Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 24 of 124

A k'ofar gidansu Ajiddeh ya tsayar da motan ba tare da ya shiga ba, enveloles guda biyu manya ya mik'o mata, sai da ta karb'a sannan yace mata "Wannan tickets ne na masu zuwa 膹aurin aure, mun riga da munyi chattering plane 膹in, in bai isa ba gobe before 1 ki sanar dani dan 3 zamu tafi, ki fa膹awa Su Mum an gama readying komai har na sauk'an baki, kuma a ranan zamu juyo bayan an 膹aura aure, da膹i taji sosai , burinta na auren Aliyu Ahmad Kyari ya kusa cika, bata tab'a jin tana son mutum kamar shi ba , tsayawa tayi tana kallonshi kamar a mafarki, hure mata fuska yayi ya 膹aga mata gira yana tambayanta ya akayi, rungumeshi kawai tayi ta shige jikinshi gabs 膹aya, bayanta ya 膹an bubbuga sannan ya janyeta, hannunta ya rik'e yana kallon lallen dake hannunta, "yayi kyau yace mata", da murmushi tace mishi "thank you baby, tun 膹azu nake jira kace nayi kyau amma baka fa膹a min ba", kallonta yayi gaba 膹ayanta tayi kyau dagasken dan baima lura ba 膹azu, gefen fuskanta ya shafa sannan yace "ai keh mai kyauce", wani da膹i ne ya kamata ta rasa mey ma zata ce mishi, ce mata yayi "ni zan wuce gida yanxu , kuyi mana addua, zamu wuce gobe mu dawo saturday, so sai mun dawo kenan, kamar kar ya tafi ta rik'a ji, har wani 膹an hawaye ne ya taru a idonta, bu膹e k'ofan tayi ta fita, sai da ta shige kamin ya ja motarsa yayi gaba, kamar ba su sukayi fa膹a ba 膹azu, sha biyu saura ya isa gida, hayaniya ne ko ta ina kamar dare bai yi ba , ko ina kunne yake da haske, 膹akinshi yaje yabi ta wata hanya da zata sada shi da 膹akin Ammah saboda yawan jama'ar dake gidan, tura k'ofan yayi tare da sallama ya shiga, tana zaune da wasu manyan kwalaye a gabanta Sadiq na daga gefenta tana mishi bayanin wani abu, waje ya samu daga kusa da ita ya zauna kamar zai shige mata jiki, juyowa tayi ta dubeshi tace "Abu kaine da daren nan", kai ya gya膹a tare da cewa "nine Ammah , nazo ne muyi sallama tun yanxu dan gobe ba lallai mu samu time ba", Sadiq ne ya sake wane murmushi mai ha膹e da dariya yace "Yayanmu ango, daga gobe kuma ka zama posession 膹in Hauwa", murmushi ya tare da girgiza kai yacewa Sadiq "you will never change" jujjuyawa yayi ya duba 膹akin can ya juyo ya dubi Ammah yace mata "Ammah ina Farida ne", ce mishi tayi "Ai Farida tun da rana ta gudu gidansu Batuul, mita take ta yi min wai ana b'ata mata 膹aki da toilet ita baza ta zauna ba, shine ta tafi wajen Batuul", sunan Batuul ne da Ammah ta ambata ya sashi tunata, ka膹a kanshi yayi yace " Faridan Abui, ai da ta fa膹a wa Abui cewa zaiyi tazo 膹akinshi", Sadiq yace "Riri akwai case", Abutturab ne ya sake matsowa kusa da Ammah, hannunta ya rik'e yace "Ammah gobe zamu tafi Maiduguri 膹aurin aure, a yi mana addua Allah ya kaimu ya dawo da mu lafiya", kallonshi tayi na y'an dak'ik'u sannan ta shafa kanshi tace "Allah yayi maka albarka Abu, Allah ya tabbatar muku da alherin rayuwanku, ya baku zaman lafiya, ya azurtaku da zuriya 膹ayyiba, Babana you are taking a great step a rayuwanka, amana zasu baka ita, ka rik'e ta tsakani da Allah, in tayi laifi ka nuna mata tayi ba daidai ba, in yayi girma ka hukuntata daidai da laifin da tayi, ka zama mai yi mata adalci a koda yaushe, hankalin mace ba irin naku bane, kayi hak'uri da duk abinda zaka fuskanta , Allah yayi muku albarka", ji yayi duniyar tayi mishi wani iri, kamar an 膹aura mishi wani abun mai nauyi, ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yace "in sha Allah Ammah, Allah ya k'ara muku nisan kwana" shafa kanshi ta sake yi tace "Amin Babana", Sadiq dake zaune a gefe ne ya ciro handkerchief daga aljihunshi yana goge hawayen k'arya yace "wannan emotional moment 膹in naku can melt a mountain, har kuka zaku sani", Ammah ce tace "saura kaima, ai kana hanya", dariya yayi tare da nuna kanshi da yatsanshi yace "Ammah ai ni yarone tukunna, mun bar manya sai sun gama tukunna" ya k'arashe maganan yana murmushi, ce musu tayi "in kunje gobe Yaa Mera ta sa a shirya komai da zaku buk'ata a shehuri na abinci, accomodation dama kun gama shiryawa ai ko" kai suka gya膹a mata a tare suka amsa da "ehh", tace "toh shikenan Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, Allah ya taimaka, ku tashi kuje ku kwanta yanxu dare yayi kuma kuna da abun yi", mik'ewa sukayi dukkansu biyu suka rungumeta tare da sumbatar goshinta sannan sukayi mata sallama suka fita

Washegari k'arfe hu膹u jirginsu ya isa Maiduguri, motocine masu yawa suka zo taransu, samari ne gaba 膹aya a airport 膹in, sai da Abutturab, Massa, Sadiq da Abba suka tabbatar kowa ya isa masaukinsa sannan suka sukavbar airport 膹in suma, gida yaje ya tarar da Abui zaune tare da mutane a palon gidansu, gaishesu yayi ya zo kusa da Abui sukayi magana ya haura sama, wanka yayi ya canja kaya ya fito , sake zuwa yayi suka yi magana da Abui sannan ya fita daga falon, mai gadi ya k'ira yace mishi ya 膹an goge mishi mota zai fita dashi yanxu ya mik'a mishi key, zama yayi k'ark'ashin wani bishiya ya danna wayanshi har aka gama wankin aka dawo mishi da key, mik'ewa yayi ya karb'a sannan ya isa inda motar take ya bu膹e ya shige, rear mirror shi ya seta zai juya kenan idonshi ya hango mishi wani abu, hannu ya mik'a daga baya ya 膹auko abun da ya gani, tsayawa yayu ya kafawa 膹an kwalin dake hannunshi ido kamar mai karanta wani abu, ranan da ya fara ganin Batuul ya tuna, ya ganta a masallaci, sai kuma da Ammah tace ya maida Batuul gida, ranshi ne ya b'aci kamar ranan akayi abun, k'ofa ya bu膹e zai yar da 膹ankwalin ko me ya tuna kuma sai ya fasa ya mayar cikin safe keep 膹in motar, tadawa yayi ya fita daga gidan, Muna guest inn yaje , bu膹e mishi k'ofa akayi ya shiga inda aka sauk'i abokanshi yaje , yana shiga yaga kowannensu har sun canja kaya, wasu na sallah wasu na cin abinci, alwala shima ya shiga yayi ya jagorance wa膹anda basuyi ba sallah , abinci ya 膹ebo bayan sun idar da sallah dan baici komai ba tun safe, yana cin abinci suna hira da abokananshi har ya gama suna ta hira

Mik'a Batuul tayi daga kan gadonta, gaba 膹aya jikinta baya mata da膹i, tashi tayi taje tayi wanka ta dawo, agogo ta duba taga k'arfe 膹ayan rana, hannu tasa ta tada Farida, "ki tashi Riri, rana tayi", da kyar ta samu ta tada Farida, tashi tayi ta zauna akan gado tacewa Batuul "Nifa ban koma na kwanta ba tun asuba sai eleven shine kika tada ni", Batuul bata ce mata komai ba ta tashi taje saka kayanta, doguwar rigar atamfa ta saka, fita tayi daga 膹akin ta tarar da Aunty a palon sama, gaida Aunty tayi sannan ta zauna kusa da ita ta jawo remote tana canja channel, Aunty ce ta tambayeta "Faridan fa, ya akayi kika fito kika barta", cewa tayi "wanka takeyi na fito na barta" tunowa tayi da mafarkin da tayi jiya, Juyawa tayi ta dubi Aunty ta cemata "Aunty jiya da safe da ina bacci nayi mafarki, wai ina kwance a wani falo babba akan gado, akwai rami a falon, wata farar mata ni banga face 膹inta ba tazo tana tura gadon cikin ramin, wai sai ga wani mutum yazo yana tare gadon, shinefa wai da mutumin ya turani na bar kusa da ramin shi sai ya fa膹a ciki, amma ya samu ya rik'e wani k'arfe daga ciki yana mik'omin hannunshi in fito dashi, kuma har sunana ya sani, da farko Batuul yake ta cewa, daga baya ne ya fara cewa Fatima, shine na sauk'o daga gadon na rik'e mishi hannu ya fito dani, bayan ya fito ina ta so ya sakeni yak'i, sai kuma ga matar ta sake yowa kanmu, shine lokacin na tashi", saida Aunty ta gama sauraronta sannan tace mata "bakiyi addu' bane kamin ki kwanta" ta tambayeta, "nayi addu'a da zan kwanta, da na tashi ma jikina yana ta b'ari, duk jikina gumi, sai da nayi wanka nayi nafila tukunna na 膹anji dama dama kuma da na tashi da safe zan fa膹a miki naga kun fita", "Allah ya rufa asiri, kina yawaita addua kullum ba sai kin kusa kwanciya ba, kuma next time in kinyi mummunan mafarki kar kina fa膹a, kinji", "toh" ta amsa da, Farida ce ta k'araso palon , wajen da Aabid ke kwance yana wasa ta k'arasa , zama tayi ta 膹aukeshi tare da gaida Aunty, ansa mata da sannan ta tashi ta tafi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.