Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 40 of 124
Bayan anyi sallahn Isha Abui ya shigo gida, dama Ammah duk ta matsu ya dawo ta fa膹a mishi abinda ke ranta, bayan ya dawo saida ya sauk'o palon k'asa tukunna Ammah ta kawo mishi abincinshi har palon, sai da tayi serving 膹inshi yana ci tukunna ta fara magana, shima dama ya lura da magana a bakinta, cewa tayi "Abul Aliyu", 膹agowa yayi bayan ya cinye spoon 膹in abinci da ya saka a bakinshi yace "Na'am Umm Aliyu", ya tsaya yana kallonta yana jiran yaji mey zatace, sai da tyi ajiyan zuciya tukunna tace "dama wani shawara nayi 膽azu akan yaran nan namu, kuma ina ganin its beneficial to both families, mey zai hana mu nemawa Abutturab auren yarinyan nan Batuul, yarinyar nutsatsiyace sosai kuma gidan da ta fito nan aka fara yiwa Abutturab tarbiya, a gidan ya fara koyon komai na rayuwanshi, kuma ko babu komai in suna tare a can , toh nasan lallai zata na watching moves 膹inshi dan tana da lura da sanin ya kamata, xa kuma tana nuna masa what's right nd wrong, gata kuma da hankali, kaga inma shi ya tafi yaqi dawowa toh ita ba yadda zatayi tayi ta zama babu ganin gida dole sai ta dawo, toh ,kaga a haka zai biyota su dawo ko dan kunyanmu", tunda ta fara magana ya maida spoon 膹in abincin cikin plate 膹in, murmushi 膹auke a fuskanshi yace "Masha Allah, wannan ai abin farin ciki ne sosai kuma nima zanfi kowa murnan ganin wannan al'amari ya faru, kamar Farida haka nake jin Batuul a raina, gobe in Allah ya kaimu zanje in tuntub'i mahaifinta akan zancen muji in babu matsala ko kuma da akwai wanda takeso ", Ammah tace"Abul Aliyu in sun yadda ma kawai a 膹aura auren su tafi in yaso daga baya ayi biki , sai taci gaba da karatunta a can,", yace "okay duk zanyi trying inji, Allah dai ya taimaka" haka dai sukayi ta zancen ha膹a Abutturab da Batuul aure har Ammah na cewa ai da tun farko ma sunyi tunanin nan da duk yanxu basa cikin matsala
Washe gari ranan juma'a bayan an idar da Sallah a masallaci Abui ya ha膹u da Baba, bayan sun gaisa Baba yace "Alhaji mu dai bama tab'a ha膹uwa dan kanmu sai dai ko masallaci ko kuma meeting",dariya Abui yayi yace "rayuwan kenan Alhaji, in mukace zamu zauna gida abin bazai yi kyau ba, da shike ma yanxu girma yazo, mun kusa sauk'a mu huta ai", duk su biyun suka sa dariya, Abui ne yacewa Baba " *Alai wa office lan g猫rezain, dai fatoro iske k猫la kwamnyen* , Alai ana jirana office yanxu, amma anjima zanzo gida, there is this issue i want to discuss with you", da haka sukayi sallama, da yamma wajen k'arfe biyar Abui na tashi daga office yayi gidansu Batuul ko gida bai je ba, lokacin Baba na gida saboda its a short day duk sun tashi aiki da wuri, fitowan Batuul kenan daga backyard 膽in gidansu, tayi mamakin ganin Abui a gidansu, har k'asa taje ta tsuguna ta gaisheshi sannan ta tashi da taje tayi serving 膹insu drinks da snacks, bayan ta ajiye zata mik'e Abui yake tamabayanta ya makaranta, tace Alhmdllh, nn yayi ta sa mata albarka har sai da taji kunyanshi sosai , bayan ta tafine Abui ya fara magana , sai da ya gama baynin abinda ya kawoshi tukunna Baba ya fa'da'da murmushin fuskarsa yace "Alai nidai b'angarena babu matsala dan babu abinda zaka nema matsawar inada iko akan abun in hanaka, kuma ma ai Abutturab yaron kirki ne sosai, dama dai akwai wani yaro da naga ya fara zuwa wajenta tun wancan watan amma bansan ko sunyi maganan aure ba, kuma tunda ga na gida da aka san halinshi ai yafi da a bawa na waje da ba'a san halinshi ba, dan ma dai naga yaron nada hankali amma zamu bashi hak'uri, yanzu dai ni zanje inyi shawara da y'an uwana da manya na sai mu san abin yi dan Yayya ma ta matsa tafi kowa son a aurar da Batuul sai gashi Allah ya taimakeni akai", godiya sosai Abui yayiwa Baba daga nan suka shiga hirar politics da matsalolin dake damun Nigeria.
Batuul na kwance kan gado wajen k'arfe 8 na dare bayan tayi sallah isha, kayan bacci ne jikinta dogon wando da y'ar riga, kan gadon duk ta baje takaddu sai Macbook 膹inta daga gefe, chocolate bowl ta janyo ta 膹au twix 膹aya ta b'are ta jefa a bakinta tukunna taci gaba da duba takaddan, tana ci taji wayanta na ringing, tashi tayi ta ciro wayan daga caji, Recieving tayi tareda komawa kan gadon ta kwanta, kamin tayi magana daga 膹aya b'angaren akayi sallama tareda da fa膹in "Ranki ya da膹e Habibty, i cant imagine life without you", murmushi tayi har ana jiyo sautin daga 膹aya b'angaren tace "tareda naka, you can live normally mana tunda ai da can ma baka sanni ba and you were living", dariya yasa yace "that was then, amma ai yanzu tunda na sanki, life is gonna be hard without you, promise you wont leave me", ji tayi gaba 膹aya ya gama bata tausayi, ita tasan ba sonshi takeba but tana respecting 膹inshi sosai, avoiding promise 膹in da yace tayi mishi tayi tace "Ya jikin Mummy, ta k'ara samun sauk'i ko?", da sauri ya tareta yace "Ba kinqi zuwa in kaiki wajenta ba, kullum sai ta tambayeni yaushe zan kawo mata kene, har banaso tana tambayana dan bansan mey zance mata ya hanaki zuwa ba", kai ta girgiza kamar yana gabanta tace "No fa ba naqi zuwa bane, we have time , kuma i dont think its right muje gidanku tun yanzu , i will come when its time", tambayanta yayi mey takeyi dan yaga mind 膽inta is not with him, tace mishi assignment takeyi, da haka ya barta tace they will talk ltr
Bayan Abui ya tafi, Aunty ce ta sauk'o k'asa ta sami Baba zaune yana kallon CNN channel, daga gefenshi ta samu waje ta Zauna tayi mishi sannu da gajiya tareda ajiye. abinda ke hannunta, volume ya rage ya juyo ya dubeta ya fa膹a mata yadda sukayi da Abui, ita gaba 膹aya bata expecting haka, ta k'asa daina kallon mai gidan nata, hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba jin xancen Baba kuma tasan babu yadda za ayi yaqi bawa Abutturab Batuul tunda har gida Babanshi yazo nema mishi aurenta, ajiyan zuciya tayi cike da damuwa tace "Uncle Batuul 膹in kuma, shi da yayi aure ko shekara bai wuce ba, ai sai ya bari ko matar tasa in ta haihu ne sai ya fara zancen k'arin aure amma ba daga aure ya bijiro da sabo ba", ta fa膹a tana jiran jin mey Baba zaice, cewa yayi "indai zai kula dasu duka biyu ai bamu da matsala, kuma ai ba sanin matsalarshi mukayi ba na son k'ara aure, kuma ma dai yaron nan 膹anki ne, kinfi kowa sanin halinshi, ya kamata kifi kowa murnan kasancewar wannan al'amari, kinsan ko shekaran jiya kina zaune kina ji sai da Yayya ta k'irani akan Batuul, toh yanxu mafitar addu'an da nayi na samu, nasan Aliyu yaron kirki ne zai kula da Batuul in sha Allah", ido kawai Aunty ta zubawa Baba yana magana hankalinta na da膽a tashi, Batuul tayi yarinya da auren mai mata, barema irin su Ajiddeh, cutan Batuul kawai za ayi indai ta zauna a gidan nan a matsayin matar Abutturab, dan tasan yadda familyn Ajiddeh suke akan kishiya, mik'ewa kawai tayi ba tareda ta sake cewa komai ba ta haura sama don bata jin xata amince da wnn batun at all, idonta ya ka膹a har ya canja kala. 馃挅馃æŒBATUUL馃挅馃æŒ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.