Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 26 of 124
Bayan few minutes Batuul ta shigo 膹akin kinkime da babban tray, saura ka膹an ta sake tray 膹in don wani irin fa膹uwa gabanta yayi ganin shi ka膹ai ne a 膹akin, kanshi ya 膹ago ya ganta tsaye, 膹auke kai yayi yaci gaba da abinda yakeyi a wayarsa, ganin ta fara gajiya da tsayuwan ne ya sata k'arasawa jiki a sanyaye ta shigo, a gabanshi ta sunkuya ta ajiye tray 膹in , shi kuma gashin kanta da tayi parking in a messy bun yake kallo, yadda sukayi curls wasu na lilo ya zubawa ido, 膹agowa tayi daga tsugunnen ta mik'e tsaye, tsayawa tayi a kanshi tana so tace yana zaune a kan 膹ankwalinta zata 膹auka amma ta kasa bude baki, binta yayi da kallo yace "wa zai zuba min abincin kin wani ajiye kin nemi waje kin tsaya kina kallona, C'mon sense din ki bae baki cewar ba dungure min abincin xaki yi ki mike ba", bata kulashi ba sae wani hade rae da tayi ta tsuguna ta 膹auki plate da serving spoon kanta a kasa tace mishi "mey zan zuba maka", ba tare da ya kalleta ba a takaice yace "anything", gima ta zuba mishi a plate 膹in, daga gefe ta saka mishi scrambled potato mai cheese sai k茅moniye a wani saucer, kallonta kawae yake har ta dago kai tana kallonsa tace " Ya isa?" Bae tanka ta ba sae sunkuyawa da yayi ya 膹auki abincin ya fara ci a hnkli, 膹agowa yayi da kanshi ya ganta tsaye tana fidgeting yatsunta kamar zatayi magana, kallonta shima ya tsaya yi sae dae fuskarsa a daure, sunkuyar da kanta tayi da sauri, shi kam bae fasa kallonta ba sae a nn ya kuma lura da yarintar ta, k'aramace ssae ya fa膹a a ranshi, a fili kuma cikin dakewar murya yace mata "get me a bottle of water", ba musu taje 膹auko mishi ya bita da kallo har ta bude fridge ta dauko ruwan, kan ta juyo ya maxa ya sunkuyar da kansa, ta karaso ta mik'a mishi, hannu yasa zai karb'a taji hannunshi cikin nata, maza tayi ta sake ruwan ya fa膹i a k'asa, kallonta yayi tare da jan 膹an k'aramin tsaki ya 膹auki ruwanshi, ganin ta kasa mishi maganan 膹ankwalinta ne ya sata kawai ta fita haka, juyawan da tayi zata bar wajen kawai ta bige tumbler dake wajen , a take suka tarwatse a wajen, ba karamin rikicewa tayi ba ta daga k'afa da sauri zata matsa daga wajen ta tak'a 膹aya daga cikin broken glass 膹in, wani k'ara ta saki ta tsuguna a wajen, wani mugun kallo yake jefa mata kmr xae maketa, ita ko duk ta tsorata ta saka kuka, ganin jini a kafar ne ya sashi ajiye abincin hannunsa a gefe da sauri ya mike, tunawa da yayi lokacin da yake k'arami suna London, Aunty na koya mishi homework 膹inshi ya 膹auki blade ya yanke hannunshi dashi, rudewa tayi sosai har idonta sai da yacika da hawaye tayi mishi treating hannun, har sai da ya warke tukunna ta fara barinshi yana yin abu da kanshi, karasawa yyi inda take ya tsugunna dab da ita har tana iya jiyo numfashinshi a fuskanta, ga k'anshin turarenshi ita yayi mata yawa, hannunshi yasa zai janyo k'afarta tayi maza ta janye, tsaki yayi tare da janyo k'afan yana dubawa, glass 膹in da ya mak'ale a k'afan ya sa hannu ya cire, wani ihu tasa tare da k'ank'ame shi, shiru yayi yaji yadda heartbeat 膹inta ke bugawa da k'arfe, idonta ta bu膹e da taji zafin ya 膹anyin sauk'i, da sauri ta sakeshi ta matsa baya ganinta kwance a jikinshi, tashi yayi ya koma gefen gadon ya zauna, yunk'urin tashi tayi itama zata tafi ta kasa, wani k'ara ta sake sawa, tasowa yayi ya dawo gabanta ya mik'a mata hannun alamun ta rik'e ya mik'ar da ita, nok'e hannayenta tayi, haushi ne ya sashi sunkuyowa ya 膹auketa cak sae jin ta tayi jikinsa, ta wara ido ganin abinda yayi, k'ok'arin sauk'a ta farayi daga hannunshi, hade rae yyi ssae ya xuba mata idonshi masu kama da na masu jin bacci, hawaye ne makale idonta suna shirin zubowa, ce mata yayi "stay still, ciwo kikaji bazaki iya tafiya ba, am helping, ki tsaya in gama or ki sha mari ynxun nn, ina wasa da ke ne" yana hararanta ya kare mgnr, shiru tayi ta dena k'ok'arin sauk'an da take sae dae ba karamin faduwa gabanta yake ba, toilet 膹in 膹akin ya shiga da ita ya ajiyeta a bakin bathtub, shower ya janyo ya kunna ruwa yana zubawa a wajen tare da sa hannu yana wanke jinin da ya fara bushewa a wajen, rintse ido tayi ta dafa sa sabida zafin da wajen keyi, sai da ya gama ya sake 膹aukanta cak ya fito da ita 膹akin, a kan kujera ya kwantar da ita , 膹akin Abui ya shiga ya 膹auko first aid kit, dab da k'afanta ya zauna ya kamo k'afan ya shiga gogewa da spirit da cotton wool, ido ta rintse tsabar azaba ta rik'e hannunshi da sauri, sae kuma ta sake kuka, hannunta da ta rik'eshi dashi yabi da ido, 膹auke hannun yayi daga jikinshi yaci gaba da abinda yakeyi, zafin ne yayi yawa tace mishi "Yaa Abu dan Allah ya isa haka, akwai zafi", dubanta yayi yaga hawaye take ssae ,ce mata yayi "clean your face and close your eyes, it wont hurt, beside raki ne yyi maki yawa", hakan tayi ta rik'e mishi riga har sai da ya gama dressing ciwon , tashi yayi daga wajen ya gyara mata k'afan ta kwanta comfortably, juyawa yayi zai fita tace mishi "Yaa Abu don Allah ka kira min farida", tsayawa yayi cak ba tare da ya juyo ba jin ta k'ira sunanshi sai da yaji abinda take buk'ata, ba tare da ya juyo ba yace "Anki" fita zaiyi daga 膹akin kenan Farida ta shigo tana ihun "Batuul mey kika tsaya yi tun 膹azu ina jiranki kizo kiga kayan da akayi mana, its f**ki....." bata k'arasa ba tayi maza ta rik'e baki ganin Yaa Abu a tsaye, dariya ne kawae Batuul bata yi ba ganin yadda ta ha膹iye maganan, a sanyaye ta k'arasa wajen Batuul tace "mey ya sameki, ya akayi kika ji ciwo har haka daga fitana" "Shut ur filthy mouth nd clean up this mess kafin in dawo" yana kai wa nn ya sa kai ya fita, da harara ta bisa snn ta dube Batuul tace "shi ya ji miki ciwon ko, ai nasani, kuma in yaga mutum yaji ciwo yafi kowa damuwa, garin yaya", kai Batuhl ta girgiza tace mata "Ba shine fa ya ji min ciwo ba, nice na fasa tumbler da na ajiye, dama ance everybody will b d first victim of his own corruption, gashi nan ni ya fara ji wa ciwo", tausaya mata Farida tayi tace "sannu", tambayanta Batuul tayi "mey kike fa膹a ne da kika shigo har da su f**king" ta k'arashe maganan tana mata dariya, "kayanmu ne na dinner, yayi kyau sosai, both d material and d style sunyi kyau sosai, sai ma mun saka tukunna", ce mata tayi "Dinner sai ku, ni yanxu ina naga k'afan zuwa dinner" a ranta kuwa hamdala tayi ta samu rusheshen excuse da xata bada dan dama bata son zuwa, a hnkli Farida tace "toh nima bazanje ba tunda bazaki ba", ido Batuul ta wara ta bu膹e baki tace "kinsan mey kike fa膹a , dan bazanje ba kema bazaki ba, ai sai in sa Ammah ta turaki dole, bare da ita ma za a ai dole kije", dariya Farida tasa tace "I wont miss it for the world wasa ma nakeyi, zanje kema kuma zakije yarinya", kamin ta bata amsa Ammah ta shigo 膹akin, ganin Batuul a kwance yasata hanzarin k'arasowa inda suke, tambayanta ta shiga yi yadda akayi taji ciwo, fa膹a mata gaba 膹aya, sai da ta gama tace mata "Toh yanxu ina Abutturab 膹in, shine dan bak'in hali ya fita ya barki ke ka膹ai Kuma bai zo ya sanar dani kinji ciwo ba", "yanxun nan ya fita Ammah", Batuul ta fa膹a mata, taimaka mata sukayi ta tashi, har toilet sukaje da Farida tayi alwala ta fito, ka膹an ka膹an take 膹ingisawa, side 膹in Ammah suka koma sukayi sallah suka fara shirin zuwa dinner dan Ammah tace babu abinda zai hanata zuwa, har da dan hawayenta don ba hka ta so ba.
[8/22, 1:54 PM] .: 馃挅馃æŒBATUUL馃挅馃æŒ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.