Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 18 of 124

Gidansu Massa Abutturab yaje, sai da ya fara shiga cikin gida , Maman Massa ya tarar zagaye da mutane a falonta da ma'aikatan gidan, gaishe shi suka farayi tun daga bakin k'ofa, k'arasa yayi ya tsuguna dab da k'afanta yace mata "Yaa Mera nda dubdo"(ina wuni Yaa Mera), kanshi ta shafa tace "Baanyi wushe" (lafiya Babana), ya shirye shiye", shi ya manta ma gaba 膹aya da aurenshi nan da sati uku, sai da ya tuno shirye shiryen mey take nufi sannan yace "Alhamdulillah Yaa", "Masha Allah" tace sannan ya mik'e yace "bari in duba Massa Yaa", tace "toh Babana, sai ka fito", mik'ewa yayi ya tafi chamber Massa, tura k'ofar 膹akin yayi ya shiga tare da sallama, su biyu ya gani a zaune suna playing game a tv, tsakin sallamar shi da basu amsa ba yayi, inda socket 膹in 膹akin yake ya wuce directly ya kashe, tsayawa sukayi suna kallonshi da mamakin yaushe ya shigo, Massa ne yace mishi "Man final tournament fa muke bugawa ka kashe", bai ce mishi komai ba sai da ya samu waje a kan gado ya zauna sannan yace "sai kace yara kun rik'e controller kuna ta game, nayi sallama babu wanda yayi responding a cikinku" ya sake jan k'aramin tsaki, a tare mazan Massa da 膹ayan suka dubi juna suka sa dariya, dubansu yayi yaga dariyan mey sukeyi sannan yace musu "abin yi ne baku da" ya ciro wayanshi daga Aljihu, 膹ayan ne ya koma daga gefen Abutturab yace mishi "ai gaskiya ka fa膹a, mu yara ne sosai ma, kai da zaka zama ango next few weeks ai kam ka zama babba", harara Abutturab ya jefa mishi yace " kuyi mana kuma auren, kun zauna kuna abun yara har ana yin sallama bakwa ji", Massa ne ya dubi wanda ke gefen Abutturab yace mishi "Abba fa膹a mishi ai jira muke manya su fara yi sai mu bisu a baya", dariya ma suka bashi yace "Ku kuka sani, mu munyi gaba", haka suka ci gaba da hira suna tsokananshi, sai 10:30 ya tuna da su Farida, mik'ewa yayi cikin hanzari yace "shit", binshi sukayi da ido suna so ya gaya musu abunda ya faru, kallonsu yayi yaga duk shi suke kallo , ce musu yayi "wlhy su Farida na kai wajen prom kuma nace by ten ya kamata in je na manta", Massa ne yayi maza yace "yawwa i wanted to ask you that girl, k'awar Farida ce ko, she is damn pretty, she is so densed, she is ....." , bai k'arasa ba Abutturab yace mishi "Hey meye hakan, k'awar Farida ce fa, yarinya ce fa kake cewa she is so densed, yarinyar da bata fi sixteen yrs ba", da ido suka bishi ganin bai tab'a shiga maganan y'an matansu ba, fita yayi daga 膹akin bai ce musu komai ba

A Tulip bistro yaje yayi parking, wayanshi ya 膹auko yayi dialing number Farida ba a 膹auka ba, sai da ya k'ira wajen sau goma ba a 膹auka ba, bu膹e k'ofan motan yayi ya fita daga ciki ya shiga cikin hall 膹in, fuska a tamke ya shiga hall 膹in ya tarar ana ta hayaniya, Farida ya hango a kan stage ita da wasu friends 膹insu suna zazzaune a zagaye sunyi round suna playing truth or dare, rasa ya zai yi ya k'irata yayi dan ko yayi ihu ma baza taji ba, Batuul ya hango daga gefe ta zaune ita ka膹ai a kan kujera da awards a kan table 膹in da take tana danna waya, deciding yayi kawai yaje yayi mata magana ta k'ira Farida su tafi, inda take ya k'arasa ya sunkuyo daidai kunnenta zai yi mata magana dan yasan ba lallai taji ba in ya tsaya yi mata maganan kuma bayason su b'ata mishi lokaci,k'anshin turaren da taji ne ya sata saurin 膹agowa , heart beat 膹inta ya k'aru, waigowa tayi da sauri suka kusa cin karo, zata mik'e ya sa hannu ya maida ta, tsayawa tayi tana kallonshi a tsorace, shima fuskanta ya tsaya kallo yadda lights 膹in ke haska stones 膹in jikinta sai ya k'ara mata kyau, lkci daya kuma ya hade rae, hannunta ta motsa alamar ya sake mata, sake mata hannunta yayi yace mata "Go and call your friend , ina jiranku a waje", juyawa yayi ya fita daga hall 膹in, mik'ewa tayi bayan ya fita jiki a sanyaye ta isa inda Farida take tace mata "Yaa Abu na jiranmu a waje", fita Batuul tayi bayan tayi sallama da mutane ta isa inda motar ke pake, shiga tayi ta zauna daga baya, ta 膹ago idonta kenan zata ce mishi Farida na fitowa suka ha膹a ido hu膹u ta mirror, maza tayi ta 膹auke nata tace mishi "tana fitowa" a hankali, Tare da Affan Farida suka fito kamar ka su rabu, sallama sukayi ta shige gaba dan horn 膹in da Abu ya danna, direct gida ya wuce dasu, suna shiga gida suka wuce 膹akin Ammah suka ga tayi bacci, a hankali suka jawo mata k'ofan suka wuce nasu, kayan jikinsu suka cire sukayi wanka, sukayi sallah isha, bayan sun 膹anyi hiran event 膹in yau suka kwanta bacci

THREE WEEKS LATER
A firgice Batuul ta tashi daga baccin da take tana ambaton sunan Allah..... 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

17

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

THREE WEEKS LATER

A firgice Batuul ta tashi daga baccin da take tana ambaton sunan Allah(a uzu bikalimatillahi tammat, min sharri ma khalaq, bismillahi llazi la ya dduru ma'as mihi shay'un fil ard wa la fis sama'i wa huwal aliyul azim), zama tayi akan gadonta, gumin da ya tsatsaffo a fuskanta ta sa hannu ta goge, mamakin irin mafarkin da tayi yau tayi, tasan mafarkanta na tsoro basa wuce macizai amma na yau daban ne, mik'ewa tayi tabi hanyan toilet ta shiga, ruwa ta watsa tare alwala ta fito, hijab 膹inta ta 膹auka ta saka sannan ta shimfi膹a abun sallah ta hau ta fara nafilfili, bayan ta idar sosai tayi addu'a Allah ya kare ta daga sharrin abun ji da na gani sannan ta 膹auko Quraninta daga kan bedside drawer ta karanta, sai da ta gama karanta suratul Anbiya' da Hajj sannan ta duba agogo taga k'arfe biyar, zama tayi a kan abin sallah ta ci gaba da addu'o inta har aka tada sallah a masallaci ta mik'e tayi raka'ataynil fajr ,tayi sallah asuba, tana idarwa tayi azkars 膹inta na safe sannan ta mik'e ta cire dogon hijab 膹in dake jikinta ta ninke shi tare da abun sallah ta maidasu inda ta 膹aukosu, gadonta ta koma ta kwanta, sai da tayi addu'a dan ta tsorata 膹azu sosai sannan ta ja bargon ta rufe jikinta dashi ta kwanta, bata tashi ba sai sha biyu saura, ta mik'e taje tayi wanka ta saka wani riga da skirt k'arami mai kyau bata 膹aura 膹ank kwalin kayan ba sai hula kawaj da ta saka a kanta, k'asa ta sauk'o bayan ta gama shafa mai, babu kowa a gidan, a ranta tace mayb mazan sun tafi ball ko tennis 膹insu na jaraba, Aunty da Yusra kuma na gidan biki, sai da taci abinci sannan ta koma palo ta 膹au remote ta canja favorite tashar ta star plus, mik'ewa tayi ta koma sama dubo wayanta, missed calls uku ta gani, 膹aya na Aunty biyu na Farida, Aunty ta fara k'ira, tana 膹auka tace "Hello Batuul, mun fito kina bacci, ki shirya a kawoki gidan bikin , Farida ma na ta tambayanki", sai da Aunty ta gama tace "Aunty kaina ke ciwo tun da na tashi, bana son zuwa saboda hayaniya", da damu Aunty ta ce mata "kinsha magani Batuul", "eh", tace sannan ta ce mata "ki kula da kanki sai mun dawo, zan k'ira su Janet a waya in fa膹a musu suna dubaki sannan suka katse wayan", suna gamawa tayi dialing number Farida, Farida na 膹auka tace "wane irin bacci kikeyi haka har na k'ira twice bakiyi picking ba", ce mata tayi "wayan fa yana 膹aki ni kuma ina k'asa, toh meye ma na k'irana da sassafe , ke da ake hidima a gidanku", "ai hidiman ne ya sani k'iranki, wlhy gidan ya cika da mutane , babu da膹i, am coming over to your place", kamin Batuul ta sake magana ta katse wayan,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.