Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 8 of 124

Yana xuwa gida, ta back door ya shiga dan baya son had'uwa da kowa saboda ranshi ya gama b'aci, 膹akinshi ya nufa ya bu膹e ya shige, toilet ya shiga ya watsa ruwa yayi alwala ya fito, pjs dinsa ya saka sannan ya shimfi膹a abun sallah ya hau ,dan yaso yayi a shehuri idan yaje amma saboda yarinyar nan bai samu yayi ba sai yanxu wajen after 9, tada sallahn yayi , bayan ya idar ya gama azkar 膹inshi ya hau gadonshi tare da janyo Mac book dinshi yana duba aikin da zaiyi nan da kwana hu膹u, yana gamawa ya kashe wutan 膹akin ya kwanta 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

9

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

K'arfe biyar 5:00 daidai adhan din sallah Asuba ya fara dai dai lokacin Abutturab ya farka daga bacci, addu'ar tashi daga bacci yayi, k'afafuwanshi ya sauk'ar daga kan gadon a hankali, tashi yayi ya isa inda comfy fararen towels dinsa ke rataye yayi, guda 膹aya ya janyo, kayan baccin dake jikinshi ya cire sannan ya 膹aura towel din ya shiga toilet, brush yayi ya watsa ruwa sannnan ya ha膹a da alwala ya fito, closet 膹inshi ya bu膹e ya ciro farar jallabiya ya saka bayan ya goge ruwan jikinshi da towel, gaban mirror ya koma ya fesa turaren j茅an p谩ul Gaulti茅r ya k'ara da Hugo sai Arabian oud ya shafa, abin sallah ya shimfi膹a yayi nafilfili, bayan ya idar ya karanta suratul Mu'minun cikin murya mai da膹i, tashi yayi ya fita masallacin dake manne a jikin gidan daga waje, yana k'arasa yayi raka'atul fajr sannan ya zauna jiran Ladan ya tada sallah su fara, k'arfe 5:40 ladan ya tayar suka fara sallah, suna idar da sallah bayan y'an azkar suka fito daga masallacin, Abui da Sadiq ya hango ya k'arasa inda suke, "Nda wattu" yacewa Abui tare da mik'a mishi hannu, Abui ne ya amsa mishi da k茅lewa s茅lai, Sadiq ne shima ya mik'o wa Abutturab hannu suka gaisa, suna tafiya Abui ya k'ira sunan Abutturab, "yaushe ne tafiyanka" Abutturab ya amsa da "Na so in tafi on monday but naga i have things to cover before meeting dina da minister on tuesday, so i have decided to leave tomorrow monday", Abui yace "okay sai kayi rescheduling flight dinka to gobe, kuma ka fad'awa Ammah dan bata sani ba, mu sai next week dawwanmu inaga" yace "okay Abui" sannan suka k'arasa cikin gida kowa yayi 膹akinshi

Hasken ranar da ya hudo window 膹akinta ne ya sata bu膹e idonta a hankali, ranan da ta gani ne ya sa ta wara y'an madaidaitan idonta ta dubi agogon dake kan bed side drawer taga 6:30, da tsalle ta tashi daga kan gadon, gashinta mai tsayi da shek'i da ya baje tana bacci ta kama ta ha膹e su in a messy bun, toilet ta shiga ta kuskure bakinta da Listerine mouth wash tayi maza tayi alwala ta fito, sallah ta tada , bayan ta idar tayi azkar ta fito daga d'akinta ta bud'e 膹akinsu Ahmad, fridge din 膹akinsu ta bu膹e ta 膹auko ruwan sanyi ta shiga kwara musu, a firgice kowannensu ya tashi suna mitsitsika ido, Sa'eed ne yace mata "haba Yaa Batuul yanxu kuma mey mukayi kika tashemu da ruwan sanyi", dukkansu ransu a b'ace suna kallonta suna jiran suji mey sukayi da ta katse musu bacci, "Y'an rainin wayo kunga ban fito sallah ba shine babu wanda yayi knocking min k'ofa, ai tunda baku ganni nazo gaida Baa ba sai kuzo ku dubani, amma kowanne da yaje masallaci dawowa yayi yaci gaba da baccinshi, sai yanxu nayi sallah asuba, yan rainin wayo kawai, Khalil ne yace " toh mu mun san baki tashi bane, kuma ai Aunty ma munsan zata tasheki" Harara ta watsa mishi, Ahmad kam ko uffan baice ba dan ya san harda haushin jiya yasa ta zuwa da watsa musu ruwan sanyi suna bacci, Mus'ab ma baice komai ba, tana fa膹an dalilinta na watsa musu ruwa yaja bargonshi ya kwanta dan inda sabo sun saba da masifanta, saida ta gama fa膹anta sannan ta juya tare da banko musu k'ofa ta fita, k'asa ta sauko taga babu kowa ta koma d'akinta

11:00 ta sauko cikin abayar Al layl tayi kyau sosai, fuskanta ba komai sai kwalli da ta saka, duk y'an gidan na parlour, Su Ahmad ne suka bita da kallo ransu a b'acen abinda tayi musu 膹azu,itama palon taje bayan ta gaida Baba da Aunty ta sami waje ta zauna, Baba ne yace mata "Batuul tafiyanmu gobe ne dan haka yau zakuje ku gaida su Yayya da kowa da kowa, meeting dina tuesday so dole mu tafi gobe, kuma kinga graduation 膹inki saura two weeks, sai ki fara shirye shirye ko" tace "yo Baa", Aunty ce tace mata "kan naki ya dena ciwon", ita ta manta ma gaba 膹aya da tayi ciwon kan k'arya, tunowa tayi da abinda ya sata yin k'arya, 膹an k'aramin tsaki tayi daga ciki, a ranta tace wannan mugu ne dagaske shiyasa Farida bata sonshi tafi son Sadiq, da sauri tacewa Aunty, " eh da nayi bacci na tashi ya dena", "sai kije kici abinci ki fito mu tafi dan muna da wajen zuwa dayawa a yau" toh tace sannan ta nufi dinning ta bubbu膹e food flaskses da kwanunkan dake kan dinning 膹in, plate ta 膹auka ta saka pancake guda da 膹aya da strawberry syrup sannan ta 膹auki Fanta ta zauna ta ci a hankali har ta gama ta dawo palon tace ta gama, Aunty ce tacewa yaran toh ku tashi mu tafi Baa Liman na jiranmu shi zai kaimu, dukkansu sukayiwa Baba sallama suka fita, wata range rover 2011 suka dosa dukkansu, Baa Liman ne ya bu膹e kofan driver ya shiga, motan duk ya hargitse da surutu kowa yana fa膹in ga wak'an da yakeso a sa, daga k'arshe ne Batuul tace a saka musu wak'okin Wael Jassar, ana sawa duk suka fara bin wak'okin shi na farko a album din 7aareg damohom, motar cike da hayaniya ba a jin abinda wani ke fa膹i har suka isa gaban wani gate sukayi horn, mai gadi ne ya bu膹e musu su ka shiga, basu bari an gama parking ba suka bu膹e k'ofofin motar suka fito, da gudu suka shiga gidan suna fa膹in *yayya ishena*, *yayya ishena* Yayya munzo, Yayya munzo)da kanuri, wani 膹aki suka bu膹e suka shiga, 膹an madaidacin parlour ne mai kyau sai k'anshi turaren wuta yake da sanyi, suna shiga suka nufi wajen wata tsohuwa fara sol, dukda ta tsufa amma kyanta na nan, anyi mata kitson gaba da ya zubo daga gefe, na bayan kuma ta tufke shi, murmushi tsohuwar tayi ta rungeme yaran, Batuul na shigowa taje wajenta ta ture yaran daga jikin tsohuwar tare da cewa "Ku 膹aga min takwara kar ku ballamin ita, tunda kuma bana yiwa takwarorinku haka, rungume tsohuwar tayi sannan tace mata Yayya *tussuna nya ruk茅i*, (na da膹e ban ganki ba, nayi missing 膹inki), Yayya tace mata " *nda rui sha, jirem g茅i*(dubeta kamar dagaske ban yadda ba), Aunty ce ta k'araso 膹akin ta zauna sannan suka gaisa da Yayya, cikin girmamawa suka gaisa sannan yayya ta k'ira daya daga cikin masu aikinta, "ki kawo musu abinci da kayan sha ki jera a kan dinning,cikin kanuri ta fa膹i maganan don bata jin Hausa, sunajin abinda yayya ta fa膹a kowa ya fara fa膹an choice dinshi na abinda zaici, duk saida aka kawo musu abinda sukace sunaso aka jera musu, a gidan suka wuni har dare

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.