Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 20 of 124
18
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Tsayawa tayi tana juye juye in zata bi, kawai deciding tayi da ta fara sallama ko zai jiyota inma a ciki yake, sallama tayi ta yi taji ba ba a amsa ba, lalube ta fara ko zata switch 膹in 膹akin har ta gama lalubenta bata ga komai ba, deciding tayi toh ta k'ira sunanshi ko zai amsa, "Massa" ,shiru tayi tana jira taji ko za a amsa amma taji shiru, sau uku tana k'iran sunan taji ba a amsa ba kawai ta juya zata fita ta ga kamar mutum na kwance a kan seater, k'arasawa tayi wajen seater ta tsaya ta tabbatar mutum ne kwance a kai, broad figure 膹inshi na kwance peacefully amma bata ganin fuskanahi dan ya juya mata baya, sake k'iran sunan tayi taji bai amsa ba, deciding tayi ta tab'a shi tunda baccin nashi ya kai har haka nauyi, hannu ta sa a goshinshi taji wani 膹umi da laushi, maza tayi zata 膹auke hannunta taji wani hannu mai laushi da fa膹i a kan nata, wani abu ne taji gaba 膹aya yabi jikinta ga heartbeat 膹in ya fara aikin nashi kamar mai shirin fitowa, idonta ya cika da hawaye tab saura k'iris ya zubo, tsayawa tayi still a wajen ta kasa ko da k'wak'waren numfashi, juyowa yayi ya jawota ta kusa fa膹awa kanshi tayi hanzari ta dafa kujerar, wayanshi ya 膹auko daga gefenshi, flash light ya kunna ya haska yaga ko wacece, idonta ta rintse da ya haska flash light 膹in a fuskanta, hawayen da ya taru a idon ne ya silalo ta ido 膹aya, tsayawa yayi yana kallon cute face 膹inta , k'aramin lips 膹inta idonshi ya sauk'a akai, yadda hawayen ya gangaro har kan cute lips 膹in yabi da ido, ita dai tana tsaye ta kasa motsi, idon ma bata bu膹e shi ba dan bata san ma ko waye bane, tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna har lokacin bai sake mata hannu ba, sai da ya zauna ya fara mamakin, ya akayi tazo gidannan, kuma mey ma ya kawota har 膹akin nan, k'ara janyo hannunta yayi , a lokacin ta bu膹e idonta, wara idon tayi ganin wanda ke rik'e da hannunta a gabanta, ihu ta bu膹e baki zata kurma yayi maza ya toshe bakinta, ce mata yayi "shut up, and tell me y you are here" tare da fixgo ta ta k'arasa gabanshi, sai da yaga kyarman da jikinta keyi ya ragu sannan ya sake mata baki da hannu, mik'ewa yayi ya isa wani waje ya kunna wutan 膹akin, gaba 膹ayanta ya duba tun daga kai har k'asa sannan ya koma ya zauna a kujerar da ya tashi, tambayanta ya sakeyi, "mey kike yi a 膹akin nan har kika zo kina tab'a ni", kasa magana tayi dan gaba 膹aya ta tsorata da ganinshi, tsawa ya daka mata "yace ba magana nake miki ba kinyi shiru kina kallo na, sai da ta tuna da sunan wacce ta aikotan sannan jiki a sanyaye tace mishi "Yaa mera ce tace in zo nan chamber in k'ira mata Massa, i didnt know inace kaine Massa, kuma 膹akin ne da duhu shine nace bari in tashe shi, kayi hak'uri", gaba 膹aya ta gama tsorata da ganinshi, juyawa tayi zata tafi yayi maza ypa fixgota, ce mata yayi "tab'a min fuskan kuma na meye", "innalillahi wa inna illaihi rajiun ta ambata a zuciyanta, ba ta fa膹a mishi tashin Massan zatayi bane kuma da duhu ita bata san ma fuska bane, cikin dakewa tace "膹akin ne da duhu, ban san fuskan ka bane" ta warce hannunta daga ruk'on da yayi mata tayi ta fita daga 膹akin a guje, sunanta ya k'ira amma ko sauraronshi bata yi ba tayi tafiyarta, ranshi ne yayi mugun b'acin k'in amsawa da tayi, tashi yayi ya shiga toilet dake bedroom zaiyi wanka
Sai da ta iso k'ofar 膹akin sannan ta tsaya ta daidaita numfashinta, ganin ta samu nutsuwa ya sata tura k'ofan 膹akin a hankali, da sallama ta shiga ta zauna sannan tace "Yaa Mera , Massan baya nan" kamar kar ta fa膹a mata taga Abu sai kuma tace "amma naga Yaa Abu a 膹akin yana bacci", jin ance Abutturab na 膹akin yasa ta cewa "ohh shi yana gida, toh dama ai dan shi nake neman Massan, yau zasuyi wushe wushen ko?", ta tambayi Batuul, 膹ago kai Batuul tayi tana dubawa ko wani ake tambaya, da ta ga babu kowa a 膹akin sai ita ya tabbatar mata da ita Yaa Mera ke magana, " No, ni ban sani ba fa Yaa, bansan mey zasuyi yau ba, sai dai in Farida ta shigo mu tambayeta" inji Batuul, Yaa Mera ce ta sake cewa "ai tunda ma yana gidan bari in k'irashi yazo in ganshi muyi magana dashi", mamakin matar takeyi kamar ba sarauniya ba, babu ruwanta, ita ko bayi ma bata ajiyewa kusa da ita gata da fara'a, ga kyau, kammansu 膹aya da Ammah, Abutturab 膹inma dasu yayi kama, hasken sune kawai bai 膹auko ba sai yayi duhun Abui, su Farida da Sadiq ne sukayi kama da Abui amma suka 膹auko hasken Ammah, tana zaune tana ta zancen zuci Farida ta shigo da plate 膹in kisre da miyar kuka da yaji kaji, gefen Batuul taje ta zauna ta cewa Yaa Mera "Yaa sun iya kisren sosai, kamar fa da engine sukeyi , ya burgeni yadda sukeyi shiyasa ma na 膹ebo ka膹an, Batuul ci kiji", Yaa Mera ce tace "shiyasa mamanku tace sai anan za ayi, yanxu ma daga nan za a kwasa akai gidansu matar Abun", ido Farida ta wara tace "Yaa drums dayawa fa akayi, kuma duka za a kai musu, wannan matar ta Yaa Abu suna yi bada wasa ba", dariya ta bawa Yaa Mera tace mata "al'adanmu kenan Farida, haka mukeyi in zamu aurar da yara", cewa Farida tayi "lallai, su suka sani", taci gaba da cin abincinta, lura tayi da Batuul bata ci tace "meye kika sani gaba, kici mana", harara Batuul tabita dashi tayi magana a hankali yadda Yaa Mera baza taji ba "ce miki nayi inajin yunwa, ki gama mu tafi ni", Yaa Mera ce ta 膹agi taga Batuul 膹in bata cin kisren, ce mata tayi "Batuul bitti, beri bei" (Batuul y'ata, kici abinci), a hankali ta amsa da "toh", sannan ma matso tasa hannu a cikin plate 膹in
Yana fitowa daga toilet 膹in bayan yayi wanka da alwalar la'asar, wayanshi ya 膹aga ya k'ira Massa, yana 膹agawa yace mishi " Kana inane", Massa ne ya amsa da "muna tare dasu Imran a Protea, ya kan naka, yayi sauk'i", ce mishi yayi "Yeah sosai, ina jiranka kazo ka 膹aukeni", sannan ya katse k'iran, kaya ya saka cikin sabbin kayanshi da suke gidan da ya 膹inka na biki, bayan ya gama ne yayi sallah la'asar, yana idarwa wayarshi tayi k'ara, 膹auka yayi yasa a kunne, "salamu alaikum, Yaa Mera nda dubdo", ehh ina gida, toh bari in sauk'o sannan ya katse wayan", sosai yayi kyau da kaftan 膹in da ya saka, ya 膹aura hula akanshi sannan ya fita, side 膹in Yaa Mera yayi, da shiga ya samu waje ya zauna ya sake gaisheta, Farida ma gaisheshi tayi , bayan ya amsa ne Yaa Mera ta dubeshi tace "yau ne wushe wushen naku ko", kai ya gya膹a tare da amsa mata da "ehh", ce mishi tayi "wane time za ayi?", "k'arfe bakwai ne zuwa sha 膹aya", "toh yanxu kace musu su shiryata k'arfe biyar, anan za ayi mata k茅la tul kamin ku wuce wajen wushe wushen, zamu tura musu mota, daga nan zamu kaita wajen, har kaya zamu bata ta saka, mun gama magana da mamanka", cewa yayi "okay Yaa, In sha Allah zan fa膹a mata, sai ta fa膹a a gidan nasu" , sallama yayi da ita ya mik'e kenan zai yi hanyan waje yaga an bu膹e wani k'ofa, k'ofan yabi da kallo, Batuul ce ta fito daga ciki hannunta rik'e da hand napkin tana gogewa, ta cire gyalen dake yafe akanta 膹azu sai hular kawai, idonta dake kan abinda ke hannunta ta 膹ago suka yi ido hu膹u, wani irin abu taji gaba 膹ayanta, shima tsayawa yayi kallonta, idonta ta 膹auke daga kanshi shima yayi k'wafa ya fita daga 膹akin
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.