Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 50 of 124

Har gida Abui yasa sukaje shida Baba da Uncle 膹in Abutturab da yaji lbrn Abdallah ke neman sonta suka samu iyayen Abdallah suka bashi hak'uri, Basu nuna komai ba suka ce dama wani ai baya auren matar wani, dama can Allah yayi ba matarsa bace, suka musu add'uan Allah ya bawa Batuul da Abutturab zaman lafiya, kuma sukace zasu bawa Abdallah hak'uri su bashi baki, da haka sukayi musu godiya suka tafi.

Ranar asabar k'arfe goma aka 膹aura auren Aliyu Ahmad Kyaree da Fatima Kashim Goni akan sadaki sisin gwal 60, a k'ofar gidan kakanta dake Goni Mukhtar street a Maiduguri, tana kwance 膹akin Aunty babu abunda takeyi sai rawar sanyi, Yayya ce ta shigo tana cewa "Keh Batuul fito ai an 膹aura, tashi daga kan gadon nan tun jiya kike kai, maza fito a ida miki kitson da kike ta gudu tun jiya", kan gado ta hau ta yaye mata bargon, hawaye ta gani idonta, sai rawar sanyi take, hannu tasa zata 膹agota taji jikinta zafi, ba shiri ta janye hannunta, Farida ce ta turo k'ofan ta shigo janye da wani akwati, ganin Yayya kan gadon yasa ta tambayan mey ya faru, da gudu ta k'araso ganin yadda Batuul 膹in take yasa ta fita a guje taje ta k'ira Aunty, a rikice Aunty ta shigo, da kanta tayi k'ok'arin 膹ago Batuul sannan ta nemi key ta mik'awa Farida tace suje dan su Ahmad na Maiduguri 膹aurin aure kuma batasan ma ina driver 膹insu yake ba, mutanen dake gidan ne suka tashi ganin yanayin jikin Batuul suna tambayan mey ya faru, babu wanda ya iya basu amsa dan Yayya da kanta ma kuka take tana k'iran sunan Batuul 膹in, ikon Allah ne kawai ya kaisu asibitin dan gaba 膹ayanta Faridan ta rikice, suna isa asibitin aka taso aka karb'i Batuul akayi emergency da ita, Yayya duk ta ishi mutane da kuka wiwi a asibitin, Anty kam xama tayi reception ta jinginar da kanta jikin kujera, da ganinta kasan hankalinta a tashe yake, farida ce tayi karfin halin kiransu Ammah ta sanar da su halin da ake ciki, kan kace me sae ga Ammah da Anty Amnah sun taho asibitin, sae bayan kusan minti talatin likita da nurse uku suka fito daga emergency ward, likitan ya bukaci Anty ta bi sa office sanin da yyi ita ce Mahaifiyar Batuul, jiki a sanyaye Anty ta shiga office din likitan, likitan ya dauki farin gilashinsa ya sa yana kallonta yace "Gskya Madam 'yar ki na cikin wani yanayi, a daina daga mata hankali don Allah, dab take da kamuwa da hawan jini" hawaye cike idon Anty tace "Ya jikin nata Dr?" Yace "Da sauki, ta samu bacci ynxu, sae dae meyasa baxa ku tuhumeta ku ji damuwar ta ba Hajiya?" Anty ta share hawayen idonta tace "Xa muyi hkn Dr, mun gode," yace "Gud!" Tace "xan iya shiga in ganta Dr?" Yace "Xa ki iya, amma kada a tada ta" mikewa tayi ta kuma yi masa gdya ta fita, bacci me nauyi ta tarar Batuul na yi an sa mata drip, su Ammah ma duk suka shiga suka dubata, ganin bacci take duk hankalinsu ya kwanta, sae a snn suka iya barin asibitin, Farida ta maida Yayya ma gida don sae gyangyadi take a asibitin, Anty bata kira baba ta sanar da shi halin da ake ciki ba sanin suna Maiduguri har lkcn, Karfe sha biyu kiransa ya shigo wayarta ta daga, nn yake gaya mata sun sauka Abuja lfya, sae a snn ta sanar da shi halin da Batuul ke ciki, hankalinsa ya tashi ssae, ya sanar ma Abui daga airport suka nufo asibitin. Karfe daya saura Abuturrab ya shigo gida duk a gajiye ga damuwa da yyi masa yawa bae san ynda xae yi da Ajiddeh ba idan ta ji xancen auren nn, sa'arsa daya bbu wanda ya sani cikin 'yan uwanta, tun da aka daura auren gabansa ke faduwa ya ji kmr an daura masa abu me nauyi ne a kai, part din Abui ya nufa direct don Avoidin mutane dake cike gidan, ko minti biyar bae yi da kwanciya ba Ammah ta shigo, ya mike xaune ya gaisheta yace "Mun dawo Ammah" murmushi tayi ta xauna gefensa tace "Toh Allah ya taya ka riko babana, sae dae fa Batuul din na asibiti ya kamata ka je dubata ynxu duk da nasan yhu are tired" yace "Asibiti kuma Ammah, me ya sameta?" Ammah tace "Kai dae ka je ka dubata, Allah dae ya bata lfya" a hnkli yace "Toh," Ammah ta mike, yace "Ammah ki ce Sadeeq ya kawo min makullin mota" fridge ta nufa ta bude ta dauko chill yoghurt ta mika masa tace "Gashi ka sha Abuu, nasan baka ci komae ba yau" karba yyi yace "Nagode Ammah" ta juya ta fita tana cewa bari in dauko maka makullin, ajiye yoghurt din yyi don bae jin xae iya sha. Driving kawae yake amma gaba daya hankalinsa baya jikinsa, a hka ya iso asibitin, Ahmad ya hadu da a haraban asibitin, Ahmad ya gaishesa da ladabi snn ya kai sa har ward din da Batuul take, Wata Sistern Anty ce xaune ward din, don Anty ita ta koma gida sbda baki, har lkcn Batuul bacci take, Abuturrab ya gaida Anty Hafsat, ta amsa masa da fara'a tana tsokanansa don sun saba, murmushi kawae yake kansa a kasa, har dae ta tashi ta tace masa tana xuwa ta fita, Ahmad ta bi bayanta. Ya dde tsaye yana kallonta snn ya ja kujera ya xauna, ya kusa minti talatin xaune ya ga tana juye juye, ya kafa mata ido ko kiftawa bae yi, a raxane ta mike xaune ta bude ido tana kwala wa Anty kira tana kkrin sauka daga kan gadon, ya Mike da sauri ya riketa, hkn bae hanata ci gaba da kiran antyn da take ba tana kuka xata sauko, ko kadan bata lura da wanda ke rike da ita ba don idonta rufe yake, rungumeta yyi jikinsa, lkci daya ta daina fixge fixgen da take tayi lamo jikinsa tana sauke ajiyar xuciya, lumshe ido yyi yaki budewa. 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

39

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Sunfi minti biyar a haka, har lokacin idonshi lumshe, hannu ya sa yana kwantar da dogon gashin kanta da aka kitse rabi aka bar rabi, k'amshin turaren da ya cikata ne yasa ta tunanin inda tasan turaren, a hankali ta bu膹e ido tana k'ok'arin janyewa daga jikinshi, saketa yayi ya 膹an matsa da baya, idonta cike da hawaye ta juya tana k'arewa 膹akin da take kallo, ganin shi ka膹ai ne 膹akin yasa ta matsa can k'arshen gadon ta fashe da wani matsanancin kuka, sosai take kuka tana k'iran Aunty, tsayawa yayi yana kallonta, can ya k'arasa inda take ya ha膹e rai yace "Wai kukan mey kike yi ma mutane hka, baki ga inda kike bane or did yhu want to worsen yhu condition, tunda na dawo nake sintirin asibiti, am even wondering anya ke ba sicker bace, da ko tawa ta sameni" ko kallonsa bata yi ba ta shiga kkrin sauk'a daga saman gadon zata fita daga 膹akin tana kuka, yayi maza ya fixgota, baya tayi zata fa膹i yasa hannu ya taro ta ya maido ta k'irjinshi, 膹ago kanta yayi har lkcn tana kuka yace "Allah zan mareki in baki nutsu ba, mey ke damunki da zaki rik'a abu kamar yarinya, are yhu okay!" kai ta girgiza mishi ta 膹ago rinannun idanunta ta sauk'e kan kyakyawan fuskanshi cikin sheshek'an kuka tace "Yaa Abuu wai an 膹aura ko, tunda baka sona bana son ka dan Allah ka taimakamin kacewa su Baba su barni a nan inyi zamana, in kayimin haka nima Zan yadda da duk wani condition 膹inka ko na meye ne, ko kuma zanyi zamana ba tareda da kowa ya sani ba sai ka saken......", bai bari ta k'arasa maganan ba ya k'ara k'arfin rik'on da yayi mata ya daka mata tsawa yana mata mugun kallo yace "Da alama baki da hankali, sae ynxu kika san da hka, C'mon wuce kije ki kwanta", ssae ta tsorata ganin yanayinshi, tana hawaye ta juya tayi kan gadon, sai da ta koma ta kwanta tukunna ya juya ya danna bell 膹in k'iran doctor.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.