Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 43 of 124

34

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Kuka sosai Batuul ke yi kanta kife jikin Anty dake hawayen ita ma, 膹agowa tayi daga karshe jin Anty ta ki cewa komae cikin rawan murya tace "Aunty mesa za a min aure nida ke karatu, mesa Yayya ta matsu inyi aure har tasa Baba ya yadda zaimin ynxu, Aunty dan Allah ki tashi muje ki fa膹a musu banason yin aure, idan basu yrda ba to su canxa min wani mijin ba ya Abuu ba, don Allah Aunty ki tashi mu tafi nasan in kika fa膹awa Baba zai yadda", ganin Aunty ta ki tashi yasa Batuul mik'ewa har lkcn tana kuka tana fa膹in "Nasan in na fa膹awa Baba zai yadda, kullum duk abinda nace mishi yana min, wannan ma zanje in bashi hak'urin ince mishi karatu xanyi...." cikin hanzari Aunty ta mik'e ta tareta ganin tayo baya zata fa膹i, ta fada kanta, sabon kuka Aunty ta fashe da ta shiga girgiza ta ganin jikinta duk ya saki idonta lumshe, sunanta ta shiga k'ira tana cewa "Batuul, Batuul ki tashi kinji, babu wanda zai miki auren nan, wasa sukeyi miki dama, ki tashi yanxu zanje in samu Baba da Yayya ince suyi hak'uri, kiyi hak'uri ki tashi kinji Batuul, babu mai sake saki kuka, ki tashi muje tare Batuul", Batuul kam ko motsi batayi sai dai har lkcn hawaye na tsiyaya daga idanunta, wani ihun Aunty ta sake sawa tana jijjiga ta, bu膹e k'ofan 膹akin akayi su Ahmad suka shigo jin ihun Anty, cirko cirko suka tsaya ganin kan Aunty kife jikin Batuul tana ta Kuka, da k'yar ya iya yin k'arfin hali ya ja k'afanshi ya k'arasa inda su Aunty suke, tsugunawa yayi dab da Batuul ya rik'o hannunta, 膹ayan hannun kuma ya 膹aga Aunty, cikin sanyi yace "Aunty ciwon kan nata ne har yanxu", kasa bashi amsa tayi sai hawayen dake ta zuba daga idonta, juyawa yayi ya dubi sauran k'annen nashi da har lkcn sun kasa motsi suna nan inda suke sai hawayen da suma suka fara har y'an k'ananan yace "kuje ku k'ira Baba, yana 膹akin Yayya", ya juya yaci gaba da murza hannun Batuul yana 膹an jijjigata, ba a fi minti biyu ba da fitansu Baba ya shigo 膹akin yana tambayan tana ina, ganinta kwance jikin Aunty ya kasa magana, sosai jikinshi yayi sanyi, yasan duk yadda akayi kan maganan auren nan da taji ne ya dameta, Bai sake cewa komai ba sai da ya sunkuya ya 膹auketa cak sannan yacewa Ahmad, "膹auko key mu tafi asibiti", a bakin k'ofar 膹akin suka ci karo da Yayya tana tambayar "meye ya faru wai, inata magana ja'iran yara kun qi kulani kun zuba min idanuwanku kamar na mujiya", ido ta wara ganin Batuul hannun Baba tasa ihu tana cewa na shiga uku ni Zara'u, mey zan gani haka, meye hakan wai kunyi min shiru, mey ya sameta, baza kuyi min magana ku fa膹amin mey ya samu Batuul 膹in ba", babu wanda ya kulata a dakin, gaban Aunty ta k'araso tace "Maryam bafa nason wulak'anci, mey kuka yiwa Batuul 膹in ina tambayanku kika min shiru, mayafi Aunty ta 膹auka ta yafa tabi bayan su Baba ko kallon inda Yayya take batayi ba, tasan indai ta bu膹i baki toh kowa bazai ji da da膹i ba dan ranta yayi k'ololuwar b'aci, hanyan Nizamiye hospital Ahmad yabi dan nan ne family hospital 膹insu, har lokacin bata farfa膹o ba, suna zuwa cikin gaggawa aka karb'eta akayi emergency da ita, har lokacin babu abinda Aunty take sai kuka da addu'a Allah ya bawa y'arta lafiya, Abuturrab kam xaga gari yyi ya koma gida Karfe tara saura ya shige daki yyi kwanciyarsa.

Washegari kamar yadda Ammah tayi alk'awari, k'arfe biyu ta shirya tayi gidan Yaa Mera, da driver ta tafi dan so take ya jirata su koma, a falo ta tarar da ita zaune ta mik'e k'afa dogaranta mata biyu na mata tausa, sallama tayi ta sa kai cikin 膹akin, da fara'a ya Mera ta tashi ta yiwa y'an matan alaman su wuce, kansu a k'asa suka gaida Ammah sukayi waje, waje ta samu daga palon ta zauna tace "Maryam wannan gidan naki da tafiya yake, dubi duk na gaji", murmushi tayi tace "kai Yaya, ai babu wani tafiya kawai dai kin da膹e ne baki zo ba", biyu 膹aga cikin y'an matan da suka fitane suka shigo 膹auke da manya tray 膹auke da fruits, abinci, sai nama iri iri, direwa sukayi suka koma daga waje, Yaa Merace ta fara magana "jiya kawai sai ga Babana, nayi mamakin ganinshi, shine yake cemin wai yayi sati ma", ruwan dake kan tray ta 膹auko ta ajiye gefenta sannan tace "ai yanxu ma zuwan nan dan shi nayi, auren Mustapha nan da sati biyu kenan ko, toh inaso a ha膹a ayi da na Abutturab, dan matar nan tasa bazan zauna in zuba mata ido su cutar min da 膹a ya zama mara amfani ba", ido Yaa Mera ta wara tace "Yaya aure Babana zai k'arayi, yaushe? kuma wa zai aura?", kai ta girgiza tace "Maryam auren ne kawai zai min maganin halin nan da yake ciki, yaro gaba 膹aya ya zama bashiba, shine nayi magana da Babanshi ya nema mishi auren Batuul, so nake ma a ha膹a da na Massa tunda saura sati biyu, in yaso sai ya koma bakin aikinshi da ita, dan yarinyar na da nutsuwa, kamar jinina nake jinta", kallonta Yaa Mera ta tsaya yi tace "Yaya badai Batuul 膹in Maryam ba?", kai ta ka膹a tace "k'warai kuwa ita", tace "toh Yaya ai na Massan ma jiya Babanshi ke cemin wai sun 膹an 膹aga, sun k'ara wata 膹aya dan Mamar yarinyar bata jin da膹i, yanxu haka an fita da ita waje, Amma Yaya baku tunanin ko Batuul nada wanda takeso, ko kunyi magana da iyayenta sunce bata da kowa, dan kar azo a shiga hakkin yarinya", Ammah zatayi magana kenan wayanta ya shiga ringing, 膹auka tayi taga Farida ke k'iranta, recieving tayi tasa a kunnenta tace "Farida ya akayi", cikin shesheka tace "Ammah Batuul", cikeda da damuwa jin ta ambaci Batuul kuma tana kuka tace " Batuul kuma, mey ya sameta", cewa tayi "Ammah tana kwance a asibiti bata da lafiya, tun jiya she is still unconscious tun.....", Ammah bata bari ta k'arasa ba tace "Farida, kina jina, kije ki samu Abu kice mishi maza ya tashi ku tafi asibitin tare, nima yanxu zan wuce daga nan", maida kukan nata tayi tace "toh Ammah", suna gama waya ta mik'e tace "Maryam kinji, Batuul din ma ba lafiya tana kwance asibiti, yanxu gunta zani in duba ta", bakin k'ofa Yaa Mera ta rakota tayi mata sallama tace Allah ya bawa Batuul 膹in lafiya ta gaisar mata da Anty, itama zasu zo dubata idan mijinta ya dawo, da haka sukayi sallama akan zasuyi waya.

Hijabi kawai Farida ta 膹aura kan top da wandon dake jikinta tayi 膹akin Abutturab, knocking tayi taji bai amsa mata ba, bu膹ewa kawai tayi ta sa kai, wani sanyi ne ya ka膹a har cikin jikinta duk da hijabin dake jikinta, kai ta 膹aga ta dubi Acn 膹akin nashi taga yana lowest temperature, k'arasawa tayi daga ciki ta 膹au remote 膹in ta kashe Acn gabaki 膹ayanshi, yana kwance kan gadonshi rigingine ya 膹aura hannunshi kan goshinshi idanunshi lumshe kamar mai bacci, a hankali ta k'araso cikin 膹akin ta zauna daga bakin gadon, sunanshi ta shiga k'ira taji bai amsa mata ba, sarae tasan kuma idonsa biyu, ce mishi tayi "Yaa Abu Ammah cefa tace inzo in fa膹a maka ka shirya mu tafi asibiti", jin ta ambaci asibiti ya sashi bu膹e idonshi dake lumshe ya zuba mata su, bai tashi ba yace "waye ba lfya?", a hankali tace "Batuul ce bata ji da膹i tun jiya, shine.....", wani tsawa ya daka mata, "tashi ki fita", a gigice ta mik'e sai da taje bakin k'ofa ta juyo tace mishi "Yaa Abu Ammah cefa ta aikoni", wani harara yabita dashi, ba shiri ta saki k'ofan tayi waje, tana fita ta k'ira Ammah ta fa膹a mata yadda sukayi da Abutturab, ran Ammah ba k'aramin b'aci yayi ba ta katse wayan ta shiga neman numbershi, jin wayanshi na k'ara ya janyo wayan, ganin mai k'iran yasashi saurin tashi zaune yayi recieving, yana 膹agawa Ammah ta fara magana "Abu kana jina, bana son shashanci, in aiko yarinyar ta fa膹a maka sak'ona shine zaka korata, toh yayi maka kyau, ina kan hanyan zuwa asibitin, ka tabbata kamin in isa kana can", tana kaiwa nan ta katse wayan, ji yayi gaba 膹aya kanshi na sara mishi, mesa Ammah baza tayi understanding 膹ina bane, mik'ewa yayi ya 膹auki key 膹in mota ya sauk'o k'asa rae ba ddi, a palo ya tarar da Farida zaune tana ta jimamin rashin lafiyar k'awarta, tana ganinshi ta mik'e, harara yabita dashi ya fita waje a fusacd, yana tafiya tabi bayanshi a ranta tana tausayin halin da k'awarta zata shiga in ta auri masifaffen nan, sai da ya shiga motar tukunna itama ta shige, bayan ya fita daga gidan ne ya tambayeta asibitin ba tareda ya 膹ago ya kalleta ba, fa膹a mishi sunan asibitin tayi daga nan ya 膹au hanya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.