Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 110 of 124

90

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

聽 聽 聽 Har suka Isa Blue Cabana duk surutun da akeyi a motar batace komai ba, Sadiq ma duk tsokanarshi haka ya gaji ya kyaleta, bayan anyi parking da kamar bazata fito ba ganin kowa ya fito itama ta fito sai b'ata fuska takeyi, Abu na gama parking shima bayan yaran sun sauk'a ya rufe motar yacewa Farida ta karb'i Aabid hannun yaran nan ta rik'eshi snn ya zagaya ta wajen Side d'in da Batuul take, cikin wasa ya harareta ya kamo hannunta yace "Keh wa yace miki ana shiga motar Sadiq, he drives roughly, bare keda kike carrying baby na", ya d'aura hannunshi kan cikinta, da sauri ta wara ido ta kalleshi jin hannunshi a jikinta tayi maza ta ture hannun tana kalle kallen ko wani ya gansu, ko a jikinshi saima tsareta da yayi da ido, kauda kanta tayi ta matsa baya, yaci gaba "Kina ganin irin gudun da ya riqa shararawa kamar mai shirin barin garin, plss kar ki sake shiga driving d'inshi, I will be there for you always, In sha Allah kinji, Let's get going", d'an k'aramin bakinta ta tsuke tareda murgud'ashi tana janye hannunta, daidai kan idonshi, ido ya lumshe ya bud'e su kanta a ranshi yace "Damn, komai tayi kyau yake mata koda kukane, shi bai tab'a ganin wanda kuka keyiwa kyau ba kamar ita, badan bayason ganin kukanta ba yana damunshi yana sashi jin wani iri da kullum sai tayi mishi ya gani sbd in tanayi face d'inta na zama cute, ainihinta yake gani batareda k'arin komai ba sai lips d'inta da suke sake komawa pink, matsowa ya dad'a yi gabanta yace "Hey mey ke damunki", yasan wani abin ne ya sameta wannan attitude d'in da ta fara displaying, kamar jira takeyi ya tambayeta hawaye ya fara bin kuncinta, wani abin yaji har cikin ranshi, wlhy ko kad'an baya son ganin hawayenta, "Ya salam" ya furta snn da sauri ya jawota ya rungumeta sosai a jikinshi, duk da hijabin dake jikinta hakan bai hanashi jiyo d'uminta dake soothing d'inshi ba, Su Sadiq suka k'araso ganin basu taho ba, "Bro, for real?, a nan d'inma?", ya fad'a muryarshi cikeda tsokana, wani kallo Abu ya jefa mishi da yasashi fashewa da dariya, sai a lokacin ya lura da Batuul dake hawaye yace "Subhanallah, mey ya sameta haka?", ya juya yana tambayan su Farida da su Ahmad da suka tsaya cirko cirko suna kallonsu, kafad'a Farida ta d'aga mishi alamun she has no idea, muryan Abu yaji yace "You guys should get going, make sure kowa ya sami abinda yakeso, anything okay?", ya mik'o mishi ATM card d'inshi da ya ciro cikin aljihu yace "We will join you shortly", Sadiq da damuwa duk ya cikashi yace "Yeah okay....but then is she fine?, like babu matsala", Kai Abu ya kad'a mishi yace "Bakomai, Farida ki kula da yaran nan, let them have all they want", Farida ta kad'a kai ta kama hannunsu suka fara tafiya, suna tafiya ya jasu suka jingina jikin mota a hankali yake patting bayanta yace "Hayat meye kuma?, what is it now, kukanki yafi komai tada min hankali, you should please stop it and tell me mey ya sameki, mey kikeso?", ajiyar zuciya takeyi har lokacin, sassauta rik'on yayi snn ya d'ago kanta yana kallon fuskarta da ta b'aci duk da hawaye, sauk'e idonta tayi k'asa bata bari sun had'a ido ba, yasa hannu ya share mata hawayen yayi cupping fuskarta da duka hannayenshi yace "Okay now tell me, mey kikeso", kamar baza tayi magana ba a hankali tace "Ko ba kaine ba", jin tace shine ya wara ido ya kalli fuskanta da kyau yace "Huh?, Really?, Ni na saki kukan?, Me nayi toh, tell me please , I will rectify it right away kinji", ya k'arashe maganan kamar zaiyi kukan shima jin shi ya sata kuka, cikeda shagwab'a kamar zata sa wani sabon kukan tace "Ko ba kai bane ba kace sai in saka hijab bayan zafi akeyi kuma fa its an evening outing sai kowa ya rik'a ganina kamar matar aure fa", sosai magananta ya bashi dariya da mamaki, bai san shirmen nata har ya kai haka ba, d'ago kanta yayi yana kallonta tareda sa hannu yana zagaye shape d'in da Hijabin yace "Fatima Hijab din ne baki so?", bata d'ago ta kalleshi ba tace "Ni ai bance banaso ba, kawai fa Kaine, kowa sai yace ni matar aure ce", ta sake fashewa da wani kukan, rungumeta ya sakeyi yanzu kam dariya yayi da kyau yace "And that's exactly dalilin da yasa nace ki saka Hijab, banason ana kallemin keh, bazan saurarawa duk wanda yayi miki wani irin kallo ba, you are married Fatima, married to me, you are just mine", ajiyar Zuciya ta sauk'e jin maganunshi tace "Ba toh zan iya saka Abaya ba or any gown", yayi murmushi yace "Yeah hakane but then, hijab zaifi rufemin keh all, nafison ganin ki so modest da kowa na ganinki yasan yes you are married, don't you know immodest dressing shike attracting filth, shike janyo duk wata musiba ta yanzu da ake facing tsakanin opposite gender", dogon numfashi taja jin abinda yace kuma tasan gaskiya ya fad'i, a hankali ta janye daga jikinshi tace "toh shikenan, am sorry", kamota yayi yayi pecking goshinta yace "I love you", wani irin rumbles taji a cikinta kamar jiya jin ya sake maimaita mata I love you, yace "Let's help you ki cire Hijabinki sai muyi zamanmu cikin mota tunda kinga zafi kikeji, I will order duk abinda kike so here", ya fad'a yana ciro wayarsa daga aljihu, da sauri ta riqe mishi hannu ta girgiza kai tace "No am fine, ai na dena jin zafin", murmushi yayi yace "Sure?", ta kad'a mishi kai tace "Yeah", da haka ya riqe hannunta suka isa wajen dasu Sadiq suke, lokacin har kowa yayi ordering abinda yakeso,聽 ido suka zuba musu su dukan suna jira suji mey ya sameta , kujera Abu Abu ya ja mata ta zauna snn shima ya zauna, raurau tayi da ido ganin duk ita suke kallo ta kalli Abu, murmushi yayi ya kallesu ya d'aga musu gira yace "She is fine, babu abinda ke damunta, y'all should relax", explanation d'in abinda ya sata kuka suke jira yayi musu amma ganin kamar bazai yi ba sukayi shiru kowa yaci gaba da abinda yakeyi, waiter ya k'ira ya bashi order abinda za a kawo mishi snn ya ce Batuul ta fad'i abinda take so, tace "Chicken wings in marinated sauce with plenty garlic, Large Lasagne, cream in chicken soup with emm french bread... ", tsayawa kowa yayi ya zuba mata ido jin taqi dena ordering, a hankali Farida tasa hannu ta d'an tab'a ta tace "kee ina zaki zuba duka wannan abinda kike ordering, mey zakiyi dasu?, k'asa k'asa tayi maganar, murgud'a mata baki tayi tace "Keh kam ina ruwanki, inma zubdawa zanyi", ta juya taci gaba da bashi order "With spicy lamb kebab, sour cream sauce, butter scotch ice cream with some toppings, just any and strawberry shake", Abu kam danna wayarsa yakeyi har saida ta gama ya kalleta yace shikenan?, kai ta kad'a mishi yace "Okay you can go",聽 ganin Expressions dake shimfid'e fuskarsu ta d'aga musu kafad'a tace "Wai meye nayine, nifa zanci kayana",聽 Sadiq ya saka wani irin dariya da聽 yasa Abu ya d'ago yana neman mey yakewa dariya, cikin dariyar yace "Do you eat this much ko kuma dai da wani abun, am not getting this seriously", ya sake saka dariya, Farida ma tasa dariya, wara ido tayi snn tayi raurau dashi ta kalli Abu kamar聽 zatayi kuka, kujerarshi ya ya matsar kusa da nata with stern voice yace "Saaadiqq", snn ya watsawa Farida dake k'ok'arin had'iye dariyarta harara, "don't mind them, shiyasa kikaga basuda lafiya, Eat as much as you want, babu ruwanki dasu", ta tsuke baki tace "Bafa dayawa ma nayi ordering ba, kad'an ne fa dan inajin kwad'ayinsu ne duka", ya jawota jikinshi yace "Shhh don't worry, ya kwantar da kanta kan kafad'arshi, suna zaune har aka kawo mata duk abinda tayi ordering

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.