Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 32 of 124
25
By Phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Tsayawa yayi ya zubawa fuskanta lumshashen idonshi, babu komai fuskanta daga dogon hanci sai lashes 膹inta da suka kwanto a fuskan da 膹an k'aramin baki, ya kai minti biyu yana kallon fuskanta ya ma rasa me yake kallo a fuskar, daga k'arshe ya dan ja tsaki ya tada motar sukayi gida, Batuul kam tunda ta kwantar da kanta bata 膹ago ba, parking yayi da suka isa gida ya kashe motar, jin an tsaida motan ya sata bu膹e idonta a hankali ta dubi side 膹in da yake, maza tayi ta 膹auke idonta don kallonta yake, bu膹e k'ofa tayi zata fita yace mata "wa zai 膹aukar miki maganin", bata kulashi ba ta dawo ta 膹auki ledan magani tayi gaba abinta, 膹akin Ammah ta nufa, a hankali ta tura k'ofan 膹akin tasa kai, babu kowa a 膹akin sai k'anshi dake tasowa ta kowane angle, shiga tayi ta zauna kan gado tare da jinginar da kanta a jikin gado ta lumshe idonta, numfashi take sauk'ewa kamar wacce tayi wani babban aikin, bu膹e k'ofan 膹akin yayi shima ya shigo, babu kowa sai Batuul jingine a gado, k'irjinta na heaving, a zuciyanshi yace "she is lazy, kamar wacce ta 膹auko gari" tabe baki yyi yaja k'ofan ya rufe, falon sama ya tsaya zai k'ira Sadiq ya tambaye shi inda Ammah take, yana ciro wayan ya hango Ammah ita da 膹aya daga cikin masu aikin gidan 膹auke da babban tray suna hawowa sama, sai da suka hawo tukunna ya k'arasa wajen ta yace "Ammah mun dawo", ba tare da kalleshi ba tace "mey suka duba sukace ya sameta", ta fa膹a tare da tura k'ofar 膹akin, sam shi baya jin da膹in yadda Ammah ke yi mishi akan yarinyar nn, binta yayi shima jiki a sanyaye ya shiga 膹akin, trayn hannunta yarinyar ta ajiye ta juya ta fita, sai da ta fita tukunna ya zauna 膹an nesa da Ammah yace "pneumonia ne sukace yana son kamata, sunce ta guji anything cold sai ta rage yawan wasa da ruwa da shan abun sanyu", katseshi tayi da "wane irin ta rage wasa da ruwa, ai dama ba yi takeyi ba, kuma da k'yar aka samu ta rabu da wannan pneumonia tun tana k'arama yake wahalar da ita, sai da aka samu yarinya ta huta zaka sa ya dawo mata, ai da baka sata shiga ruwa ba da babu abinda zai sameta", a hankali yace "Ammah nace kiyi hak'uri fa, bazai sake faruwa in sha Allah, kiyi hak'uri", tana kwance bata bu膹e ido ba tana jiyo duk abinda yake fa膹a, wani 膹an k'aramin murmushi tayi dan taji da膹in yadda yake yiwa Ammah, ashe akwai wa膹anda yake jin maganarsu, "ai dama aikin kenan , da kayi abu ka fara bani hak'uri, k'arfe nawa zakuje gaisuwan iyayen?", sakin murmushi yayi dan ya gano cewa ta hak'ura tunda ta fara wani zancen, ce mata yayi "bayan azahar zamu je, sai dare kuma aje a 膹aukota", "Allah ya kaimu , Su Aunty Amna sai suje su 膹aukota, ba sai kun shiga gidan naka ba ai tunda kwana hu膹u kawai zakuyi ku wuce, tayi zamanta kawai a nan a side 膹inka, kar a bata mata gida, duk ranan da kuka tashi dawowa gidanku ya zamana sabo", yace "hakan ma yayi Ammah, inaso inci abinci" ya fa膹a mata kamar wani k'aramin yaro, tray 膹in ta nuna mishi tace "dama Batuul na sa akawowa, amma yana da yawa zaka iya ci a ciki, Ammah ce ta mik'e ta isa inda Batuul take ta tasheta taci abinci, har kan gadon ta bita da abincin, ta ansa, kasa cin abincin tayi da hankalinta sam yaki kwanciya, shiko ko kallon inda take ma bai yi ba sai abincin shi yake ci suna ta hira da Ammah, a hankali ta 膹an tsatsakuri abincin ta tace ta k'oshi, mik'ewa yayi ya yiwa Ammah sallama akan zaije ya shirya suje gidansu Ajiddeh.
Wayan hannunta ta k'urawa ido xuciyarta na bugawa da karfi ga wani mugun bacin rw da ya baibayeta, gumi yana ta tsatsafo mata, mesa takejin fa膹uwan gaba ne duk lokacin da taji sunan Batuul ko ta ganta, yanxu akan yarinyar nan Aliyu ya katse min waya harda yi min tsawa, danshi taji a fuskanta tana kai hannun taga hawaye a fuskanta, rai a b'ace ta mik'e ba tare da tasan mey zatayi ba, 膹akin Mum ta nufa hawayen wani na bin wani, mata ne sun kai takwas a 膹akin wasu kwance wasu kuma na cin abinci suna hira, ba sallama ta shiga 膹akin tafa膹a jikin Mum, kuka ta saka kamar wacce aka daka, a firgice Mum ta 膹agota tana kallon jikinta taga ko da akwai abinda ya sameta, da taga jikinta lafiya ta tambayeta "meye ya faru haka, mey ya sameki, ko Aliyun ne wani abu ya sameshi", kasa magana tayi sai ci gaba da kukanta takeyi, Yaa zee sake gefe taja tsaki tace "waye kuwa in bashi ba, ai 膹an wulakancin nan nema ko baku tambaya ba", tambayanta kowa ya shiga yi amma ta kasa basu amsa, sai da ta gaji dan kanta Mum na rik'e da ita ta 膹ago tace "Mum kefa kikace idan mukayi aure zai soni fiyeda koma..." bata k'arasa ba Mum ta tareta da cewa "toh meye ya faru yanxu", cikin sheshek'a tace "Mum katse min waya yayi harda min tsawa wai ya kai k'anwar shi asibiti, kuma ba k'anwarshi bace, ni bana son yarinyar nan, duk randa na ganta sai zuciyana ya rik'a fa膹i, har gumi nakeyi, ko a wajen dinner kuna ganin yanda ya rikice wai dan ta ji ciwo, mum na tsaneta wllh", sai da ta gama tukunna Mum ta mik'ar da ita tace mata "mey na yin kuka toh, ba wannan bak'ar yarinyar bace dai y'ar Maryam, mey zaiyi da ita yana da farar mata kamar ki, ko kuma kin tab'a ganin wanda aka yiwa kishiya duk zuri'armu, ai mun fi k'arfin kishiya, duk jarabar mutum sai dai ya rabu damu rabuwar kuma sai ya 膹an膹ani ku膹arsa amma ba dai yace zai shigo da wata matar muna ciki ba, kuma ke 膹innan da kike gani auren mutu ka raba, bare azo zancen kishiya, ki share hawayenki babu abinda zai faru dake", Yaa zee ce ta turo baki tace "Ammah nifa yaron nan bai kwanta min ba, ya rik'a wani huhhura hanci yana kallon mutane 膹ai 膹aya, ni mugun haushinsa ma nake ji", juyowa Ajiddeh tayi cikin rashin kunya tace "ai ni dama bance mijina ya birgeki ba, kinje kin kaso aurenki kin kasa zama a 膹akin miji shine zaki dameni da mijina bai birgeki ba, toh ni a haka nake sonshi kuma babu ruwanki dashi, a fusace Yaa zee ta mik'e tayo kan Ajiddeh kamar zata daketa tana fa膹in "da wa kike, maimaita abinda kika fa膹a yanxu inji in baki da hankali", Mum ce tareta da cewa "Mey kukeyi hakan wai, kuda zaku ha膹u ku rufawa kanku asiri kunkama kuna fa膹a, keh zainab babu ruwanki da mijinta, kema Ajiddeh babu ruwanki da ita" taja tsaki, Jainaba dake gefe itace ta taso ta 膹ago Ajiddeh tace "ke yanxu kukan na meye kikeyi haka, akan dan ya 膹auki yarinyar ya kaita asibiti koko dan taji ciwo ne ya taimka mata kike kuka, share hawayenta tayi tace "Jainaba tun randa na fara ganin yarinyar kawai naji bana sonta, gashi mamarshi sai tayi ta ha膹ashi da ita, haka ranan graduation 膹insu tace wani wai su biyu su tsaya ayi musu hoto, wlhy da na gansu tare sai da zuciyana ya kusa harbawa ga wani gumi da nakeyi kamar nayiwa sarki k'arya duk da sanyin da akeyi, ko jiya da zamuje dinner da ita yazo wai babu motoci a gidan sun k'are duk yawan motocin gidansu amma sai da ta ha膹oshi da ita, haka ma da aka tashi ta tafi yawonta sai da akayi ta nemanta duk sunbi sun 膹agawa kansu hankali, ni wlhy bana sonta", sai da tayi shiru Janaba tace "toh meye alak'arshi da ita?", "ni ban sani ba, kullum ce min yakeyi wai cousin 膹inshi ce, ban san ta ina ta zama cousin 膹in tashi ba, ko a wajen wannan wushe wushen nasu kunga yadda abokanshi suka tsaya yi mata liki kamar itace amaryar, ni in bata dena shiga harkata ba Allah illatata ma zanyi", Mum ce tace "Ai ba wani alak'a na jini bane a tsakaninsu, abotace kawai a tsaksninsu na iyaye tun suna yara", kai Janaba ta girgiza tace "toh ita mamartasa mesa take son ha膹ashi da ita kullum, ko tana son shi ne ya aureta", 膹agowa tayi ta dubi Janaiba da idonta suka rine tace "babu wani, mey zaiyi da ita, kawai dai iko take nuna mishi na ita ta haifeshi dole yayi abinda takeso, kuma ni bata tab'a nuna bata sona ba", "toh ki kwantar da hankalinki, babu abinda zai sami aurenki indai muna raye, ku da zaku bar k'asar ma gaba 膹aya, ki kwantar da hnklin ki kinji", kai ta gya膹a kawai ba tare da tace komai ba, haka suka ci gaba da hiran babu namijin da ya isa yi musu kishiya ko da ta wasa ce, da yadda za ayi da duk wani wanda yayi gigin cewa zai yi dashi da wacce zai auran.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.