Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 28 of 124

Allah Allah ta rik'ayi su isa inda zasu ta rabu dashi, gashi ya wani hade rae wane hadarin kaji, ko kwakkwaran motsi ta kasa a motar, mistakenly idan ta kallesa kuma ya xabga mata harara, gate 膹in gidansu Ajiddeh ya shiga dan a bu膹e yake kasancewar ana biki, wasu motocin sun samu sun shigo, wasu kuma na daga waje, parking yayi, y'an mata ne dayawa duk sunsha kwalliya sunyi kyau, wata ce daga cikinsu ta iso inda motan Abu yake, tace "ango muna ta jira har amarya ta gaji da jira", a takaice yace "Ae gashi nazo 膹aukanta, kuyi mata magana, ko kuma bari in k'irata ta fito", harara tabi Batuul da ganinta a gaban Motan Abutturab, sae kuma tayi dariya tace "No bari inje in fito da ita dan nima yanxun daga wajenta nake", ta juya ta tafi, Massa ne ya fito yacewa sauran y'an matan suzo su shiga motocin kamin amaryar ta fito, a hankali take takowa, tun daga nesa ake ganin kyan da tayi, kayanta sai walwali suke saboda hasken dake wajen, tana k'arasowa wajen motan ta tsaya tabi abinda take kallo cikin motan da ido, bu膹ewa yayi ya fito tare da cewa Batuul "get back" a hnkli ta bu膹e k'ofan motar tayi ta fito, wani irin Kallo Ajiddeh tabi Batuul dashi baki bude, Batuul bata ma san tanayi ba ta bu膹e gidan baya ta shige, zagayowa yayi ta gabanta yace "wifey" yana kallonta tare da bu膹e mata k'ofan, wani irin kallo ta sakar mishi tace "Aliyu mey haka?, wane sabon wulak'anci ne kuma wannan, ya zaka zo 膹aukana zamu tafi dinner sai kazo da wata, motan nan fa musamman mukayi order saboda in shiga ranan nan shine ka 膹auko wata a ciki", shiru yyi yana kallonta sanin gskya ta fada, hannunta ya kamo ya wara mata manyan idonsa yace "c'mon its your happy day, meye dan wata ta shiga, Batuul cefa ba kowa ba, my cousin sis bbu motar da xata shiga ne shi sa Ammah tace in daukota nima ba a son raina ba coz ke naso ki fara shiga motar", a fusace tace "ai nasha fa膹a maka ni bana son yarinyar nan, wlhy hankalina baya kwanciya duk inda na ganta, kuma ya xaka yrda ta biyoka bayan ga motoci da drivers a gida", Iska ya furzar daga bakinshi a fusace yace mata "get in, in kuma baxa ki shiga ba ki koma gida" yana kai wa nn ya zaga mazauninshi ya zauna, sai da taga dama tana cika tana batsewa sannan ta shige motan, yana fita sauran motocin suka bi bayanshi , a conference hall akayi dinner, suna shiga mutane duk sun hallara, shi da kanshi ya fito ya bu膹e mata k'ofa ta fito tana ta b'ata rai tana cin magani, Aunty Amna ta fito ta samesu tace k'annen ango ne zasu shigo da amarya, tsayawa Ajiddeh tayi tana jiran taga su waye k'annen Aliyun da zasu shigo da ita, a hankali Batuul ta fara 膹ingisa k'afarta zata shiga hall 膹in, Aunty Amna ce ta tsaida ita, Batuul tsaya ku shiga da amarya, Farida na fitowa, tana gama rufe bakinta Farida ta fito, su suka tsaya a gaban amarya ka膹an , Batuul a hannun hagu, Farida daga hannun dama, sai Abutturab daga gefen Farida, ki膹a ne ke tashi a hall 膹in kowa yy kyau ssae, sae da suka shigo hall din Batuul tayi tuntub'e don dama 膹ingisa kafan takeyi, kan ta kai kasa Abutturab yayi maza ya rik'ota, shiru hall 膹in yayi kowa idonshi da hankalinshi yayi kansu duk da basu karaso ciki ba gaba daya don da yawa sunyi xaton amaryar ce ya rike, xame jikinta tayi daga rikon da yyi mata ta karashe durkusawa wajen tana runtse ido hade da yarfe hannu, yana gnin hka shi ma ya bita ya durkusa da sauri yana kallon kafar yace "What?" Hawaye cike idonta tace "Na buge ciwona" Anty Amna ce ta taho da sauri don gnin abinda ya faru, Farida ta xaro ido tana kallon ikon Allah, Ajiddeh kam still tayi a wajen xuciyarta na bugawa da karfi. 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

23

By Phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Tunda ya rik'eta masu hotuna ke ta 膹aukansu hotuna dan sun zata amaryarce, Ammah dake zaune can gaba tana hango lokacin da suka shigo har lokacin da Batuul ta bige ciwonta, a ranta taji inama Batuul 膹anta ya aura, dan tana son yarinyar, tunanin cewa matar mutum kabarinsa da tayi ne ya sata kawar da zancen tayi musu addua zaman lafiya, Aunty amna ce ta k'araso da sauri ta rik'e k'afan Batuul 膹in, babu abinda Batuul ke yi sai yarfe hannu, hawaye na ta zubowa 膹aya na bin 膹aya, 膹agowa Abuturrab yayi ya dubeta yaga yadda hawayen ke zuba, ya hade rae yace "cmon shut up, mey aka yi miki kike ta wani kuka kamar yanxu kikaji ciwon, clean those tears ynxun nn", ya fa膹a yana kallon idonta, sauri tayi ta kawar da nata idon daga dubanshi, Aunty Amna ba tare da 膹ago ta dubeshi ba tana rik'e da k'afan tace "kai fa mugune Abuu, yarinyar tazo yi muku abin kirki taji ciwo shine zaka fara mata fa膹a, akan wane dalili, ka rabu da ita ka kama matar ka ku shiga ciki", Farida ce tace "Aunty Amna mu maidata gida mana in baza ta iya tafiya ba", shi dai bai tafi ba kuma bai ce komai ba yana tsaye a kansu, Sai da Aunty Amna ta 膹ago ta dubeshi sannan ta sake ce mishi "Abu kama matarka ku shiga ciki mana, zan kula da Batuul," sai da ya sake kallon fuskanta dake ta ambaliyan hawaye tukunna ya ja 膹an k'aramin tsaki ya juya ya dubi Ajiddeh, tana nan a tsaye kamar ta kurma ihu dan takaici sae wani xufa take, hannunta ya rik'e sannan yace mata "wife muje ko", wani k'ululun bak'in ciki ne ya sake kamata, duk b'ata mata lokacin da yayi bai gani ba bare ya bata hak'uri shine ya wani rik'e mata hannu wai suje, ji tayi a wajen kamar tace ta fasa dinner amma sanin halinshi zai iya cewa ta tafi kawai ya sa ta bishi kmr Wanda aka xare ma laka, tana tunanin yadda zatayi da wannan yarinyar da yake ikirarin cousin 膹inshi ce, dan tana sonshi kuma bata son ganin kowace mace ta rab'eshi ko da y'ar uwarshi ce, kae da ba dan in ta kasheta dole sae an hukuntata da gwara kawae ta daba mata wuka ta huta, da tunanin nn a ranta suka k'arasa MC na ta ko膹a su a wajen nan, sae dae Sam fuskarta bbu annuri xufa kawae take yi, Ammah ce ta k'ira wayan Farida dan duk hankalinta na kansu tace mata su shigo da Batuul 膹in ciki, haka kuwa akayi , Aunty Amna da Farida su suka taimaka mata ta mik'e suka shiga hall, daga gaba wajen su Ammah ta zauna, Aunty na daga gefenta, tunda ta amsa gaisuwanta bata sake ce mata komai ba , bare ta tambayeta yadda akayi taji ciwon, MC ne ya fara magana da k'iran mai bu膹e taron addua, Aunty ya k'ira, she wasnt expecting it amma tunda aka k'ira ta tasan girmamata sukayi, tashi tayi taje tayi musu addu'a tare da fatan samun zaman lafiya da xuri'a dayyaba, data gama aka bi ta addua, daga nan aka k'ira abokin ango da k'awar amarya suzo su fa膹i biography 膹in couple 膹in, Massa ne ya fitowa Abutturab, ita kuma Ajiddeh k'awarta da taje k'iranta da Abutturab yazo 膹aukanta ce ta fito, suna gamawa aka fara sauran events 膹in, sai da akazo yanka cake ne aka k'ira iyayen amarya da ango, Ammah cewa tayi baza taje ba , Aunty da Yaa Mera suje kawai, haka kuwa akayi, daga nan aka fara rawa, ita dai Batuul tana nn inda take zaune, sai dai in daga ido taga idon Abutturab a kanta, da sun ha膹a ido kuma ya zabga mata harara, haka ma Ajiddeh da in ta maka mata wani hararan sae ka rantse kace idanuwanta xasu zaxxago, Batuul kam sae dae ta tabe baki a xuciyarta tace kwa ji da shi daga ke har mijin naki, daga yau ma ba lallai ku kuma ganina ba bare ku harare ni" ko lik'in ma kin tashi tayi ta musu, a haka dai har a gama dinner lafiya aka tashi komawa gida,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.