Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 77 of 124

62

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Jawota yayi ya d'aura ta kan cinyarsa yasa hannayenshi cikin towel d'in dake jikinta, numfashinta ne taji yana neman d'aukewa jin hannayenshi a k'ugunta, kuka ta saka sosai tace "Yaaa Abuuu dagaske ban sani ba, kayi hak'uri
ka barni", dariya ta bashi ya sake janyota jikinshi ya d'aura bakinshi kunnenta, cikin rad'a yace mata "then, shine zan nuna miki abinda take nufi", girgiza kai ta shiga yi tana hawaye, bata ankara ba sai ji tayi ya juyo da ita tana fuskantarsa, rintse ido tayi dan bata iya kallon idonshi, jikinta sae rawa yake, cikin wani irin murya da taji har cikin ranta yace "open your eyes", sake rintse su tayi kamar abinda yace tayi kenan, a hankali ya sunkuyo yayi kissing idon nata d'aya, wani irin shock taji yabi jikinta, sake rintsewa tayi hawayen na dad'a silalowa, d'agowa yayi yana kallon yadda jikinta ke shivering, kirjinta sai heaving yake, murmushi yayi ya sunkuya ya sake kissing d'ayan, nan ma shivering jikinta ya dinga yi, d'agowa yayi ya sake kallon k'aramin pink lips d'inta da hawaye ya jik'a, har lokacin hannunshi bai bar cikin towel dinta ba, sunkuyawa ya kuma yi yayi brushing lips d'inshi kan nata, a tsorace ta bud'e ido tayi 'yar kara dan ita yanzu Yaa Abu ya fara bata tsoro, murmushi yayi ganin ta bud'e ido don dama haka yake so, lips d'inshi ya maida kan nata ya shiga yi mata wani deep kiss, wani irin ajiyar zuciya ta sauk'e jin yadda yake kissing d'inta, a hankali ya kwantar da ita kan gadon har lkcn bakinsa na nata, ta rike towel dinta gam jin yana kkrin cire mata, kuka sosae take tana kokuwa da shi, da kyar ta kwace bakinta ta turasa da duk karfinta ta mike xaune tana kuka sosai ta shiga komawa baya tace "Am on my period ya Abuu" kallonta ya tsaya yi da idanuwansa da suka sauya kala ko kifta wa bae yi yana sauke numfashi a hankali, ta tsorata ba kadan ba, xata sauka daga gadon ya fixgota yana kallonta cikin husky voice dinsa yace "Na fiki sanin u are not clean, Laifi ne don nayi kiss din ki, ke baki ji dadi ba ma na hada baki na da naki?" Sunkuyar da kai tayi jikinta na rawa bata ce komae ba, murmushi yayi yana kallonta cikin sanyayyan muryarsa yace "xaki gaya min ma'anar tsoron nan nawa da kike, soon" mikewa yayi ya nufi kofa ya fice daga dakin, ta bisa da kallo xuciyarta na bugawa.

Bayan Ammah ta gama waya dasu Batuul, Ammah ta juyo ta dube ta tace "Amnah ashe mahaifiyar Hauwa bataji dad'i ba wae", da mamaki Anty Amnah ta dubi Ammah tace "wacce Hauwa?", Ammah tace "Ajiddeh ko, matar Abu", baki Aunty Amna ta tab'e tace "Au! Allah ya bata lafiya", taci gaba da abinda takeyi, Ammah tace "kaji min yarinya, toh fa har Hauwan ta taho wae yau, kin ga kenan jikin yayi tsanani, ai baza a daka ta halinta ba, auren d'an uwanku ne kanta, dan shi zakuyi ba dan ita ko halinta ba", Aunty Amna tace "Ammah bance komai bafa, addu'a nayi mata", Ammah tace "kin dai ji, tun wuri ku gyara halin nan naku", da murmushi Aunty Amnah ta dubi Ammah tace "Allah ya k'ara nisan kwana Hajiya Ammah, yadda kikace haka za ayi", hararanta Ammah tayi tace "tashi ki koma gidanki, nasan su Nawal da Babansu na can suna jiranki", girgiza kai tayi tace "Ammah kullum sai kin korani in nazo gidan nan, can ma in Babansu na nan babu ruwansu dani shima haka, tare sukeyin komai nasu basa sani, in kuma a can ne baya nan har rasa yadda zanyi dasu nakeyi, shiyasa nake zuwa gidan nan, amma kullum sai an korani", Ammah tace "da bakya barinsu ai da zasu na sakoki a abubuwan nasu, ni yanxu tashi ki tafi, nima yanzu zan shirya a kaini gidansu Hauwan inji ya jikin mahaifiyar tata" mik'ewa Aunty Amna tayi tareda ziran gyalenta tace "Ammah kinga sai muje a tare mu dubata, ko na koma babu abinda zanyi musu in banda wahala da zasu taramin", Ammah tace "A ah ban yadda ba, kama hanya ki koma gidanki sun fi buk'atarki fiyeda zuwa gaisuwan da zakije yi, nima da driver zanje yanzu in dubota, daga baya sai mu koma da Abui", kamin Ammah ta gama magana Aunty Amnah ta shiga dialing number a wayarta, ana d'auka tace "Hello honey, zamuje mu duba Maman matar Abutturab tareda Ammah bataji dad'i ba wllj, you guys should not miss me nasan zakuyi, I will b back shortly", murmushi yayi yace "as though bamu saba ba, you know we are not going to do that, ki gaida Ammah, Allah ya bata lafiya ita kuma, ki gaishesu", tafiyanta Ammah tayi dan tasan halin Amnah, sama ta haura daga nan, Aunty Amnah ma dariya tayi tabita a baya, basu jima da hawa ba suka sauk'o, Aunty Amnah na riqe da keyn mota, tare sukaje har gidansu Ajiddeh a WUSE II, a bakin gate suka tarar da masu gadin su Ajiddeh, da sauri d'aya daga cikinsu ya taso ya fara musu magana cikin Hausarshi da ba dai dai ba yace "Sannunka da zuwa Hajiya, kazo wajen dayan Hajiya na ciki ne", kai Aunty Amnah ta gyad'a mishi tareda cewa "Ehhh", Allahumma salli Ala, kamar jira yake ta gyad'a Kai ya fara zuba "Hajiya, ai Hajiyan ciki dinma baya nan, kwananshi biyu Kenan, dayan Aunty dinne ya fara tafiya tun ya dade sai kwana guda biyu sun wuce sai babban Hajiya din shima ya tafi, toh tun rana din har yanzu basu dawo ba, Alhaji ne kawai yana nan sai masu yin aiki din na gidan suma y'an iska tun Hajiya Babba da ya tafi basa bamu abinci mai dadi yirin na da, toh munason Hajiya ya dawo, Dan Allah kayi mishi waya sai kace mangal ne yace ya dawo Dan ........", hannu Aunty Amna ta d'aga mishi tace "Kai ka tabbata, Hajiyar gidannan fa nake nufi", ta nuna mishi gidansu Ajiddeh, juyawa yayi ya dubi gidan sannan ya juyo yana kallonta yace "Ye shine gidanmu din ai, gida na Alhaji namu, sunanshi ya fada a TV munji ma lokacin Abba Ahmad Jidda", kallon juna Aunty Amna da Ammah sukayi jin bayanin mai gadin, Ammah ce tayi magana wannan karon tace "Hajiyar gidan ba rashin lafiya tayi aka kaita asibiti ba?", kai ya shiga girgizawa kamar zai yadda k'asa . "Hajiya baije asibiti ba, yapot ne Abor ya kaishi ya tafi gari nasu can", da mamaki Ammah take dubanshi tace "Toh Hauwa kuma fa, ta dawo itama ko tare sukayi tafiyan", kai ya d'aga alamar yana tunani sannan ya kallesu yace "Hauwa din ni ban sanshi ba, ba a gidan nan yake ba", dariya Aunty Amnah tayi tace "Toh mangal ai Hauwan macece ba namiji ba, Ajiddeh fa muke nufi, wacce tayi aure", yace "Owo, ai baka fadamin Aunty ne kana nema ba, ai shi din yayi auren tun ya dade, so daya ne naga ya dawo gida tun lokacin da yayi aurenshi ya tafi da miji mai kyau wannan, yana bamu kudi in yazo kullum, Kai wannan mutum da Aljanna ne nace", Kai Aunty Amna ta gyad'a tace mishi "Toh Mangal mun gode, in sun dawo zamu dawo muma", ta ciro kud'i daga jakarta ta mik'a mishi, godiya ya dingayi musu yana washe baki, suna barin k'ofar gidan Aunty Amnah ta dubi Ammah dake tunani tace "Ammah kinji wai basa nan, kuma Ajiddeh ma batazo ba, can kuma su Abu sunce miki ta dawowa mamarta ba lafiya, anya wannan abin da akwai kanshin gaskiya kuwa?", Ajiyar Zuciya Ammah ta sauk'e tace "Amina koni abinda na kasa fahimta kenan, kuma kinji fa wai ita Ajiddeh ma bata nan, toh Allah dai ya tsare", baki Aunty Amna ta tab'e tace "dama can ni Ammah hankalina bai kwanta ba, Allah dai ya rufa asiri", "Amin",basu sake yin maganan ba har suka isa gida, sai da ta sauk'e Ammah sannan tayi mata sallama ta wuce nata gidan, Ammah na isa gida ta buga waya Maiduguri, nan take ta bada order akan ayi addu'a da sauk'an Qur'ani ta tura musu kud'in sadaka, don ga dukkan alama ba abun kirki ya dawo da Ajiddeh gida ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.