Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 124

Batuul tace "okay",

sama suka haura suka isa dakin Faridan, suna shiga ta cire gyalenta ta ajiye a akan gadon ta juya inda fridge din dakin yake zata dauki Fanta, tana budewa taga babu Fanta è„¿ fridge din, "kinsan zanzo shine baki saka Fanta a Fridge dinki bako, sai tarin bakaken drinks da kika ajiyewa mutane(coke),ni na sauka fridge din kasa in dauko, batajira jin abinda Farida zata ce mata ba ta sauka ta isa dinning area ta bude standing fridge din zata dauki Fanta taji wata Murya cikin sanyi an Ce "Farida kawomin bottle water daya", bugun zuciyantane ya k'ara tsananta, Bata juyo ba kuma batayi magana ba har sai da ya k'ara maimaita maganar amma yaji shiru, ransa ne ya b'aci ya taso yaga abinda takeyi da har ya hanata amsa mishi, yana zuwa ya fizgota da k'arfi da har saida ta fada kirjinshi kamin yayi sauri ya janyeta
[8/22, 1:35 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

6

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

tsayawa yayi ya na kallonta ita kuma kanta è„¿ kasa, ba a Jin komai sai bugun zuciyanta da ya kara tsananta, riqon da yayi mata ne da kuma bugun zuciyanta yasa hawaye taruwa è„¿ idonta, kiciniyar kwace kanta ta fara yi daga wajenshi amma yaki saketa, Dumi yaji a hannunshi ya juya yabi hannun nashi da kallo, hawayen da ya gani ne yasa shi sakinta a hankali ya juya mata baya, juyowa ya sakeyi zai yi mata magana yaga bata wajen,

Parlour ya koma zauna yabi stairs din da ta hau da kallo, lokaci daya ya shiga kwada ma Farida qira, A bakin kofa ta kusa cin karo da Farida, Farida tace "kinga abinda nake gaya maki, I Wonder why he is calling me yanxu" bata karashe maganan ba ta ta riqe Baatul tana tambayarta "Why are you sore ? Mey ya sameki kuma idonki ya canja , kamin ta bata answer ta sukaji ya sake kwada ma Farida kira, bata jira cewan Batuul ba ta sauka kasa tace "Gani Yaa Abu" a nutse yace "Who is she ? I mean that lady, doesnt she talk ko kuma gaisuwa ne bata iya ba ? A zuciyanta cewa tayi "Innalillahi wa inna illaihi rajiun, Yaa Abun nan komai ba a yi mishi daidai, in nayi magana yace na cika surutu, yanxu kuma Batuul bata yi magana ba zaiyi fada" Tana cikin tunanin taji yace "am i not asking you ?"
"No Yaa Abu bata jin dadi ne shiyasa bata gaisheka ba, Ce mata ya sakeyi "daga ina take"? "Batuul cefa kawata tun muna Centagon wacce ka kaini gidansu a Maitama last year da ka dawo har kace bazan kwana ba",

Hannu ya daga mata alaman ya isa,

"ki miqomin ruwa a fridge", a kan center Table din gabanshi ta ajiye ta juya ta bar falon

D'aki ta nufa, tana shiga ta tarar da Batuul è„¿ tsaye tana riqe da jaka da gyalenta a hannu, "Zan tafi gida"

"Ban gane zaki tafi ba saboda mey" Farida ta tambaya , Yaa Abu yayi miki fada ne dan nasanshi da yiwa mutane fada, "Ni baiyi min komai ba kawai zan tafi ne"

"In kinje toh mey zaki cewa Aunty ya dawo dake bayan kince har dare zaki kai " kuma in Ammah ta dawo mey zan fada mata ? That kinzo har kin koma ? If Yaa Abune baza mu sake bin hanyan da yake ba nima haka yake min

"Toh naji bazan tafi ba amma baza muje inda yake ba " Farida ta kyalkyale da dariya tace,

"Keh da kika ce zaki fada mishi ina gulman shi yanxu kuma ke da kanki zaki qi bin hanyan da yake "

"Ni ki rabu dani, kuma ai ni babu abinda yayi min kuma zan fada mishi din ai", haka suka ci gaba da hira har Batuul ta manta da Abutturab na gidan

Yana zaune a palo bayan ya kurbi ruwan da Farida ta miqo mishi, tunani yayi na lokacin da Baatul ta bigeshi a masallaci da yadda tace mishi sorry har yanxu da ta zo gidansu yaga hawaye a idonta, hawayen da ya tuna ne ya sashi ajiye ruwan yana fadin "Damn it" è„¿ hankali, "does shi always cry"? Yana cikin tunanin yaji an bude kofan palon , Ammah ce tare da Sadiq a bayanta suka shigo suna hira, ciki suka karaso suka zauna a palon, Abu ne yayi musu sannu da zuwa, Ammah ce tace "baku tsaya anyi hawa bane da ku "? "Ehh naso mu zauna sai kuma na fasa amma Abui yana can" , "Muma munje mun duba Ayyi ne, sannan ta kwalawa Fanne kira,cikin hanzari Fanne ta karaso tacewa Ammah "sannu da zuwa,Gani"
"kije ki duba min Farida kice mata mun dawo, sama Fanne ta haura ta fadawa Farida sakon da aka bata sannan ta fita, Farida tacewa Batuul "muje ki gaida Ammah nasan baza ta hawo palon sama ba shiyasa ta sa a fadamin"

"Ni sai kinje kin duba in Yaa Abu baya palo tukunna zanzo"
"Farida tace you are kidding me,taso mu tafi ai in Ammah tana nan bazai yi komai ba" Hannun ta Farida ta jawo suka sauko k'asa, lokaci daya ta d'ago kanta suka hada ido hudu dashi, ta dauke nata da sauri ta karaso cikin falon ba tare da ta kallesa ba suka iso gun Ammah, Farida da gudu ta karasa gun Ammah tana fadin "shine Ammah kuka qi dawowa da wuri inata jiran ku, Ammah bata yi mata magana sai Batuul da ta cewa " A ah Batuul yaushe kikazo, su Aunty na lafiya ? Ashe kunxo, Aunty da mukayi waya tace mayb baza ku zo ba dan Baba na aiki, anyi sallah lafiya ? Batuul da murmushi a fuskanta ta k'arasa wajen Ammah ta zauna daga k'asa sannan tace Alhamdulillah, ta tambayeta ta karfin jiki, "Alhamdulillah Batuul, kun gama karatu lafiya ? Next two weeks zakuyi graduation dinku ko ? Da "Eh" ta amsawa Ammah, Ammah tace "Allah yasa kuyi a sa'a, suka amsa da Amin dukkansu, Sadiq ne ya cewa Batuul "Wane school kikayi applying admission ne , ko har yanxu oxford din zakije ya k'arasa maganan yana dariya, Batuul tace " ban sani ba ko Baba nan yake nema min but if ban samu ba may Baze ko Nile zai kaini dan bayason inyi nisa, Sadiq yace "ai dama oxford makaranta masu ilimine ko da yake ai kema kina da ilimi you can do it", tayi murmushi tace kai Yaa sadiq"

Abutturab na zaune yana kallon TV amma duk hankalinshi yana kansu, tunani yake yaushe ma suka santa and everything about her,wai har Sadiq ma yasan makarantar da take son zuwa, tab'e baki yayi ya ci gaba da kallonshi, Ammah ce ta tashi ta hau sama, yan matan ma suka bita, da ido ya bi bayanta har saidai suka shige ciki

7:20 na dare duka y'an gidan na kan dinning suna dinner,Abutturab ne kadai baya nan Ammah ce ta tacewa Batuul "kwana zakiyi amma ko" Batuul tace "a ah Amma zan tafi yau, yanxu ma Ahmad nake kira baya picking, shi zaizo daukana Ammah tace , "No ai ba sai kin kirashi ba , gasu Sadiq sai su mayar dake bari a gama dinner, Toh kawai tace dan batason yiwa Ammah musu

Abui ne yace "su tafi da Abutturab dan yanxu zamu fita da Sadiq", mik'ewa yayi yacewa Batuul in taje gida ta gaida Baba, tace mishi yayi ta trying number dinshi its not going" Ta amsawa Abui da "Toh" sannan ya ciro rafar kud'i daga aljihunshi yace ga Barka da sallahn ta nan,tayi godiya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.