Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 23 of 124

Yana barin wajenta ta sauk'e ajiyar zuciya, 膹azu a wajen lik'in nan taji an k'irashi da Massa, da ma shine, tab'e baki tayi a ranta tace toh wannan ne prince , ai surutunshi yayi yawa, dama Abutturab 膹in ne prince zai fi dan shi yafi ji da kai, ku kuka sani dai, dama sune take ganin pictures 膹insu a album 膹in gidansu suna yara , baki ta tab'e tace ku kuka sani dai,

Mik'ewa tayi daga indactake zaune ta isa wajen Aunty, marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace "Aunty, ciwon kan 膹azun fa ya dawo, insaso in je gida", dubanta Aunty tayi sannan tace "baki sha magani bane 膹azu", da sauri ta ka膹a kai, "nasha, mayb effect 膹inshi ne ya sakeni, inaso in sake shan wani", Aunty bata sake cewa komai ba ta 膹aga waya ta k'ira Ahmad, yana amsawa tace "ga Batuul nan zaka kaita gida, kanta na ciwo", bayan ta katse wayan ta cewa Batuul "ki tashi ku tafi, Allah ya sauwak'a, in kuma zaki iya ku bi ta asibiti Dr zaka ya dubaki", cewa tayi "toh Aunty bari muga idan na sha na yau 膹in bai yi ba sai mu tafi gobe ya dubani", da haka ta mik'e tayi hanyan waje, a bakin k'ofa tazo zata fita shi kuma zai shigo suka kusa bugewa, matsawa tayi da sauri kar ya bugeta dan taga ranshi duk a b'ace, tsayawa yayi kallonta har sai da ta wuce, Massa ne da ya ganta ya fara smiling, "Cutie ia zuwa", sunan da yaji ya k'irata dashine yasa shi saurin juyowa, tsayawa yayi yaji mey zatace, a hankali kamar mai ra膹a ta ce mishi "kaina ne yake ciwo za a mayar dani gida", baiji mai tace ba, haushi ya sake turnuk'e shi yaja tsaki ya shiga ciki, tsakinshine ya jawo hankalinsu suka dubeshi, su sunace ma ya tafi, da damuwa Massa ya dubeta "let me drop you mana", "No brother na yana jirana shi zai kaini, nagode" tace ta juya ta bar wajen bata sake ce mishi komai ba, a mota ta tarar da Ahmad yana jiranta, bu膹ewa tayi ta shiga ta zauna, with concern yace mata "sannu Yaa Batuul", ta amsa da "yawwa muje", dan so take ta bar area nan gaba 膹aya, rage Ac motar yayi sanan ya tada suka tafi

A kujera ya tarar da Ajiddeh ta cika tayi fam, yana zama ta dubeshi tace "Aliyu dama wushe wushen naku kenan, muzo a wulak'anta mu", tunda ta fara magana bai ce mata komai ba sai da yaji ta ambaci wulak'anci, katseta yayi tareda da tambayanta "wulak'anci mey aka yi muku", "ehh mana wulak'anci mana , dubi fa yadda abokanka da yan uwanka suka dinga yiwa bak'ar yarinyar nan lik'i kamar itace amaryar, da kunsan ita kuke son yiwa lik'in kaje ka aureni, ai da an aura maka ita sai kuji da膹in yi mata lik'in da kyau, wani kallo ya bita dashi da ya sata ha膹iye magananta da sauri, "mey ke damun kankine wai, wa yace miki ana fa膹a min ko wane irin magana, ba ni ba ko mutum dake kusa dani bana yadda a fa膹a mishi magana anyhow bare ni da kaina, da kike cewa a aura min ita ai da naso tare za a ha膹a min dake akai min ku ko kuma in fasa nakin in aureta, sai ki rik'a yin magana kamar yarinya, jibi ne 膹aurin aurenmu inma zaki gyara tun wuri ki gyara dan bazan yi tolerating shit 膹innan a gidana ba, you have change", ya fa膹a yana mai kallon agogon hannunshi, duk maganan da sukeyi a hankali suke yin shi kamar masu yiwa junansu hiran soyayya

Batuul na isa gida ta hau sama, wipes ta 膹auka ta goge abinda ke fuskanta sannan ta shiga tayi wanka tayo alwalar isha ta hau abin sallah, tana idarwa ta cire hijabin jikinta ta ninke shi ta ajiye a gefe, ko hula bata 膹aura akanta ba ta sauk'o k'asa dinning dan yunwa takeji, kwanukan wajen ta shiga bu膹ewa, plate ta jawo ta 膹ebi white rice da stew sai potato salad, 膹akinta ta tafi da abincin sannan ta zauna taci a a nutse, tana gamawa ta bu膹e fridge 膹inta ta 膹auki ruwa tasha, sai da ta gama abubuwan da zatayi tahau gado ta yi addua ta kwanta, bacci nebmai nauyiya 膹auketa, can cikin bacci wajen k'arfe goma sha 膹aya ta jiyo murya kaman na Farida, a hankali ta bu膹e idonta taga Farida tsaue kanta da wannan wide smile 膹in nata tana kallonta, ta kunna hasken wutan, Aunty ce ta shigo 膹aki tana tambayan Farida "tayi bacci ko, watak'ila kan ne ya 膹an saketa", ganin Batuul ta farka ne ya sata cewa "ya kan Batuul, yayi sauk'i", a hankali tana goge ido tace "ehh Aunty yayi sauk'i nasha analgesic ", da Masha Allah ta ta amsa sannan tace mata "Allah ya k'ara lafiya" tayi musu sai da safe ta fita, kallon Farida Batuul ta tsaya yi, "You didnt tell me you were coming over", baki Farida ta bu膹e da mamaki tace "toh ko in koma ne, wannan tambaya haka da ake jeho min", bata cewa mata komai ba taja bargonta ta rufe kanta ta kashe wutan daga gefen gadonta, Dariya Farida tayi bata ce mata komai ba sai da taje tayi wanka tayi sallah ta canja kayan bacci, wutan 膹akin ta sake kunnuwa tayi tsalle ta hau gadon, Mik'ewa Batuul tayi ta dubi Farida tace mata "meye matsalanki wai", tashi Farida tayi daga kwance da take tace "my problem is i love you so much", tsaki Batuul taja zata koma ta kwanta ta farida ta janyota "kinsan na fa膹a miki dama gida ya isheni, wait ma, keh da na barki kina yiwa ango lik'i sai nemanki nayi na rasa, Allah kinga yadda kika yi kyau a wajen kamar kece amaryar sai lik'i ake miki , ko amarya ma ba ayi mata ba, Yaa Massa ne ya fara miki ai ko sunace kece amarya har Pounds an zuba miki, mehn i enjoyed that part", "Allah Farida ke ko, yanxu dan wannan kika tada ni, Allah ya shiryaki", wayanta ta jawo ta k'ira Affan, yana 膹agawa kamin yace komai tace "Bestfriend com and carry your girl, tun 膹azu take damuna ta hanani bacci", ce mata yayi "bata wayan, mik'awa Farida yayi, zama tayi tana jira ta gama wayan, amma har bayan minti talatin basu gama ba, da taga basu da ranan gamawa ne ta jawo bargonta ta kwanta
[8/22, 1:52 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

20

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Bayan Aunty ta duba Batuul, 膹akinta ta koma ta tabbatar su Yusra sunyi bacci, addua tayi musu ta tofesu dashi gaba 膹aya jikinsu sannan ta tofa a duka angles 膹in gidan, toilet ta shiga tayi wanka sannan ta fito tayi sallah, sai da ta idar ta gama addu'o'inta sannan ta mik'e ta cire doguwar rigar dake jikinta, ninkesu tayi sannan ta 膹auko kayan baccinta doguwar riga har k'asa, yellow silk mai flaps biyu ta saka, turare ta shafe jikinta dasu sannan ta nemi hula ta saka a kanta, k'asa ta sauk'o ta k'arasa kicin ta tsiyayo fresh orange juice a cup ta 膹aura a kan k'aramin serving tray ta haura sama, da sallama ta shiga 膹akin Baba, yana zaune a kan gado da farar jallabiya idonshi da glasses yana rik'e da ipad, da alama aiki yake, 膹agowa yayi ya kalleta cike da Kulawa sannan ya amsa sallamarta,har ta k'araso ciki, a bakin gadon ta zauna sannan ta ajiye juice 膹in a kan bed side drawer, dubanshi tayi itama da kulawa tace "uncle sannu da hutawa, ya dare", bai 膹ago daga kallon da yakewa ipad 膹in ba ya ansa da "Alhamdulillah", sai da ya amsa sannan ya ajiye ipad 膹in a gefe ya juyo ya dubeta yace "Ya gidan biki", cike da natsuwa Aunty ta amsa da Alhamdulillah, amaryar tashi ma mai kyau, Allah ya basu zaman lafiya", Amin Baba ya amsa da sannan yace "nima 膹in sai jibi zan tafi , 膹aurin auren 11 ne, by nine zanbi flight sai mu dawo a ranan", "Allah ya kaiku lafiya, ya dawo daku lafiya, su kuma Allah ya basu zaman lafiya", a tare suka amsa da "Amin", a hankali ta sake cewa "uncle", bayan ta mik'a mishi cup 膹in juice, kurb'a yayi ka膹an sannan ya juyo bayan ya ajiye cup 膹in yace "Maryam, ya akayi ne", a hankali ta 膹ago ta dubeshi kamar bata son magana tace, "uncle dama karatun Batuul ne, kwanaki da sukayi graduation tace min inyi magana da kai akan karatunta, wai in baka hak'uri ka barta ta fita waje, dama kunyi magana ne da ita kace baka son zuwan nata waje?", cewa yayi "Allasarki mamana, eh munyi maganan da ita na ce mata tayi hak'uri da wajen nan , ta zab'i duk inda takeso a nan Nigeria zan kaita, "toh uncle mey zai hana a kaitane tunda munsan Batuul mun san hankalinta, am sure zata kula da kanta da mutuncinta, baza mu samu matsala ba in sha Allah", glass 膹in dake idonshi ya cire ya dubi Aunty sannan yace "Maryam, nafi kowa son ganin na bawa Batuul abinda takeso a duniyan nan, amma bazai yiwu ba, wannan zuwan da mukayi Maiduguri sallah Yayya ce min tayi indai Batuul zata fita waje karatu toh sai da miji, ni kuma ban shirya yiwa Batuul aure ba, tayi k'arama da yin aure shiyasa nace gara in nemo mata makarantanta a nan gida tunda ita Yayyan cewa ma tayi ko a gidan ne sai an mata aure, toh yanxu bakinta nake son rufewa in bar Batuul a gida tayi karatunta dan ta dage sai anyi mata aure", kallo kawai Aunty ke binshi dashi, cewa tayi "aure kuma uncle, nawa Batuul 膹in take da za a fara mata zancen aure, ko 17 fa bata cika ba uncle, yaushe za a fara sata a lissafin aure, tayi zamanta a gida tayi karatunta, zan bata hak'uri tayi a gida, in yaso sai taje ko da msc 膹inta ne a waje, by then zan yadda da aurenta", sai da tagama Baba yace "Allah ya tabbatar mana da alheri , ya zab'a mata abinda yafi alheri", ta amsa da "Amin", mik'ewa tayi ta 膹auke cup 膹in da Baba yasha juice 膹inshi da ta kai k'asa ta dawo sama ta kashe musu wuta suka kwanta, tunanin maganan da suka gama yi da Baba ta rik'a yi, addu'a tayi daga k'arshe ta shafa ta kwanta ta barwa Allah komai

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.