Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 93 of 124

Hawaye kawai Farida keyi dan ita Sam bata shirya tafiya ba yanzu, Abu kam driving yakeyi hankali kwance ko kallonta baiyi ba, a hankali ta bud'e baki tace "toh Yaa Abu kaga bari in k'ira Ammah in fad'a mata ina zuwa kar taga nayi dawowan baza....", wani irin kallo da ya wurga mata yasa ta saurin sunkuyar da Kai, bata sake d'agowa ba saida taji yaja ya tsaya da motar, jiki a sanyaye ta d'ago kai tanace airport suka zo, duk ranta ba dad'i batayi sallama da Batuul ba, ganin ba airport bane yasata sauk'e ajiyar zuciya tareda murmushi, fita yayi daga motan yayi gaba itakam tana nan zaune dan baice ta fito ba, saida yaje bakin k'ofar shiga yaganta zaune cikin mota ya daka mata harara yace "kin fito cikin motar nan ko sai nazo na fidda ki mara kunya", ba shiri ta fito tana zumb'uro mishi baki tabi bayanshi, numfashinta ne ya kusa d'aukewa ganin irin tsaruwar gidan, tasha ganin gidaje masu kyau ko designs d'in Yaa Abu amma wannan daban yake, ya tafi da ita ba kad'an ba, binshi kawai takeyi har suka k'arasa hawa sama ya bud'e wani d'aki ya shige ciki, bayanshi tabi itama ta shiga, Batuul ta hango kwance kan gado tana bacci hankalinta kwance, batasan lokacin da ta fasa wani ihu tana fad'in "Sweetheart ashe kina nan shine kika barni so lonely inata Nemanki....", tana yi tana nufar gadon da niyyar hawa, da hanzari ya fizgota yana mata mugun kallo yace "bakida hankali ko? Tashinta zakiyi daga baccin", ta zumb'uro mishi baki tace "toh aini ban sani ba" , yaja tsaki ya jefar da ita ya koma gaban computer da alama tunda ya fita baccinta takeyi hankali kwance, d'an murmushi yayi ya dawo bakin gadon tareda hawa yana kallon kyakyawar fuskarta, hannu yasa ya gyara mata gashinta da ya bazar tun d'azu snn ya gyara mata duvet, a hankali ta bud'e lumsassun idanunta dake cike da bacci ta sauk'esu kanshi, murmushinta mai kyau tayi mishi ta sake maida idanun ta rufesu, shima har lokacin murmushin ne a fuskanshi, Farida ikon Allah ta tsaya gani, a hankali ya sunkuya yayi kissing goshinta snn ya sauk'o daga kan gadon, Farida ya gani duk ta wara ido tana kallon Abunda yake, harara ya sakar mata yace "kallon na lafiya ne, mara kunya kawai saura ki tada ta, kuma if you try something stupid sai nayi maganinki dan yanzun ma ba k'yaleki nayi ba" daga haka ya fita, itakam yana fita ta murgud'a bakinta tace "masifaffe" tayi windown d'akin tana kallon yadda tsarin gidan mai kyau yake

Mummy zaune gaban boka Namurje bayan ta gama zayyano mishi abinda ke tafe dasu tana haki, saida ya gama jin bayanansu snn ya d'ago kanshi tare da janye abunda ke kife akan nashi mai kamada hood, innalillahi wa inna illaihi rajiun, wani irin mutum ne zaune gabansu da ko kad'an bashida kyan gani, bak'i ne k'irin snn ga wani shafteten maki shimfid'e a fuskanshi, irin mazan nan ne murd'ad'u, Su Mum hankali kwance ko tsoron halittarsa basuji ba, magana ya fara da wata irin razananniyar murya yace "duk naji bayananku kuma zaku sami aiki daidai bud'ewar jakarku, Mummy tayi caraf tace "ai In kud'i ne bakada matsalarsu, ranka shi dad'e munason wannan yarinyar a fara ta kanta, ba abinda ke cikinta kad'ai za a halaka ba har itama in san samune munaso tabishi inyaso daga baya sai musan yadda za ayi da sauran matsiyatan, dan ni har iyayen yarinyar sai naso ganin bayansu tunda suma ganin bayanmu sukeson yi", ya saki wata shegiyar dariya da gama jin maganganunta yace "Aikinki ya gama, a mik'osu tukunna sai kiji kanun bayanin", jiki na rawa Mummy ta janyo jakarta ta shiga zazzage mishi mak'udan kud'in dake cikin jakar masu uban yawa, kai kace ita akayiwa kishiyar sabida yadda jikinta ke b'ari, sai da ta juye tas snn tace "gasu nan ranka shi dad'e, inma da k'ari za a biyoka dasu", baice komai ba ya d'auko wata jaka ya ciro wani abu shi ba nama ba snn ba jini ba k'ulle a leda ya mik'o mata yace "wannan abin da na baki zaki jefa cikin kogi, bazaki bud'i baki ba har sai kin gama aiwatarwa , yadda zai b'ace cikin ruwan nan haka nan cikin jikinta zai b'ace itama tabi sahu", Mummy jiki na rawa tasa hannu biyu ta amsa kamar wacce aka mik'owa abin kirki ta shiga ce mishi "Nagode ranka shi dad'e", Aunty Jainaba tace "muna nan dawowa bada dad'ewa ba", shidai baice musu komai ba har suka gama b'ab'atunsu suka fita, Aunty Jainaba tace "Yaya kinga wannan mutumin da gani bana wasa bane dan har firgitani yayi da farko", Mummy tayi murmushi tace "Ai Bilkisu da zauri'arta wasa suke dani basu san wacece Zuwaira ba har yanzun, sunana kawai sukeji", suka sa shewa gaba dukkansu biyun sukaci gaba da hiran abubuwan sharrin da zasu jefi Zuri'ar Ammah dasu har suka iso inda motar Sadi take, a firgice ya tashi daga baccin da yakeyi jin an bud'e motar ya Shiga
mitsike ido yace "Hajiya ashe har an fito" basuce mishi komai ba tunawa dasukayi da gargad'in da bokansu yayi musu kawai suka fad'a mota, tab'a baki yayi ganin babu wanda ya kulashi yaja k'ofar ya tada mota suka tafi, wajen sha d'ayan dare suka iso garin Abuja, saida suka zo dab Jabi lake snn Mummy ta shiga tab'a Aunty Jainaba ta tsaida Sadi a wajen, hakan kuwa akayi yayi parking suka fito suka gama tsafe tsafensu suka dawo mota sunata murna tareda fatan samun Nasara har suka isa gida

Kanshi ya kifa jikin steering motar yana tunano stress d'in da ya shiga kwanakin nan, sam hankalinshi yaqi kwanciya da barin Batuul, ga wannan sarkin y'an rawan kan tazo zata k'ara mishi akan na da, iska ya furzar bakinshi ya tada motar yayi hanyar gida yana tunanin yanda zai shawo kan Ajiddeh ya bata hak'uri, parking yayi ya fito daga mota ya shiga gidan, kamar kullum tana nan kwance idonta a kumbure, tana ganinshi ta fashe da wani kukan, yasan hakan zai faru shiyasa ya shigo a shirye, rarrashinta ya shigayi da bata baki as usual don aikin kenan kullum, itakam murna cike fal ranta jin bayanin dasu Mummy sukayi mata a waya, sai da ta gama bashi wahala snn ta sauk'o kamar ko da yaushe, daga nan suka fad'a wata duniyar, ko masallaci bai fita ba nan gida yayi Magrib da Isha itakam tana kwance har saida yayi dagaske tukunna ta tashi tayo alwala ta had'e sallolin da duk ma babu nutsuwa cikinsu, tana idarwa ta dawo jikinshi ta shiga yi mishi wasu abubuwan amma gaba d'aya hankalinshi na wajen Batuul, so yake yaje ya ganta dan yasan ba kowanne abincin takeci ba sai kayan kwad'ayi amma fir Ajiddeh taqi kyaleshi, ita ko tambayar inda ya kai ta ma bata yi.

Kamar yadda yace kar ta tada ta batayi karambanin tada ta ba, k'asa ta sauk'o tana zagaye gidan tana yaba kyan da yayi mata, sai da ta gaji dan kanta ta hawo sama, bata dad'e da dawowa ba Batuul ta farka da mamaki take kallon Farida ta wara tace "Laaah yaushe kikazo, wa ya kawoki?" Farida tayi dariya tace "wannan baccin naki ai har a saceki baki sani ba, tun d'azufa kike kwance", "Wanne irin tun d'azu? Bai jima bafa da na kwanta" inji Batuul tana k'ok'arin sauk'owa, Sallah azahar ta d'auro alwala tayi daga nan suka sauk'a k'asa sukayi kitchen Farida sai santin gidan takeyi, Farida ce ta shiga had'a musu lunch Batuul kuma na zaune kan island d'in kitchen d'in, in no time Farida ta had'a musu spaghetti lasagne tanayi sunata shan hira, saida ta gama snn tayi musu serving a bowl d'aya, tana tunkaro Batuul dashi dariyar dake fuskarta ta d'auke ta toshe bakinta, Farida tace "A'a meye hakan" da k'yar ta samu ta iya bud'e baki tace "kin saka cheese bana so", da mamaki Farida ta tsaya kallonta Dan tasanta da son cheese, sabida itama ta zuba tace "Cheese d'in ne ya saki kamar zakiyi kuka?", ta bud'e baki kenan zata yi magana taji amai na yunk'uro mata, da gudu ta sauk'o tayi sama, Faridan ma a guje ta ajiye fork d'in hannunta tabita a baya tana tambayarta ko lafiya?, saida ta gama kwarara amanta a toilet snn ta d'ago a galabaice duk batada k'arfi, Farida duk ta rud'e sai hawaye take ta rasa yanda zatayi gashi ta baro wayoyinsu wancan gidan sabida tsabar masifan shi, kamo Batuul tayi daga toilet d'in ta wanke mata fuska snn suka fito, kan gado ta kwantar da Ita sai maida numfashi take, tashi tayi ta fita ta dafo mata noodles cikin lokaci kad'an, nanma Batuul turewa tayi tace batason kamshinshi, Farida duk ta damu tace "Besty wai mey ke damunki?, dama yana miki haka kuma yaushe kika zama allergic to cheese da har zai na saki amai",Batuul dai shiru tayi mata tana maida numfashi, a hankali kamar mai rad'a tace "Orange Juice zansha da Toast", da sauri Farida ta mik'e bata dad'e ba ta dawo riqe da abinda Batuul d'in ta fad'a mata, kad'an taci ta ture tace ta k'oshi, ta kwanta bacci, Farida kam kallonta kawai takeyi jikinta duk yayi sanyi, saida ta tabbatar baccin Batuul keyi sannan ta tashi ta sauk'a k'asa dan ta fara jin yunwa, sai a snn ta tuna da girkin da tayi musu, warming tayi ta tsiyayo juice tayi sama dashi, duk bayan seconds sai ta kalli Batuul ta tabbatar tana lafiya, Batuul kam Bacci takeyi sosai, lokaci lokaci takan bud'e ido suna had'a ido da Farida zata sakar mata murmushi taci gaba da baccinta abin har tsoro ya fara bawa Faridan, Har magrib Batuul bata tashi ba sai da Farida taga gari yayi duhu snn ta tada ta suyi sllh magrib, tana farkawa tace "Yaa Abu fa?, bai dawo ba?", Farida tace mata "Ehh", take mood d'inta ya canja ta had'e rai tayi toilet abinta, koda ta fito kin yin magana tayi, Farida har saida ta gaji dan kanta tayi shiru, Kallonta Farida tayi tana murmushi dan ta kasa daurewa da sudden behavior nan nata tace "uhnnm Besty ko dai Baby za a samawa Yayana ne wannan rashin lafiya haka?", kunya duk ya rufe Batuul tayi kicin kicin da fuska tace "Baby kuma, wani irin baby, Malaria nake ya kama ni", dariya maganan ya bawa Farida tace "Ko ba Malaria ba, ai 9ja muke dole kice Malaria kikeyi", bata kulata ba dan ita rashin zuwan Abu ke damunta, itama Faridan badan ta yadda ta k'yaleta ba, haka ta zama wata shiru shiru har goman dare tana tsammanin dawowanshi amma baizo ba har sha d'aya har saida Farida ta gane, shima Abu gaba d'aya hankalinshi na kan Batuul, gashi ta zama so choosy akan abinci duk hankalinshi ya tashi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.