Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 52 of 124
Washegari tunda aka sallameta bayan taji ranan za a wuceta da ita take kuka kmr ranta xae fita, duk ta fita hayyacinta, k'arfe takwas aka zo 膹aukanta, lokacin Aunty ta bata wani lace blue mai kyau da tsada ta saka, ta bata wani laffaya shi kuma Golden, ta saka mata costumes 膹in gwal, Batuul dai babu abinda take sai kuka, duk da ba wani kwalliya tayi ba tayi kyau sosai, wajen Baba aka fara kai ta yayi mata Nasiha sosai, rungumeshi tayi sosai tana rusa kuka, da k'yar ta sakeshi, k'annenta ma kukan sukayi tayi ganinta tana kuka, Ahmad, Sa'eed da Khalil ne kawai basuyi kuka ba amma suma jikinsu yayi sanyi, Aunty kam kasa mata magana tayi dan ji takeyi itama zatayi kukan idan ta bude baki, kanta kawai ta shafa cikin sanyin tace "Allah ya miki albarka, ya kare ki a duk inda kike", daga nan ta juya tayi 膹aki, Sistern Baba ce ta kai ta har mota, suka shishshiga convoy 膹in motocin dake waje akayi gidan Ammah da ita.
[8/22, 2:09 PM] .: 馃挅馃æŒBATUUL馃挅馃æŒ
40
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Suna isa bayan an shishiga dasu gidan Aunty Hafsat ta d'ago Batuul dake ta faman razga kuka, sauran Aunties 膹in Aunty da suka taho tare suma suka fiffito daga motocin, Aunty Amnah ce ta fito ta tarbesu da fara'arta, babu abinda Batuul takeyi sai kuka kmr xata shide tana rungume jikin Aunty Hafsat, k'anshin turaren wutane kala kala ke tashi ta kowane angle 膹in babban palon, ga wani sanyi dake bugasu, babu abinda matan palon suke sai gu膹a, sama akayi da Batuul zuwa 膹akin Ammah, Farida na biye bayansu ta rasa farin ciki take taya Bestyn nata ko kuma bakin ciki take da auran Yayanta, A kan lallausan rug 膹in dake 膹akin Ammah Aunty Hafsat ta zaunar da ita, 膹agota Aunty Amnah tayi ta maidata kan gadon tace "A ah baza ta zauna a k'asa ba", Aunty Hafsat dai batace komai ba sai murmushin da tayi, haka akayi ta shigowa gaida amarya amma fir taqi bu膹e fuskanta sai faman zubda hawayen da take, saida duk suka gama suka fita tukunna Ammah ta shigo 膹akin, hannu tasa ta sake janyo gyalen yadda baza a gane ba, Ammah na k'arasowa ta zauna daga gefen Batuul, mayafin dake kan Batuul Ammah ta 膹aga tana kallon fuskan Batuul da ke hawaye, "Masha Allah", abinda Ammah ta fara fa膹i kenan gani yadda Batuul tayi kyau sosai, matso da ita gefenta tayi tace "Bitti kukan har yanxu, toh kiyi hak'uri kinji, ai nanma gidane, karki damu kinji, ki kwantar da hankalinki", ita dai Batuul taki cewa komai sai hawayenta da ya da膹u, mik'ewa Ammah tayi tasa Aunty Amna su kawo musu abinci tace tana zuwa itama ta fita.
Yana kwance rigingine 膹akin Massa idonshi lumshe kamar mai bacci, Massa ne ya shigo 膹akin yana waya ganinshi kwance yasa ya katse wayan ya zauna daga arm 膹in kujerar ya 膹an tab'ashi, a hankali ya bu膹e idanunshi dake lumshe ya sauk'esu kan Massa yana jiran jin mey zaice, mik'ewa yayi ya zauna ganin Massa ya ki cewa komae yace "wai meye kake kallona haka ne, is this your first time seeing me", murmushi Massa yayi yace "ango irinka ne ni ban tab'a gani ba, yau za a kai maka amarya shine kazo ka kwanta min a 膹aki, da ni nake ango yau ai da tun rana zan tafi, da kanku ma zaku kaini in na isheku", 膹an tsaki Abutturab yaja zai koma ya kwanta Massa yasa hannu ya rik'oshi yace "Man what are you doing wai, tun 膹azu kazo ka kwanta, kai ko marmarin 膹auko amaryar taka ma bakayi, dukda nasan ba kai zaka 膹aukota ba ai sai kaje ka dubata koh", wani irin kallo ya sakar mishi yace "ni ba sai ka tsaya yimin surutu ba pls, just tell me you need privacy, i should excuse you", ya koma ya kwanta, baki Massa ya bu膹e zai yi magana yaji wayanshi na ringing, tashi yayi yaje ya 膹auko, ganin Ammah ke k'iran yasashi amsawa a risine, a nutse yace "Ammah Nda dubdo, ya gajiya", ta amsa mishi da "Lafiya Massa, kana tare da Abu ne", juyawa yayi yana kallon Abun da ya mik'e da sauri tun sanda yaji Massa ya ambaci Ammah, ce mata yayi "Ehh Ammah, gashi nan muna tare", tace mik'a mishi wayan", "Toh kawai yace ya isa inda Abutturab yake ya mik'a mishi wayan, ansa yayi yasa a kunnenshi a hankali yace "Ammah Nda dubdo", bata ansa gaisuwan da yayi mata ba tace "Shine har da kashe waya tsabar raini ko Abu, Yayi maka kyau ai, bakaje ka 膹auko matarka ba dan ka nuna mana kai ka isa ko, toh Abui yasa anje an 膹aukonta hkn kuma bae sa ka xo gaida wa enda suka kawo tan ba yayi maka kyau, kayi abunda kaga dama Abu", bai samu yace komai ba tana kaiwa nan ta katse k'iran, kanshi ya dafa tareda cewa "Shit not again, wlhy bana son Ammah na fushi dani akan yarinyar nan", wayanshi ya janyo dake gefenshi a kujera a sanyaye tareda da 膹aukan key ya shiga neman layin Ammah, ringing yakeyi amma taqi 膹agawa, mik'ewa yayi yacewa Massa da ya kafeshi da ido yace "Am going", bayanshi Massa yabi yace "Mu tafi tare", tare suka fita Abu na tuk'a motar, tunda suka shiga gidan matan dake cike falon suk'e tsokananshi, Farida ya gani na sauk'owa kan stairs, tsaidata yayi ya tambayeta "Ammah fa" ce mishi tayi "tana side 膹in Abui", daga nan bai tsaya jin komai ba ya juya yayi side 膹in Abui, Ammah kawai ya gani tana k'ok'arin rufe wani akwati, k'arasawa yayi har wajenta yace "Ammah kiyi hak'uri kinji, bansan kina nemana ba, wayan na silent ne, I was having a slight headache shine na tafi gun Massa in huta", ya k'arasa magana tareda da yi mata side hug, ji tayi baza ta iya ci gaba da yi mishi fushin ba, juyowa tayi itama ta kalleshi tace "Abu mesa kullum sai kasa ni yin magana", kai ya girgixa da sauri yace "In sha Allah Ammah bazan sake saki magana ba", tace "Allah yasa, kaje ku gaisa da y'an uwanta da sukazo tare da ita, wannan akwatunan ma nasune zansa a fidda musu inda motocin ke pake", yace "Toh" ya juya ya fita, a palo ya tarar dasu Aunty Hafsat har sun sauk'o k'asa, a nan ya gaggaisa dasu cikin jin kunya, Aunty Amna sai tsokanarshi take, shi dai baya cewa komai sai murmushi da yakeyi kanshi a k'asa, da haka sukayi sallama suka wuce, su Aunty Amna suka rakosu har wajen motocinsu, sukayi Godiya suka bar gidan.
Su Aunty Hafsat na tafiya Farida ta shigo 膹akin ta hau kan gadon da Batuul ke zaune, mayafin kan nata ta yaye, jikinta ne yayi sanyi ganin yadda Batuul ke hawaye babu k'ak'k'autawa, janyota tayi jikinta itama ta fara hawayen tace "Batuul you are making me emotional, kiyi hak'uri ki bar kukan nan haka dan Allah kinji, everything happens for a reason, it was destined to happen kuma In sha Allah its for d best, ni nasan ko ba komai Ammah will b there for you always kinji, as it is kuma, Yaa Abu is not that bad, just that baison raini and baya sakewa da mutane but bayan haka he is a very nice person at heart, nasan he will take care of you, kiyi hak'uri ki bar kukan nan kinj, kar ya sa miki ciwon kai, kinga Ammah ma in ta shigo taga har yanxu kina kukan nan baza taji da膹i ba", ta gama maganan tana sharewa Batuul hawayen da yaqi ya dena zuba daga idanunta, da kyar Farida ta samu tasata tayi shiru, Ammah ce ta shigo ganin Batuul zaune a inda take bata motsa ba tace "Bitti baki tashi kin canja kaya ba tun 膹azu, maza tashi shiga kiyi wanka, ai kayan nan sun miki nauyi", kanta a k'asa dan wani kunyan Ammah takeji kwana biyun nan, Ammah ta dubi Farida tace "taimaka mata ta shiga tayi wanka", ita kuma Ammah ta juya wardrobe 膹inta ta cirowa Batuul kayan baccin da zata saka, tana ajiyewa ta fita.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.