Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 34 of 124
Alhamdulillah, a nn xan dakatar da rubuta littafin *Batuul* har xuwa bayan Ramadan idan Allah ya Kai mu da rae da lfya. Duk Wanda na bata ma knowingly nd otherwise, ya yafe min ni ma na yafe masa from the bottom of my heart, Allah Ubangiji ya karbi ibadunmu a wnn wata mai girma, ya sa mu cikin 'yantattun bayinsa don son ma'aiki S.A.W.
Ramadan Kareem fanz.
Urz *Phartiemarhk*
[8/22, 1:59 PM] .: 馃挅馃æŒBATUUL 馃挅馃æŒ
26
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
A YEAR AFTER
K'aran Alarm ne ya cika dakin gaba 膹aya, kwance take tana bacci har sai da K'aran ya kusa katsewa tukunna taja tsaki, ta Janyo wayar da k'afarta, ko kallon fuskar wayar bata yi ba ta saka hannu ta katse karan tukunna ta maida wayan, duk abin nan da tayi bata bude ido ba, sai da ta mike ta zauna daga bakin gadon tukunna ta bu膹e idonta a hankali wayar ta sake 膹auka taga 7:09, tafi minti biyar a zaune daga bisani ta mik'e tana fadin "mutum da kanshi zai saka abinda zai dameshi", gashinta ta tattare ta ha膹e su waje 膹aya, ta isa inda bathrobe dinta ke rataye ta cire kayan baccin dake jikinta ta saka bathrobe din ta shige toilet, sai da tayi brush tukunna tayi wanka, gaban mirror ta zauna bayan ta fito daga wanka ta shafe duk jikinta da mai,ta fesa body spray tukunna ta je saka kaya, closet dinta ta bu膹e ta ciro wata coffee abaya mai Babban hannu da adon milk daga jiki, sai da ta saka kayanta tukunna tayi inda jakunkunanta ke rataye ta jawo d'aya daga ciki ta zuba tarkacenta a ciki sannan ta yafa gyalen abayar a kanta sannan taje ta saka slippers din Laura Ahman shima milk, har ta fita ta tuna da key 膹 in mota da wayarta ta koma cikin hanzari ta 膹auko lokacin 8am daidai, k'asa ta sauk'o babu kowa a gidan shiru, ta tasan kowa ya tafi makaranta, Aunty da Baba kuma mayb suna bacci, ta nufi dinning area, sai da ta bubbu膹e duk kwanun dake dinning din tukunna ta 膹auki soviet ta 膹auki sandwich 膹aya a cikin wani transparent bowl, ta 膹auki disposable cup ta tsiyayi fresh orange juice a juice dispenser, har ta zauna zata fara ci taga time zai k'ure maza ta mik'e ta yi hanyan waje , sai da ta taje dab bakin k'ofa zata fita Taji muryan Aunty a zaune a parlour tana ce mata "sannu Batuul , kin kyauta , cin abinci a waje ko ? Nasha fada miki banaso babu kyau shine kika wani 膹auki sandwich a paper kamar wacce ta rok'o toh yayi miki daidai", sai da Aunty ta gama maganan da takeyi tukunna ta juyo da murmushi a fuskanta ta dubi Aunty tana k'arasowa cikin parlour ta ce "Aunty Nda wattu, nifa banma San kin tashi ba, Ina kwana" ta sake maimaitawa bayan ta zauna kusa da Aunty, Da lafiya Aunty ta amsa mata sannan tace "Batuul ba kya Jin magana ko" Da sauri Batuul ta girgiza kai tace "Aunty ba haka bane fa, har na zauna zanci naga time ya kusa k'urewa zanyi latti shinefa zanje mota dashi , bama a layi zanci ba fa" ta gama maganan tana sadda kanta k'asa dan tasan Aunty ta hanata, Sai da Aunty ta dubi hannunta taga ma abinda ta 膹auka din tukunna tace "mota ba layi bane ko ? Ai cikin gidane, kuma waye ya hanaki tashi da wuri har kika kusa lattin ke da ba sllh kike ba bare ace baccin asuba kika koma kika makara, kin wani 膹auko Sandwich 膹aya kamar wacce ta rok'o" ganin fa膹an baya k'arewa kawai ta fara cin Sandwich 膹 in tana tunkud'awa, haka ta gama ci tana kurb'an juice 膹 in har ta gama, mik'e wa tayi zataje ta ajiye sauran juice da ta rage, dama tunda ta fara cin abincin Aunty bata kalleta ba sai da ta gama ta mike tukunna ta dubeta tace "sauran Juice din kuma fa? wa kika ragewa" marairaicewa tayi tare da da juyowa tace "Aunty na koshine zanje in ajiye", "Da kinsan bazaki iya shanyewa ba kika 膹ebo dayawa, dawo ki zauna ki shanyewa shi", haka ta dawo ta zauna ta shanye a ranta tana addu'a Allah yasa bata yi latti ba, bayan ta gama shanyewa a dustbin ta jefa cup din da tissue ta dawo tace "Aunty zan tafi" 膹agowa tayi ta kalli Batuul tace "A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a" ta amsa da Amin ta wuce, har taje bakin k'ofa Aunty ta sake k'iranta "Batuul", juyowa tayi tare da cewa "Na'am Aunty", "What time zaki gama lectures" Aunty ta tambayeta, "10:30 zan gama, class 膹aya dani yau, by 11am zan dawo", "okay in kin gama inaso kije ki gaida Ammah, jiya munyi waya tana tambayana ke, so ki wuce daga can sai ki dawo da yamma" toh kawai tace ta fita, Parking area ta nufa taga 膹aya daga cikin masu aikin gidan na goge motar, farar BMW, k'arasawa tayi wajen motan tana laluben makulli daga cikin jakan, 膹agowa tayi bayan ta samu makullin ta amsa gaisuwan da mai aikin ke mata "Yauwa Friday sannu da aiki" ta danna button din motar, kamar jira yake dama tana dannawa ya bu膹e mata, sai da ta shiga ta zauna tukunna ta ciro 膹ari biyar ta mik'a mika mishi, murna ya dinga yi yana mata godiya, murmushi kawai tayi ta jawo motar ta ta tafi, a bakin gate ma sai da ta mik'awa masu gadin 膹ari biyar biyar tukunna ta fita daga gidan, a wajen wani traffic ta tsaya tana jira a basu hannu su wuce, wani super tint AMG ce ta tsaya daga gefenta nata, bata kalli motar ba saima wayarta da ta 膹auko daga 膹ayan kujeran zata duba time, jiya tayi kamar ana kallon ta ta gefe, a hankali ta juya ta dubi gefenta, k'irjinta ne taji yayi dam , wani mugun fa膹uwa gabanta yayi, sosai ta tsorata da mutumin dake cikin motar dan wani irin kallo ya tsaya yana yi mata, sunan Allah ta shiga jerowa tare da fatan traffic 膹 in ya basu daman wucewa ta wuce, bata sake k'ok'arin kallon gefen ba, a haka traffic 膹 in yayi signalling 膹insu da su wuce, a guje ta figi motar kamar mai shirin tashi, Sai da tayi nisa sosai tukunna ta 膹ago ta rear mirror ta duba ko mutumin na binta a baya amma bata ga alaman motanshi ba, wani ajiyan zuciya tayi tare da fa膹in Alhamdulillah a fili, 8:34 daidai ta isa school, dpt dinsu taje tayi parking sannan ta fito tayi hanyan class 膹insu, a tare da lecturer 膹insu dai dai suka iso, ta k'ofan baya ta shiga ta samu waje ta zauna , nutsuwa kowa yayi a ajin har malaminsu ya fara lecture, 10:30 dai dai ya gama ya fita suma suka mik'e suka fito, sai da ta 膹an gaggaisa da y'an ajinsu da ta sani tukunna tayi hanyan motan ta , bata tsaya yin komai ba ta shige ta wuce abinta, hanyan gidansu Farida tabi, a hanya tana driving tana tambayana k'iran number Farida tasan duk yadda akayi dai ta tashi daga bacci yanzu dan can gari yanxu 2 biyu tayi, sau biyu tana k'ira bata 膹auka ba, cikin minti 18 ta isa, har cikin gida ta shiga tayi parking , da sallama ta shiga parlour babu kowa a ciki sai kanshi da yake tashi, hanyan stairs tabi zata hau sama wata mai aiki ta fito daga kitchen ta gaisheta sannan ta tambayeta Ammah na gida, Ce mata tayi ehh tana sama, godiya tayi mata ta k'arasa hawa Saman, a hankali ta bu膹e k'ofan 膹akin Ammah tare da sallama, su biyu ta tarar a zaune, da gudu Farida ta taso ta rungume Batuul tana ce mata "dullop head I missed you, you didn't tell me zakizo" murmushi Batuul tayi tace "ai yanzun ma ba wajenki nazo ba" bata rai Farida tayi tace "Really? well am not hurt, nasan zaki dawo ki nemenin nima" ido Batuul ta juya tare da mata gwalo tace "not in this life" Ammah na daga zaune tayi murmushi ta girgiza kai, gaban Ammah Batuul taje ta zauna tace mata "Nda dubdo Ammah" , "Lafiya kalau Bitti, ya gida ya Aunty, ya kuma karatu, ana dai yi lafiya ko'? kai ta gya膹a mata tare da cewa "Alhamdulillah Ammah , duk lafiya " dubanta Ammah tayi tace "kin buya Bitti, sam ba a ganinki ko kuma makaranta ne? " Da sauri ta sadda kanta k'asa dan tasan bata kyauta ba, rabonta da gidan ta kai wata biyar, kuma kullum suna ha膹uwa da Farida a school, jiki a sanyaye ta girgiza kai tace " Ammah, zan rika zuwa yanxu" Ammah tace "toh yayi kyau, ai Faridan ma 膹azu da asuba suka iso, ni yanxu zan shiga in kwanta dan yau ban samu nayi bacci ba tunda Farida ta iso ta isheni da surutu" ta fa膹a tare da mik'e wa zata kwanta , da ido Batuul ta bita ganin yadda maganan Ammah yayi sanyi gashi har ta 膹an rame, ganin zata juyo ne ya sata tayi maza ta 膹auke idonta daga duban ta, Ce musu ta sakeyi " Farida in kun sauk'a ki turomin Yaa Bawa" tare suka amsa da toh dukkansu biyun, tana shigewa Batuul ta Janyo hannun Farida tana tambayanta "Ke da muka turaki Uk kiyi wata 膹aya shine ko sati 膹aya baki cika ba kika dawo " Suna fita suka ha膹u da Yaa Bawa ta tattaro kaya zatayi k'asa suka ce mata Ammah na nemanta sannan suka shige 膹akin Farida "Batuul ce ta sake tambayanta "wai meye inata magana kinyi min shiru" tsaki Farida taja tace "ai ni da dan ta nice wlhy ko kwana 膹aya banyi a kasar nn, dama can ba so nake ba Ammah ta sani dole inje, wlhy saura ka膹an in mutu dan baqin ciki, dama sai da kika tayi min dariyan mugunta har da wani rakani airport bakiga ko waya banyi nace miki zan dawo ba, ni nan gaba ko meye za a bani ba zanje gidan ya Abuu ba, toh meye ma yayi zafi, ni dai ban k'ara zuwa, gidan Yaa Abu bai yi ba, shi zafin kai matarsa y'ar duniya mara mutunci, gaba 膹aya ta gama da Yaa Abu, Dan tausayi ma yake bani " tsaya Batuul tayi tana kallonta har sai da tayi shiru tukunna tace "tun 膹azu kike surutu, tell me exactly what happened da kika dawo before time " tsaki Farida taja tace "kina son spoiling mood 膹ina ko, toh tunda baki ganeba, gidan ne babu da膹i, tunda nayi stepping k'afa na a cikin gidan maganan arziki bai tab'a ha膹ani da Ajiddeh ba, kai tun lokacin da na shigo gidan tana hakimce a parlour ita da wasu y'an uwanta ko k'awayenta ne oho taqi amsamin sallama ban sake bi ta kanta ba, shima Yaa Abun da ya dawo gida da yamma naje zan fara mishi complain cewa yayi wai shi fa baya son K'ananan maganganu , wai haka matar tashi take I shud let her be, ni nake dafawa kaina abinci, shima 膹in sae dae Cook suyi ya ci, gara ma da naje ne take 膹an sani in dafa mishi wani abun, kuma baya iya ce mata komai duk iskancin da takeyi, daga ta ganni zata fara wani shan magani tana habaice habaice, har da cewa rannan wai aikin banza, ai mun riga da mun makara daga ni har iyayena tunda har muka bari ta aureshi, toh shine shekaran jiya da naga iskancin nata ka膹an ne da ta saka Ammah jiya na tashi na bita har 膹aki bayan y'an iskan y'an uwan nata sun tafi nace wlhy in ta kuma fa膹in wani abu akan iyaye na sai na laka膹a mata dukan tsiya, kuma in daki banza babu mai ce min komai, da yake k'aramar y'ar iska ce bata ce min komai ba...." Ido Batuul ta wara ta riko hannun Farida tace "Dan Allah dagaske kike, duka fa kikace zakiyi mata har 膹akinta kuma, ta girmemu fa sosai farida" hannunta ta Janye tace "Ni ina ruwana da girman ta, ai bata rike ba, y'ar rainin hankali ai da ta sake fa膹in wani abun wlhy da sai ta raina kanta, sai na kusa illatata, Dan ko banida karfi sai na samu wani abin na bigeta dashi, shine fa bayan Yaa Abu ya dawo, yana shigowa ta fashe da kukan munafurci wai yau wuni nayi ina zaginta har dasu dungure mata kai, dukana kadae ne bae yi ba in gaya maki, shine fa yayi maza yayi min booking flight na dawo yau, har ce min yayi fa wai hutun ya isa haka in koma dama shi bai nemeni ba bare inzo ina tayarwa matarsa hankali, Dan bakin ciki ma ko tsayawa banyi na mishi explaining komai ba na juya naje ha膹a kayana, a parlour ma na kwana shi kuma ya jata sukayi sama , da asuba ya sauk'o ya tulo min ku膹i masu Uban yawa kamar su aka ce mishi nazo nema, ya ha膹ani da John Driver 膹inshi ya kawoni airport, da ya rakani bakin k'ofa nidai sai da na mishi magana nace mishi wlhy Hakkin su Ammah bazai barshi ba, tunda yayi aure sau 膹aya ya tab'a zuwa ya dubasu waya kam ba a xancen sa don baya kira, kuma fa ba wai baya shigowa Nigeria ba, yana shigowa Dan ko randa naje a jiyan shi ya dawo, sai da naga jikinshi yayi sanyi tukunna na fita na bar mishi gidanshi, yau da asuba muka k'araso, kinji yadda akayi na dawo banyi wata 膹aya ba, tagumi Batuul tayi tana kallonta cike da tausayin Ammah, shi yasa duk bata da sukuni knn ta ga ta rame, gskya ya Abuu bae kyauta ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.