Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 29 of 124

Inda su Aunty sukayi parking nan Batuul ta 膹ingisa k'afarta taje ba tare da kowa ya ganta ba tun kamin mutane su fara fitowa a hall 膹in, jiran Fitowan Aunty tayi daga hall 膹in, sai da mutane suka fara watsewa tukunna Aunty ta fito, ganin Batuul zaune ita ka膹ai da mamaki ta k'araso tace mata "Batuul mey kikeyi a nan?"mik'ewa tayi tare da k'arasowa inda Aunty ke tsaye tace "gida zan bi ki muje", sai da Aunty tabita da kallo sannan tace mata "ban gane gida zaki bini ba, da ni kika zo dama ko kuma can 膹in da kika baro ba gida bane", kmr xata yi kuma tace "Aunty ni kawai....", bata bari ta k'arasa ba ta katseta da cewa "kije ciki motoci na tafiya yanxu, na fa膹awa Baba ma can zaki kwana, tunda ke ba a abun arxiki dake sae na tsiya", jiki a sanyaye idonta duk ya cika da k'walla ta juya zata tafi, Aunty ce ta dakatar da ita da cewa "Batuul", tsayawa tayi for some seconds tukunna ta juyi tana k'ok'arin maida hawayen dake shirin zubo mata a fuska, juyowa tayi ta dubi Aunty tana jiran jin mey zata ce mata, cewa tayi "Batuul mey ke damunki, ya akayi kika ji ciwo", hawayen da ta ke ta k'ok'arin dannewa ne ya zubo , takowa Aunty tayi tazo gabanta ta rik'e ta tareda tambayanta "Batuul lafiya kike kuka, meye ya sameki, kinyi shiru ki fa膹a min, ciwon da kikaji ne?", kai ta girgiza, "toh meye" Aunty ta sake tambayanta, a hankali ta amsa da "babu", "Ban yadda babu ba, babu ne ya saki zuwa da cemin zaki gida ko kuma babu ne ya saki yin kuka", ita dai Batuul ta kasa cewa komai dan batasan ma mey ke sata kukan ba, cewa tayi "kawai inason komawa gida ne dan gidan da hayaniya ba zan iya bacci ba", ta k'arashe maganan tana share hawayen fuskanta, ba dan Aunty ta yadda da maganan ta ba tace mata "toh yanxu idan na koma da ke mey zaki cewa Ammah ya maida ki gida, ki bari tunda bikin ma ya k'are gobe sai ki dawo gida kinji" ta fa膹a mata tare da 膹an dafa kanta, kai kawai ta gya膹a a sanyaye , "keh da wa kika zo ne ma", ajiyar zuciya tayi tace tare da Yaa Abu mukazo", Aunty batace komai ba tace mata "toh yanxu ki koma ciki, su Ammah ma yanxu zasu tafi, kiyi maza ku tafi, gobe sai Ki dawo gida ki huta abun ki", toh kawai tace, Baa Liman ne yazo inda motar ke pake yace "Hajiya zamu jira wani ne", tace mishi "a ah Baa Liman, yanxu zamu tafi", sai da safe Batuul tayiwa Aunty a sanyaye ta yi hanyan hall 膹in, sai da ta jira taga Batuul ta shiga snn ta shiga mota suka tafi

Ammah ta hango ita dasu Aunty Amna sai y'an tsirarun k'awayen amarya da y'an uwanta, inda Ammah take ta k'arasa , Ammah na ganinta ta mik'e tace "Batuul ina kikaje, inace kun tafi da Farida , yanxu na k'irata a waya tace baku tafi tare ba, daga ina kike", cewa tayi "Ammah hayaniya ne yayi yawa a hall 膹in shine na 膹an fita waje", ajiyar zuciya ta sauk'e tace "toh, da har munji tsoro kowa aka tambaya sai yace bakwa tare, sae Amnah tace kila kin bi mamanku, ga Abun ma can na tsai dashi nace sai ya maidaki ko kuma in an ji kina gida su wuce, mu sai munyi ensuring everyone is safe home zamu tafi", gya膹a kai kawai tayi dan yanxu ta yadda shiga motar Abutturab 膹innan qaddarar tace, Ammah ce tayi mishi alama da yazo, k'arasowa yayi giranshi na sama da k'asa a ha膹e, harara yabita dashi sannan yace wa Ammah gashi nan, "ku tafi toh tunda tazo, kayi maza kaje ka sauk'e y'ar mutane ta gaji", a tak'aice yace toh ya juya, ko ba a fa膹a mata ba tasan binshi ya kamata tayi, a baya ta bishi shi da matar tashi dake wani yatsine yatsine har wajen mota, shi ya bu膹ewa Ajiddeh front seat ta zauna, shi kuma ya zagaya ya shiga side 膹inshi, itako back seat ta zauna kanta a kasa, a nutse yake tuk'in hannunshi cikin na Ajiddeh yana yi mata magana k'asa k'asa tana ta shan k'anshi, da suka isa gidansu Ajiddeh ma fita sukayi suka barta a motan sai da sukayi wajen minti talatin a waje tukunna ya rungumeta kmr baxa su rabu ba daga k'arshe ya shigo dan da alama aikin lallashi yake ta yi, yana shiga motan sae da ya bari ya fita daga compound din gidan snn ya juya yana kallon Batuul fuskarsa daure yace "waye driver ki, c'mon kin dawo gaba ko sae na sauke ki a titi", ita dai bata ce mishi komai ba ta bu膹e k'ofa ta dawo gaba, sai da ya kama hanya ssae tukunna ya fara magana ba tare da ya kalleta ba "keh wato ni na zama driver 膹inki ynxu ko, duk yadda za ayi sai kin samu yadda kika yi Ammah ta ha膹ani dake koh, kin wuce kin tafi yawon ki kin 膹agawa mutane hankali ana ta nemanki, inama kika fita kika tafi in d first place?" kinsa matan aure zama a waje duk da sunan jiranki, tunda ya fara magana bata ko kalli inda yake ba, shiru tayi bata kulashi ba, tsawa ya daka mata tare da cewa "ba tambayanki nayi ba, ina kikaje?" hawayen da tayi ta mayarwa ne ya zubo mata, kuka ta saka da karfi kamar wacce aka daka ta kifa kanta akan gwiwanta tana rerawa, sosai take kukan kamar ran ta zai fita, juyawa yyi yana kallonta, a fusace yace "wato ba a isa yi miki fa膹a ba shine zaki fashe min da kuka kmr wata yarinya, shut that mouth ynxu", kamar k'ara mata kukan akeyi taci gaba da kukanta kamar bata ji shi ba har da shessheka, tsaida motar yayi xuciyarsa na tafasa yace "fita min a motata", ko kallonsa bata yi ba tana ta aikin kukanta, da tsawa ya sake ce mata "i said get out,", 膹ago kanta tayi tareda share hawayenta ta dubi cikin idonshi tace "babu inda zanje, ka mayar dani wajen Ammah kace mata baza ka kaini ba mana", mamaki ne ya sashi sakin baki yana kallonta, dama tana magana haka, ranshi ne yaji b'aci, bu膹e k'ofa yayi ya fita ya zagaya ta inda kofarta take, bu膹e nata k'ofan yayi ya ce mata "out", tana zaune kamar bata jin abinda yake fa膹a, fixgota yayi ya fitar da ita daga motan da karfi ya juya ya koma nashi side 膹in ya tada motan ya tafi, tana ganin tafiyarshi ta nemi waje ta zauna tana kuka ssae, iska ne ya fara ka膹awa mai k'arfi tare sa walk'iya, 膹ankwalin dake kanta ta warware ta yafa a kanta tana hawaye, tana nn zaune aka fara yayyafi, duk'unk'une wa tayi waje daya dan sanyi yayi mata yawa ga tsoro don bbu alamar mutum wajen, ruwane sosai ya sauk'o kamar da bakin k'warya amma ko niyyan tashi ba tayi ba sae hade kanta da tayi da gwiwa tana kuka a hnkli, ruwan da ya ganine ya sashi parkin, snn juyar da kan motan a hnkli, cikin 'yan mintuna dawo wajen da take sbda gudun da yyi, fitowa yayi daga cikin motar ya isa inda take har lkcn yace "tashi mu tafi", kamr bataji shi ba ta 膹auke kanta, sai rawar sanyi take, da taji zai isheta ne ta tashi tayi hanya daban da sauri jin ya biyota yasa ta saka gudu, binta yayi da hanxari ya fixgota, jiri ne taji yana 膹ibanta dan sanyin ya mata yawa, tanga膹i ta fara zata fa膹i yayi sauri ya tarota jikinshi, mutsu mutsu ta shiga yi xata kwace kanta bugun xuciyanta ya tsananta, kin saketa yyi ruwa na dukansu, cak ya 膹auketa daga karshe ya kaita cikin motan yayi mata baya da seat 膹in ya kwantar da ita fuskarsa dab da nata har tana iya jiyo numfashinsa cikin kaushin murya yace " Idan kika kuskura kika fito xaki sha mamaki na" kasa motsi tayi daga gurin xuciyarta kmr xae fito don tsoro kamshin turarensa duk yabi ya isheta ga fuskarsa dake dab da nata har lkcn, da kyar take jan numfashi tsabar wani rawan sanyi da take, yafi minti uku yaki daga kallonta duk da ynda yaga jikinta ke rawa ssae, daga karshe ya mike ya rufe motar.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.