambayan mey ya faru, Farida da Sadiq dake side d'in Abui tare suka fito suna tambayan mey ya faru, Aunty Amna ma na tambayarshi ko ciwon nata amma ya kasa ce mata komai sai sunan Ammah da yake k'ira yana girgiza Batuul d'in ta tashi, Gaba daya duk sun rud'e kowa ya rasa abinda zaiyi ganin jikin Batuul d'in duk ya saki, Farida na kuka tace "Ammah ni kam nace ku kaita wajen Dr Zakaa zai dubata ya fad'a mana abinda ke damunta," hawayen dake idonta ta goge tace "Sadiq Abui na Guest room tareda bak'onshi, kace ciwon nata ya dawo", a rud'e Sadiq d'in ya amsa ya fita amsa aiken da Ammah ta mishi, da k'yar Ammah tayi k'arfin hali ta kamo Abun dake riqe da Batuul ya kasa cewa komai tace "Babana kawota ka kwantar da ita, zataji sauk'i In sha Allah, yanzu za ayi mata magani", ta fad'a tana k'ok'arin karb'an Batuul daga hannunshi, girgiza kanshi yakeyi hawaye na gangarowa idonshi, zama yayi kan kujerar Batuul na rungume jikinshi, gefenshi Ammah ta dawo ta zauna zatayi magana kenan Abui yayi sallama shida Ashiekh da Sadiq, Abui yace "Subhanallahi, jikin nata ne kenan", Abu bai iya cewa komai va don shi kadai yasan mey yakeji cikin ranshi, bayason kowa ya tab'ata sbd fargaban abinda za a ce mishi ya biyo baya, bayajin ko d'aya daga cikin nerves da pulses d'in jikinta na aiki, Ammah ce ta kawo hannunta ta rik'o na Batuul d'in, gabanta ne ya rik'a fad'i ganin hannun Batuul d'in ya saki, d'agowa tayi tana kallom Abu da idanunshi suka kad'a, lumshe ido yayi snn ya bud'e yace "Ammah babu abinda ya sameta ko?, I know she will be alright, nasani Fatima zakiji sauk'i i know you won't leave me just like that isn't it Batuul, you have to get up", Aunty Amna Abui ya kalla yayi mata alamun taja Farida da Ammah da ta matsa baya tana girgiza Kai, hakan ko tayi ta kama hannun Ammah tace "Ammah zataji sauk'i fa, ba dama haka yakeyi mata ba, yanzun nan zata farfad'o, muje muyi mata addu'an samun sauk'i", Itama Aunty Amna k'arfin hali kawai takeyi gaba d'aya jikinta yayi sanyi sai hawaye da takeyi, Farida ce ta karb'e hannunta daga rik'on da Aunty Amna tayi mata ta dawo gaban Abu ta tsuguna dab fuskar Batuul d'in tana kallonsa hawaye na sakko mata tace "Yaaa Abu saida nace maka a kaita asibiti fa, don Allah mu tafi", ta kalli Abui dake tsaye ta mike ta isa kusa da shi cikin kuka tace "Abui don Allah nace mu kaita asibiti da yanzu ta warke, ka ganta yanxu kwance ko motsi batayi, Dan Allah muje a kaita", Hannu Abui ya d'aura kanta ya shafa snn yace "Babu abinda ya sameta kinji, zataji sauki" yacewa Sadiq " *Sadiq tai sha samiro Leno*, Sadiq kamata ka kaita sama", tana girgiza kai tana kuka haka Sadiq ya jata yayi sama da ita ya rage daga Abui sai Abu dake riqe da Batuul snn Asheikh, Asheik ya dubi Abui yace "Alanguro akwai Zamzam a kusa?" Abui yace "Ehh bari a d'auko",
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

85

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Cikeda masifarta take kallonshi, shiko karasowa yayi hannunshi cikin aljihun wandonshi yace "Sit!, magana zamuyi", kallonshi ta tsaya yi a tsagere kamin ta zauna ganin duk ya canja mata kamar ba Idrees d'in dake shakkarta da gudun b'acin ranta ba, wanda in ta fad'i abu jiki na rawa zai d'auki maganan, had'e rai tayi ta dake tace "Wai kai yanzu sabida tsabar wulakanci kan wadannan tsinannun kayan naka kasa na taso na baro muhimman abubuwan da nakeyi a Abuja na taho Lagos?, toh wlhy yanzu maza maza ka kwashe tsiyarka kuma gyaran ma ni ba irin wannan nace maka inaso ba ai", ba yabo ba fallasa ya fara magan yace "Tun baki san kayan mene ba kike wannan b'ab'atun, toh kaya dai nakine in baki sonsu ki zubar dan haka al'ada yace min kuma itama d'in haka nayi mata", katseshi tayi da hannu tace "Kayi wa uwar wa irin wadannan kayan, dan cin mutunci irin naka ma ba ni kadai kayiwa wadannan kayan ba harda had'ani da banzaye, nasan bazai wuce wad'annan masu kafar sauron bane da ke yawo a cikin gari kayi mana tare dasu, nasha fada maka ka dena had'ani da wadannan matsiyatan kana mana kaya tare......", bata rufe baki ba sai ji tayi yace "Aure zanyi next week, Kayan fad'ar kishiya ne gashinan snn wannan yawon naki daka yau kin barshi kenan, in har badaa izinina kika fita ba toh koma inane kikajeshi karki dawo min gida, kiyi zamanki a can", brain d'inta ne ya dena functioning for a minute, kamar a planet Neptune take jinta sbd yadda taji tana yawo saman iska, komai na juya mata, ido kawai ta zuba tana kallonshi har saida hankalinta ya dawo snn ta miqe tana cire duk wani abu dake kanta dan ji takeyi sun mata nauyi, takowa tayi tazo gabanshi tana mishi wani mugun kallo tace "Kace meye?, Aure?, Idrees ashe ko lallai zaka tafka babban kuskure na rayuwanka da baka taba yi ba wlhy, tun wuri ka gyara maganarka, kai d'in banza har ka isa tozartani kayi min kishiya?, wlhy Allah baka isa ba, bamu gaji ayi mana kishiya ba, You had better take back your words tun muna mu biyu da kai kamin duniya ta jimu, kai ka ma isa kayi aure, toh duk munafikan da suka saka yi dan ganin bayana sunyi kad'an, Ka koma kace musu ta Allah ba tasu ba ni nafi karfinsu, ai babu mai yimin wannan tijarar ni nasani inba wannan tsohuwar da ka ajiye can gida ba", Tasss ya d'auketa da mari da yasa hawayen dake idonta ya shiga zubowa, mik'ewaKame tayi cikin zafin rai ta cakumo rigarshi tana "Wlhy sai kasan ka mareni, munafiki kawai maci amana, azzalumi, wlhy ba ni ka wulakanta ba sai tsohuwar banzar da ko tafiya batayi daka ajiye a gida, kwace rigarsa da ta cukwuikuye yayi daga hannunta snn ya kara mata wasu lafiyayyun marin, cikeda fushi ya shiga bugunta ko ta ina, duka yakeyi tana ihu tana zage_zage, duka yayi mata sosai har saida yaga ta jikata snn ya jefar da ita yayi yace "Keh kinyi kad'an, nan gaba koda wasa kika kuma zagar min Family sai nasa kinyi regretting, keh d'in har wata matar kirki ce da baza ayiwa kishiya ba?, mey kika iya a auren da har zai hanani yi miki kishiya kullum in kika fice kika bar gari sai lokacin da kika ga dama kike dawowa, wane mijin ne zai yadda matarsa take irin wannan shashancin, Y'ay'an da kika haifa da kansu basu san dad'in uwarsu ba, basu taba samun time d'inki, I have finally made my decision, aure ne nan da sati biyu zanyi shi" ya tsallaketa yayi ficewarsa daga d'akin amma har lokacin bakinta bai mutu ba sai zazzaga rashin mutunci takeyi, da k'yar ta iya samu ta mik'e ta janyo jakarta ta ciro wayarta daga ciki, tana kuka ta shiga neman layin wayar Mummy, bugu d'aya ta d'aga daga d'aya b'angaren tace "Wai uwar mey ya miki da ya uzzura miki da dawowa, jarababbe", Jainaba ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Nikam na shiga uku, Yaya kasheni yakeson yi", Mummy tace "Kasheki? Dan uwarsa shi ya haifake da zai kasheki, shege matsiyaci", Jainaba na sheshek'a tace "Yaya wai aure zaiyi shine ya kirani harda kayan fad'ar kishiya", Mummy ta buga k'irji ta miqe tsaye tace "Ni Zuwaira, Jainab Bakal Abuki, da hankalinki kike kiramin mijinki aure zaiyi?", Jainaba na kuka ta gama fayyacewa Mummy gaskiya da karyar abinda ya faru, Mum tasa salati, nan ta rarrashi Jainaba akan zasu nemo maganin matsalar snn suyi maganinshi, daga nn sukaci gaba da zaginshi da yadda za aci uban nashi daga nan sukayi sallama

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.